Kuna Wa’azi Gida-Gida Don Ku Cancanci Ceto Ne?
A’a. Muna fita wa’azi gida-gida kullum, amma ba mu gaskata cewa yin hakan zai sa mu cancanci ceto ba. (Afisawa 2:8) Me ya sa?
Ka yi la’akari da wannan misalin: A ce wani mutumin kirki ya ce zai ba da wata kyauta mai tamani ga duk wanda ya hallara a wani wuri kuma a rana kaza. Idan ka tabbata cewa mutumin zai cika alkawarinsa da gaske, ba za ka bi umurninsa ba? Hakika! Mai yiwuwa, za ka gaya wa abokanka da iyalinka game da zarafin samun kyautar don su ma su amfana. Duk da haka, ba bin umurninsa ne zai sa ka cancanci kyautar ba, za ka sami kyautar ne domin mutumin yana son ya ba ka.
Hakazalika, Shaidun Jehobah sun gaskata cewa Allah zai ba duk wanda ya bi umurninsa rai na har abada. (Romawa 6:23) Muna kokarin bayyana imaninmu wa mutane don muna son su amfana daga alkawuran Allah. Amma ba mu gaskata cewa za mu cancanci ceto don wa’azin da muke yi ba. (Romawa 1:17; 3:28) A gaskiya, babu dan Adam da zai iya yin aikin da zai sa ya cancanci ceto domin wannan kyauta ce mai tamani daga Allah. “Ya cece mu, ba wai don wani aikin adalci da mu muka yi ba, a’a, sai dai domin jinkan nan nasa” ne.—Titus 3:5.