Koma ka ga abin da ke ciki

Yin Wa’azin Bishara a Arewacin Amirka da Turai

Yin Wa’azin Bishara a Arewacin Amirka da Turai

A shekara ta 2014, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta ba da umurni game da wani sabon shiri na yin wa’azin bishara a yankunan da ke arewacin Amirka da Turai. (Ayyukan Manzanni 1:8) Da farko, an mai da hankali ga wasu yankuna da ke jihar Alaska (Amirka) da Lapland (Finland) da Nunavut da kuma Yankunan da ke arewa maso gabashin Kanada.

Shaidun Jehobah sun yi shekaru da dama suna zuwa wa’azi a wadannan wuraren. Amma, sukan je su zauna na dan lokaci su rarraba littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki kuma su dawo.

A wannan sabon shirin, ofisoshin Shaidun Jehobah da ke kula da wa’azin bishara da ake yi a yankuna masu nisa sun gayyaci masu wa’azi na cikakken lokaci (majagaba) su je su yi watanni uku ko fiye da hakan suna wa’azi a wasu yankuna da ke wadannan wuraren. Idan mutane a yankin sun amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su, masu wa’azin za su iya yin fiye da wata uku a yankin kuma su gudanar da taro don jama’a.

Ko da yake, yin wa’azi a wasu yankunan da ke Arewa yana kunshe da kalubale. Daya daga cikin masu wa’azi biyu da aka tura wa’azi a garin Barrow da ke jihar Alaska, ya fito daga kudancin California, dayan kuma daga jihar Georgia da ke Amirka. Sun yi fama da sanyi sosai a lokaci na farko da suka je garin Barrow! Duk da haka, a cikin ’yan watanni da suka zo, sun yi wa’azi a kusan dukan gidajen da ke garin kuma sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki guda hudu, hakan ya hada da nazarin da suke yi da wani saurayi mai suna John. Ana amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? don yi wa shi da budurwarsa nazari kuma yana gaya wa abokansa da abokan aikinsa abubuwan da yake koya. Kari ga haka, yana nazarin Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana ta JW Library app da ke wayarsa.

Babu hanya zuwa Rankin Inlet da ke yankin Nunavut a Kanada. Saboda haka, majagaba guda biyu da aka tura yin wa’azi a wurin sun bi jirgin sama zuwa wannan kauyen kuma sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da dama. Bayan wani mutum ya kalli bidiyon nan, Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? sai ya yi tambaya cewa yaushe ne za mu gina Majami’ar Mulki a kauyen. Ya kara cewa, “Idan ina nan a lokacin, zan halarci taro.”

Majagaba da aka tura zuwa yankin Savukoski a kasar Finland sun ce: Ana matsanancin sanyi da dusar kankara.” A wannan yankin, akwai dabobbi kamar gada kuma yawansu ya ninka yawan mutane da ke wurin wajen sau goma. Duk da haka, sun ce zuwansu faduwa ce da ta zo daidai da zama. Me ya sa suka ce hakan? Amsarsu ita ce: “Mun yi wa’azi a dukan yankunan da ke wurin. Hanyoyin zuwa kauyukan da karkaran suna da kyau kuma ana kula da su. Mutane sun kasance a cikin gidajensu saboda sanyin.”

Kokarin da muka yi don mu yi wa’azin bishara wa mutanen da ke wadannan yankunan arewaci ya ja hankalin mutane sosai. Bayan wasu majagaba biyu suka ziyarci magajiyar wani gari da ke jihar Alaska, sai ta rubuta labari mai kyau game da tattaunawar da suka yi da ita kuma ta saka hoton warkar nan Mene ne Mulkin Allah? a shafinta na dandalin hira a Intane.

A karamar hukumar Haines, Alaska, an marabci majagaba biyu sosai kuma mutane takwas sun halarci taron da aka yi a laburaren gwamnati da ke wurin. An ba da rahoto a jaridar da ke garin cewa wasu mutane biyu daga jihohin Texas da North Carolina sun shigo gari suna koya wa mutane Littafi Mai Tsarki a gidajensu. An kammala rahoton da cewa: “Ka shiga dandalin jw.org don ka sami karin bayani.”