Wane Ne Ya Kafa Addininku?
Ƙungiyar Shaidun Jehobah ta zamani ta fara ne a ƙarshen ƙarni na 19. A wannan lokaci, wani ɗan ƙaramin rukunin ɗaliban Littafi Mai Tsarki waɗanda suke da zama a kusa da Pittsburgh, Pennsylvania, a ƙasar Amirka, ne suka fara bincike mai zurfi cikin Littafi Mai Tsarki. Sun fara gwada abin da ake koyarwa a coci da kuma abin da ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Sai suka fara buga abin da suka koya a littattafai, jaridu, da kuma mujallar nan da ake kira a yanzu Hasumiyar Tsaro—Mai Shelar Mulkin Jehobah.
Tsakanin waɗannan ɗaliban Littafi Mai Tsarki akwai wani mutum mai suna Charles Taze Russell. Ko da yake Russell ne ya ja-goranci aikin koyar da Littafi Mai Tsarki a wannan lokacin kuma shi ne editan farko na Hasumiyar Tsaro, bai kafa sabon addini ba. Muraɗin Russell da kuma sauran Ɗaliban Littafi Mai Tsarkin, kamar yadda ake kiran rukunin a dā, shi ne su yaɗa koyarwar Yesu Kristi kuma su bi misalin ikilisiyar Kiristoci na ƙarni na farko. Tun da Yesu ne ya Kafa Kiristanci, a ganinmu shi ne ya kafa ƙungiyarmu.—Kolossiyawa 1:18-20.