WAƘA TA 158
“Ba Zai Yi Latti Ba!”
(Habakkuk 2:3)
1. Dukan duniya
na da kyau sosai,
Ta nuna cewa
kai mai hakuri ne.
Alkawuranka
ba sa canjawa,
Za ka cika su,
“ba zai yi latti ba.”
(AMSHI)
Muna roko Uba, ka ba mu jimiri,
Don mu shiga Aljanna.
Madaukaki, Uba,
ka kawo Mulkinka.
Mun san zai zo,
ba shakka,
Ba zai fasa ba!
2. Muna marmarin
ganin lokacin
Da amintattu
da ke kabarbura,
Za su sami rai
a duniyar nan.
Mu jimre sosai
don mu marabce su.
(AMSHI)
Muna roko Uba, ka ba mu jimiri,
Don mu shiga Aljanna.
Madaukaki, Uba,
ka kawo Mulkinka.
Mun san zai zo,
ba shakka,
Ba zai fasa ba!
3. Kana tattara
masu kaunar ka
Don su bauta ma,
su sami albarka.
Muna waꞌazi
da himma sosai.
Yin hakan na sa
mu yi kusa da kai.
(AMSHI)
Muna roko Uba, ka ba mu jimiri,
Don mu shiga Aljanna.
Madaukaki, Uba,
ka kawo Mulkinka.
Mun san zai zo,
ba shakka,
Ba zai fasa ba!
Uba, ka sa mu jimre!
(Ka kuma duba Kol. 1:11.)