KU ZAUNA A SHIRYE!
Me Ya Sa Mutane Suke Yawan Tsane Juna?—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
Kafofin yada labarai na cike da rahoto game da mutanen da suke yi wa juna bakar magana da mutane da suke yin fada da wasu don sun fito daga wata kabila da kuma yake-yake.
Jaridar The New York Times na 15 ga Nuwamba, 2023 ta ce:Yanzu mutane suna wa juna bakar maganganu a dandalin sada zumunta don yakin da ake yi tsakanin Israel da Gaza da kuma masu tsattsauran raꞌayi da suke son tashin hankali.”
A ranar 3 ga Nuwamba, 2023 Dennis Francis wanda shi ne shugaban Taron Majalisar Dinkin Duniya ya ce: “Tun ranar 7 ga Oktoba yadda ake bakar maganganu da tashin hankali don nuna wariya ya karu.”
Bakar maganganu, tashin hankali da yake-yake ba sabon abu ba ne, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mutane a zamanin dā da suka “harba mugayen maganganu kamar kibiyoyi, kuma sun yi yake-yake da yin mugayen abubuwa. (Zabura 64:3; 120:7; 140:1) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa akwai dalilin da ya sa ake kiyayya a yau.
Kiyayya, alamar zamanin karshe ne
Littafi Mai Tsarki ya nuna dalilai guda biyu da suka sa ake yawan kiyayya a yau.
1. Ya annabta cewa akwai lokacin da “kaunar da yawancin mutane suke yi wa juna za ta ragu.” (Matiyu 24:12) Maimakon nuna wa juna kauna, mutane da yawa za su nuna halayen da suke sa mutane su tsane juna.—2 Timoti 3:1-5
2. Tsananin kiyayya da ake yi a yau yana nuna mugun halin Shaidan Iblis. Littafi Mai Tsarki ya ce “duniya duka tana a hannun mugun nan.”—1 Yohanna 5:19; Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9, 12.
Amma Littafi Mai Tsarki ya ce, ba da dadewa ba Allah zai kawar da abubuwan da suke sa mutane su tsane juna. Kari ga haka, zai magance wahalolin da kiyayya ta jawo. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa:
Allah “zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko bakin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun bace.”—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.