Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Marek M. Berezowski/Anadolu Agency via Getty Images

KU ZAUNA A SHIRYE!

An Shiga Shekara Ta Biyu a Yakin Yukiren​—Wane Bege ne Ke Littafi Mai Tsarki?

An Shiga Shekara Ta Biyu a Yakin Yukiren​—Wane Bege ne Ke Littafi Mai Tsarki?

 Ranar Jummaꞌa, 24 ga Fabrairu, 2023 ne ya zama shekara daya cif-cif da aka soma yaki a Yukiren. Kamar yadda wasu rahotanni suka fada, sojojin Yukiren da Rasha wajen 300,000 ne suka mutu ko suka ji rauni, saꞌan nan farin hula wajen 30,000 ne suka mutu a yakin. Amma kila adadin sun fi haka.

 Abin bakin cikin shi ne, ba alamar karshen yakin a nan gaba kadan.

  •   Gidan rediyon NPR (National Public Radio), 19 ga Fabrairu, 2023 ta ce: “Kusan shekara daya ne yanzu da Rasha ta kai wa Yukiren hari kuma ba alama cewa an kusan daina yakin. Akwai alama cewa babu wanda zai yi nasara a cikinsu, kuma zai yi wuya su fahimci juna har ya kai ga sulhu.”

 Mutane da yawa suna bakin ciki don irin wahalar da wannan yakin da kuma wasu yake-yaken suke jawo wa mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba. Wane bege ne ke Littafi Mai Tsarki? Za a daina yake-yake kuwa?

Yakin da zai kawo karshen yake-yake

 Littafi Mai Tsarki ya ce za a yi yakin da za a ceci mutane ba hallaka su ba. Sunan yakin shi ne Armageddon, kuma shi ne ‘yakin babbar Ranar nan ta Allah Mai Iko Duka.’ (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 16:​14, 16) Ta wajen yakin ne, Allah zai kawo karshen mulkin ꞌyan Adam, wanda ke jawo yake-yake da suke jawo kashe-kashe da yawa. Don samun karin bayani game da yadda yakin Armageddon zai kawo salama, ka karanta talifofin nan da ke gaba: