Kana Fushi da Allah Ne?
“ME YA SA nake shan wahala? Me ya sa Allah ya ƙyale waɗannan abubuwa su same ni?” Waɗannan su ne tambayoyin da Sidnei mai shekara 24 da ke ƙasar Brazil ya yi. Ya zama gurgu sanadiyyar faɗuwar da ya yi sa’ad da suke wasa a ruwa.
Shan wuya sanadiyyar hatsari da ciwo da rasuwa da bala’i ko kuma yaƙi za su iya sa mutane su ga kamar Allah bai damu da ’yan Adam ba. Wannan ba sabon abu ba ne. Ayuba uban iyali da ya rayu a zamanin dā ya fuskanci bala’i iri-iri. Cikin kuskure ya zargi Allah yana cewa: “Ina yi maka kuka, ba ka amsa mani ba; nakan tashi tsaye, ka kan zuba mani ido kurum. Kā juya, kā zama mara tausayi gareni: da ƙarfin hannunka kana tsananta mani.”—Ayuba 30:20, 21.
Ayuba bai fahimci dalilin da ya sa yake shan wahala ba, balle ma ya san abin da ya sa aka ƙyale hakan ya same shi. Abin farin cikin shi ne, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana dalilin da ya sa irin waɗannan abubuwan suke faruwa da kuma yadda ya kamata mu bi da su.
ALLAH YA HALICCI MUTANE SU RIƘA SHAN WAHALA NE?
Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Allah: “Aikinsa cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne: Shi Allah mai-aminci ne, marar-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 32:4) Tun da haka Allah yake, shin kana ganin zai dace a ce “mai-adalci . . . mai-gaskiya” ya nufi ’yan Adam da shan wahala ko ya sa mutane su sha wuya don ya horar da su ko kuma ya yi musu gyara?
Akasin haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada kowa sa’ad da ya jarabtu ya ce, daga wurin Allah ne na jarabtu: gama Allah ba ya jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba ya jarabtan kowa.” (Yaƙub 1:13) Hakika, mun koya daga Littafi Mai Tsarki cewa Allah bai nufi ’yan Adam da shan wahala ba. Ta yaya muka sani? Ya ba Adamu da Hawwa’u gida mai kyau da abubuwan da suke bukata da kuma aiki mai kyau. Allah ya gaya musu: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta.” Babu shakka, Adamu da Hawwa’u ba su da wata hujja na cewa Allah ba ya kula da su.—Farawa 1:28.
Amma a yau, duniya ta lalace sosai. Hakika, ’yan Adam sun daɗe suna shan wahala. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ce: “Dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.” (Romawa 8:22) To, mene ne ya faru?
ME YA SA MUKE SHAN WAHALA?
Don mu fahimci dalilin da ya sa muke shan wahala, zai dace mu bincika abin da ya jawo hakan. Wani mala’ika da ya yi tawaye kuma ya zama Shaiɗan Iblis, ya rinjayi Adamu da Hawwa’u su ƙi bin dokar da Allah ya ba su cewa kada su ci ’ya’yan “itace na sanin nagarta da mugunta.” Iblis ya gaya wa Hawwa’u cewa ba za ta mutu ba idan ta yi wa Allah rashin biyayya kuma da hakan, Iblis yana nufin cewa Allah maƙaryaci ne. Shaiɗan ya sake zargin Allah cewa yana hana su ’yancin zaɓan yin nagarta da kuma mugunta. (Farawa 2:17; 3:1-6) Shaiɗan ya yi da’awa cewa ’yan Adam za su ji daɗin rayuwa idan ba sa ƙarƙashin sarautar Allah. Wannan abin da ya faru ya ta da wannan tambayar, Shin Allah ya cancanci yin sarauta?
Iblis ya sake ta da wani batu. Ya yi da’awa cewa mutane suna yi wa Allah ibada don abubuwa masu kyau da yake ba su ne. Game da Ayuba mai aminci, Iblis ya ce wa Allah: “Ba ka kewaye shi da shinge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da yake da shi, a kowane sassa? . . . Miƙa hannunka kaɗai yanzu, ka taɓa dukan abin da yake da shi, za ya la’anta ka a fuskarka!” (Ayuba 1:10, 11) Ko da yake Shaiɗan ya yi wannan furucin ne game da Ayuba, amma batun ya shafi dukan ’yan Adam.
YADDA ALLAH YA BI DA BATUN
Ta yaya Allah zai magance waɗannan matsalolin don kowa ya gamsu? Allah ya san yadda zai yi hakan don hikimarsa babu kamarta, saboda haka, bai kamata mu fid da rai a kansa ba. (Romawa 11:33) Ya tsai da shawarar barin ’yan Adam su yi sarauta da kansu na ɗan lokaci don a fahimci wanda ya dace ya yi sarauta.
Irmiya 10:23) Sarautar Allah ne kaɗai zai iya kawo salama ta dindindin da farin ciki da kuma abubuwan da ’yan Adam suke bukata. Me ya sa? Don haka Allah ya nufa tun farko.—Ishaya 45:18.
Taƙaicin da muke gani a duniya ya nuna sarai cewa sarautar ’yan Adam jabu ce. Gwamnatocin ’yan Adamu sun kasa kawo salama da kwanciyar hankali da farin ciki a duniya, kuma suna gab da halaka duniya. Hakan ya tabbatar da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Ta yaya Allah zai cika nufinsa na halittar ’yan Adam? Ka tuna addu’ar da Yesu ya koya wa mabiyansa cewa: “Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Babu shakka, nan ba da daɗewa ba, Allah zai yi amfani da Mulkinsa wajen kawo ƙarshen dukan wahala. (Daniyel 2:44) Talauci da cututtuka da kuma mutuwa ba za su sake addabi ’yan Adam ba. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah zai “ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi.” (Zabura 72:12-14, Littafi Mai Tsarki) Ya kuma ce game da marasa lafiya: “Wanda yake zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.” (Ishaya 33:24) Yesu ya kuma ce game da matattu: “Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito.” (Yohanna 5:28, 29) Waɗannan alkawura ne masu kyau sosai, ko ba haka ba?
YADDA ZA MU MAGANCE WANNAN MATSALAR
Sidnei da aka ambata a farkon wannan talifin ya yi wannan kalamin shekaru 17 bayan hatsarin da ya yi: “Ban zargi Allah don hatsarin da na yi ba, amma da farko, raina ya ɓaci sosai. A wasu lokatai nakan yi baƙin ciki sosai kuma in yi kuka sa’ad da na tuna yanayina. Amma Littafi Mai Tsarki ya fahimtar da ni cewa hatsarin da na yi ba horo ba ne daga Allah. Kuma kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘sa’a da tsautsayi sukan sami kowannenmu.’ Yin addu’a da kuma karanta wasu ayoyi sun taimaka mini in ƙarfafa dangantakata da Allah kuma in riƙa farin ciki.”—Mai-Wa’azi 9:11, LMT; Zabura 145:18; 2 Korintiyawa 4:8, 9, 16.
Sanin dalilan da suka sa Allah ya ƙyale shan wahala da kuma yadda za a kawo ƙarshen hakan nan ba daɗewa ba, yana taimaka mana mu shawo kan tunanin cewa Allah ba ya kula da mu. Ƙari ga haka, muna da tabbaci cewa Allah “mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.” Ba zai taɓa kunyatar da waɗanda suka dogara a gareshi da kuma Ɗansa ba.—Ibraniyawa 11:6; Romawa 10:11.