KU ZAUNA A SHIRYE!
Gasar Kofin Duniya Yana Hada Kan Mutane Kuwa?—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
An ce mutane wajen miliyan biyar ne za su kalli gasar cin Kofin Duniya na FIFA da za a buga daga ranar 20 ga Nuwamba zuwa 18 ga Disamba, 2022. Mutane da yawa suna sa rai cewa ba hada kan masu kallon wasan kawai zai yi ba.
Nelson Mandela, tsohon shugabar kasar Afirka ta Kudu ya ce: “Wasa yana da ikon canja duniya. Yana da ikon sa mutum ya so yin wani abu. Akwai yadda yake sa mutane su kasance da hadin kai.”
Shugaban gasar cin kofi na FIFA a mai suna Gianni Infantino ya ce: “Wasan kwallon kafa yana hada kan mutane don yana sa su kasance da bege da farin ciki, yana sa su rika son yin wani abu da nuna kauna ga juna kuma yana sa su ga cewa suna da wani abu da suke yi tare.
Gasar cin Kofin Duniya ko kuma wata wasa za su iya cim ma wadanan abubuwan da aka ambata? Shin za a iya yin zaman lafiya da kuma hadin kai?
Gasar ta hada kan mutane kuwa?
Gasar cin Kofin Duniya na wannan shekarar ta sa mutane su yi tunani a kan wasu batutuwa ba wasan kawai ba. Wasanni sun sa mutane su tattauna batutuwan siyasa da zaman jamaꞌa da suka kunshi kāre hakkin ꞌyan Adam da wariyar launin fata. Kari ga haka, sun kuma yi mahawwara a kan yadda wasu mutane suna da arziki sosai, wasu kuma talakawa ne sosai.
Har ila, mutane da yawa suna jin dadin kallon wasa kamar gasar cin Kofin Duniya. Duk da cewa mutane suna so wadannan wasanni su hada kansu, ba za su taba sa mutane su sami hadin kai na gaske ba. Maimakon haka, suna sa mutane su nuna halaye da ayyukan da Littafi Mai Tsarki ya ce za a rika gani a “kwanakin ƙarshe.”—2 Timoti 3:1-5.
Abin da zai kawo hadin kai na gaske
A cikin Littafi Mai Tsarki an nuna abin da zai kawo hadin kai na gaske a dukan duniya. Ya yi alkawari cewa dukan mutane a duniya za su kasance da hadin kai yayin da “mulkin Allah” yake sarauta daga sama.—Luka 4:43; Matiyu 6:10.
Yesu Kristi Sarkin wannan Mulkin zai tabbata cewa za a yi zaman lafiya a fadin duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce:
“Adalci ya yalwata a kwanakinsa, salama ta karu.”—Zabura 72:7.
“Yakan kubutar da masu bukata yayin da suka yi kira . . . Daga masu danniya da masu tā da hankali yakan fanshe su.”—Zabura 72:12, 14.
A yau ma, koyarwar Yesu ya hada kan miliyoyin mutane a kasashe 239. Koyarwar ya sa sun daina nuna kiyayya. Don ka sami karin bayani, ka karanta jerin talifofin da ke cikin talifin nan “Yadda Za A Magance Kiyayya.”
a Fédération Internationale de Football Association, wato hukumar da ke kula da kwallon kafa a fadin duniya.