WAꞌAZI NA MUSAMMAN
Kiwon Lafiya—Abin da Mulkin Allah Zai Yi
A ranar 22 ga Mayu, 2023, shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce: “Ko da yake yadda annobar korona take kashe mutane ya ragu, hakan baya nufin cewa annobar korona ba matsala ba ne a duniya. . . . Zai dace mu kasance a shirye domin mu san cewa wata annoba za ta sake bullowa a nan gaba.”
Sanadiyyar annobar korona, mutane da yawa suna shan wahala. Shin gwamnatoci da kungiyoyin kiwon lafiya za su iya zama a shirye don annoba da za ta sake bullowa, kuma su taimaka mana don matsalolin lafiya da muke fama yanzu?
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da gwamnati da zai iya kawo mana lafiyar da muke bukata. Ya ce: “Allah na Sama zai kafa wani mulki” ko gwamnati. (Daniyel 2:44) A lokacin “Ba mazaunin kasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’” (Ishaya 33:24) Kowa zai more koshin lafiya da kuma ka karfi kamar matasa.—Ayuba 33:25.