Koma ka ga abin da ke ciki

Rumbun Hotunan Warwick na 7 (Satumba 2016 zuwa Fabrairu 2017)

Rumbun Hotunan Warwick na 7 (Satumba 2016 zuwa Fabrairu 2017)

A wannan rumbun hotunan, za ka ga yadda aka kammala gina hedkwatar Shaidun Jehobah da kuma yawan mutanen da suka soma amfani da wurin daga Satumba 2016 zuwa Fabrairu 2017.

Hoton hedkwata na Warwick da aka kammala. Somawa daga 1-8:

  1. Inda Ake Gyara Motoci

  2. Wajen Ajiye Mota don Baki

  3. Gidan Gyare-gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

  4. Gidan Zama na B

  5. Gidan Zama na D

  6. Gidan Zama na C

  7. Gidan Zama na A

  8. Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

8 ga Satumba, 2016​—Wajen da Ake Aiki a Warwick

A yanzu haka, an soma amfani da dukan gine-ginen da ke Warwick. Mutane 500 ne suke zama a Warwick sa’ad da aka shiga watan Satumba. Adadin ya hada da wadanda suka ba da kai don su yi ginin da kuma sauran wadanda suke aiki a Bethel da suka kaura daga Brooklyn.

20 ga Satumba, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani mai zane-zane yana kallon wasu tayil masu walkiya da za a saka a jikin bangon inda za a shiga wurin nuni mai suna “A People for Jehovah’s Name.” Yana hakan ne don ya ga ko an shirya su da kyau. An kera su tayil din a hanyar da za su fito kamar sun dade sosai don su nuna cewa abubuwan da ke wurin nunin sun tsufa.

28 ga Satumba, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu mai suna Stephen Lett, ne ya fara gudanar da ibada ta safe a Warwick kuma an yada shirin a wasu ofisoshinmu. Dan’uwa Lett ya karanta wata wasika, kuma a cikin wasikar an gode wa ’yan’uwa 27,000 da suka ba da kai suka gina wannan wurin da kuma wadanda suka ba da nasu gudummawar a wasu hanyoyi dabam.

3 ga Oktoba, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani kafinta yana saka harufa da ke hanyar shiga daya daga cikin wuraren nuni guda uku da ake da su. Wurin nuni da ake kira “A People for Jehovah’s Name,” na dauke da kayayyakin tarihin Shaidun Jehobah daga 1870 zuwa yanzu.

5 ga Oktoba, 2016​​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Kwamitin Rubuce-rubuce suna tattaunawa da mataimakansu da kuma membobin Sashen Rubuce-rubuce. Manya-manyan telibijin suna nuna irin hotunan da ake so a yi amfani da su a littattafanmu da za a fitar. Kari ga haka, telibijin din yana taimakawa a ga wadanda ake tattauna da su daga sashen rubuce-rubuce a ofisoshinmu a wurare dabam-dabam. Wani ne ya ba da kyautar teburin da suke amfani da shi shekarun baya kuma an dauko shi daga Brooklyn zuwa Warwick.

20 ga Oktoba, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani mataimakin Kwamitin Masu Kula da Ayyuka tare da wani ma’aikaci suna tattaunawa game da yadda za su taimaka wa ’yan’uwan da suke Filifin. Don a ranar 19 ga Oktoba, 2016, guguwar Haima (ko kuma Lawin) ta auku a kasar. Tsarin kira ta kwamfuta yana taimaka wa ’yan’uwa a hedkwata su shawo kan matsaloli na gaggawa da wuri kuma su iya tattaunawa da sauran ofisoshinmu a fadin duniya.

28 ga Oktoba, 2016​—Gidan Gyare-gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Wannan wani dan tafki ne da aka tsara a hanya ta musamman kuma yana tsakanin gidan gyare-gyare da hanyar shiga hedkwatar. Tsarin wannan tafkin da na sauran tafkuna da ke Warwick yana cire datti mai guba daga ruwan sama da ya taru a ciki. Wannan tsarin yana taimakawa wajen rage kudin da za a kashe don gina magudanan ruwa. Bayan an tsabtace ruwan, yana gangarowa zuwa kogunan da ke yankin kuma hakan yana kyautata mahalli wa dabbobi da shuke-shuke.

4 ga Nuwamba, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wasu ’yan’uwa da aka ba su aikin kwasan kayan masu kaura suna sauke kaya daga wurin da aka ajiye su don su kai su dakuna dabam-dabam. Ma’aikata wajen 80 ne suka taimaka wajen kwasan kayan ’yan’uwanmu da ke aiki a hedkwata da suka kaura daga Brooklyn zuwa Warwick.

14 ga Disamba, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Masu yin burodi suna sauke kulli daga injin hada kullin zuwa kan teburi. Da yake nauyin kullin yana iya kai kusan na buhun siminti, ana amfani da babban injin hada kullin don ya zama da sauki. Gidan burodin da ke Warwick yana da wani na’ura da ke daidaita yanayin sanyin dakin da makamantansu idan ana son kullin ya tashi da wuri ko ya tashi a hankali. Wadannan injunan da na’urori suna sa a iya gasa burodi da yawa kowane sati da sauki.

14 ga Disamba, 2016​—Gidan Gyare-gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Masu aiki a sashen da ke kula da tsabtar hedkwatar suna fitar da buhunan datti daga Gidan Gyare-gyare. Yawancin gine-ginenmu a Warwick suna hade, saboda haka ma’aikata da kuma motoci kadan ne kawai ake bukata don kwasan shara da kuma wasu kayayyakin da za a iya sake sarrafa su. Amma ba haka ne aka tsara gine-ginen da ke Brooklyn ba.

14 ga Disamba, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Ana fesa ruwa a kan wani riga kafin a goge shi da injin guga. Sashen Wanki da Guga a Warwick suna wanke kayayyakin da nauyinsu ya fi buhun siminti 500 kowane sati. Ana saka alama a jikin rigunan da wata na’ura don kada su bata. Ana bincika wannan alamar yayin da kayayyakin suka isa hannun masu wanki dabam-dabam don a tabbata cewa an kula da su da kyau kuma a iya mai da su wurin da ya kamata a kai.

20 ga Disamba, 2016​—Gidan Gyare-gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Wani makanike yana gyarar motar da ke daga ma’aikata sama a cikin dakin lantarki. Irin wannan gyarar tana sa kayayyakin aiki su dade kuma za ta taimaka wa ma’aikata su yi aiki ba tare da hadari ba.

10 ga Janairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani mai gyarar kwamfuta yana gyara manhajar da ke gabatar da abubuwan da za a gani a dakin nuni na “Faith in Action.”

11 ga Janairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wasu kafintoci suna shirya wani keken da aka kera a 1903 don a ajiye shi a dakin nuni na “A People for Jehovah’s Name.” Ma’aikatan da suke Warwick ne suka sake gyara wannan keke da wani ya bayar kyauta don su nuna yadda Daliban Littafi Mai Tsarki (daga baya an soma kiran su Shaidun Jehobah) suka kokarta sosai don su yada bishara da kwazo ta amfani da ababan hawa dabam-dabam.

12 ga Janairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Kafintoci suna saka gilas a inda za a ajiye abubuwan da aka yi amfani da su a fim din “Photo-Drama of Creation.” Wannan fim ya kunshi hoton majigi mai kala da murya da aka shirya bisa ga labarin Littafi Mai Tsarki, kuma an fara nunawa a 1914. A wannan shekarar, mutane wajen miliyoyin tara ne suka kalli fim din.

12 ga Janairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wasu masu adana kayan tarihi da kuma mai zane-zane suna shirya juyin Littafi Mai Tsarki na Zurich Latin Bible, fitowar 1544 don za a ajiye shi a dakin nuni na “The Bible and the Divine Name.” Wannan jar alama da ke Littafi Mai Tsarki na hannun hagu yana nuna inda sunan Allah, wato Jehobah yake. Wadannan ’yan’uwan suna yin iya kokari su ga sun kāre Littattafai Masu Tsarki da za su iya yagewa da sauri. Alal misali, sukan manne kowane shafi da farin leda mai gam. Wurin nunin yana da na’ura da ke daidaita sanyi da zafin dakin kuma akwai wani irin hasken wuta na musamman a cikin dakin don kada littattafan su lalace.

16 ga Janairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Bakin da ake kai su zagaya suna kallon gine-ginen Warwick gaba daya daga wata hasumiya mai tsawon mita 23 wanda ya yi daidai da gidan sama mai hawa wajen 7. Daga ranar 3 ga Afrilu ne aka soma barin baki su shirya ranakun da za su zo yawon bude ido da kansu don su zagaya wuraren nuni. Wadannan wuraren nunin suna da alamu da suke nuna wa baki yadda za su yi zagayar da kansu. Wadanda suke so su zo yawon bude ido za su iya cika fom da ke dandalinmu a karkashin GAME DA MU > OFISOSHI DA ZAGAYA.

19 ga Janairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani dan’uwa mai adana kayan tarihi yana ajiye juyin King James Version na farko da aka wallafa a 1611 a cikin wani akwati. Ma’aikatan Warwick ne suka gina akwatuna musamman don baza tsofaffin littattafai masu tsarki.

19 ga Janairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wata mai zane-zane tana ajiye hula a cikin akwati a dakin nuni. Hular Joseph F. Rutherford ne, dan’uwan da ya ja-goranci Shaidun Jehobah karni daya da ya shige. Wannan hoton yana cikin abubuwan da aka ajiye a dakin nuni na “A People for Jehovah’s Name,” inda za a ga yadda Shaidun Jehobah suka sa kwazo wajen yin wa’azin Mulkin Allah a shekarun baya.

20 ga Janairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Ana daukan muryar wanda yake karanta yadda baki za su zagaya wurin nuni na, “The Bible and the Divine Name” da kansu. An harhada wannan dakin daukan murya kuma aka soma aiki da shi a Warwick bayan sati daya da ’yan kwanaki kawai da aka warware dakin a Brooklyn. Ana amfani da wannan ofishin (daya ne daga cikin kananan ofisoshin daukan murya da ke karkashin babban ofishin daukan murya a Watchtower Educational Center na Patterson) ma don a dauki muryoyin masu karatun New World Translation da Hasumiyar Tsaro da Awake da wasu talifofin jw.org da kuma wasu littattafai.

27 ga Janairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wata ’yar’uwa mai koyan aikin kafinta tana fenta gefen wasu hotuna da za a ajiye a wurin nuni. A wannan wurin nunin da ake kira “A People for Jehovah’s Name,” akwai wasu hotunan Daliban Littafi Mai Tsarki wadanda suka soma hidima wajen shekara ta 1870.

15 ga Fabrairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wata ’yar’uwa mai zane-zane tana shafa ma Kaleb fenti, wani dan wasan da ke jerin bidiyoyin nan Ka Zama Abokin Jehobah. Za a saka wannan mutum-mutumi ne a dakin kayan wasanni da ke dauke da kayayyaki da kuma shirye-shiryen da Shaidun Jehobah suka tsara musamman don yara.

15 ga Fabrairu, 2017​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani kafinta yana yayyanke hotuna da kuma rubutun da aka yi a kan roba don a saka a wurin nunin da ake kira “A People for Jehovah’s Name.” Mutane fiye da 250 ne suka yi aiki daga farko har karshe a wadannan wuraren nuni ko kuma gidajen tarihi guda uku, da ake baje kayayyakin tarihinmu. Wadannan mutanen sun hada da kafintoci da masu aiki da kwamfuta da masu zane-zane da masu aiki da wutar lantarki da dai sauransu.