ABIN DA KE SHAFIN FARKO | SHIN YA DACE KA YI NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI?
Tsarin Nazari don Kowa
An san Shaidun Jehobah sosai da yin wa’azi ga jama’a. Amma ka san cewa muna nazari da mutane a duk duniya?
A shekara ta 2014, Shaidun Jehobah sama da 8,000,000 a ƙasashe 240 sun yi nazari da mutane kusan 9,500,000 a kowane wata. * Hakika, adadin mutanen da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su ya wuce adadin mutane a ƙasashe ɗaya-ɗaya har wajen guda 140.
Don su sami kayan yin wa’azi, Shaidun Jehobah suna buga Littafi Mai Tsarki da littattafai da mujallu da dai sauran littattafai masu bayyana Littafi Mai Tsarki kusan biliyan ɗaya da rabi a harsuna 700 kowace shekara. Irin waɗannan littattafan da ake bugawa suna ba mutane damar yin nazarin Littafi Mai Tsarki a yaren da suka zaɓa.
AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA AKE YAWAN YI GAME DA NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI DA MUKE YI DA MUTANE
Yaya ake yin nazarin?
Muna zaɓan batutuwa dabam-dabam daga cikin Littafi Mai Tsarki, sa’an nan mu bincika nassosin da suka shafi batutuwan. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshin waɗannan tambayoyi: Wane ne Allah? Mene ne kamanninsa da kuma halayensa? Shin yana da suna? A ina yake da zama? Za mu iya ƙulla dangantaka da shi kuwa? Abu mafi wuya shi ne inda za mu ga amsoshin a cikin Littafi Mai Tsarki.
Don mu taimaki mutane su sami waɗannan amsoshin, muna yin amfani da littafin nan mai shafuffuka 224, wato Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? * An buga wannan littafin ne don a taimaki mutane su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki. Littafin yana ɗauke da darussa game da Allah da Yesu Kristi da wahalar da mutane suke sha da tashin matattu da addu’a da dai sauransu.
A wane lokaci ne ake yin nazarin kuma a ina?
Za a yi nazarin a lokacin da ya dace da kai da kuma a inda kake so.
Nazarin zai ɗauki tsawon minti nawa?
Mutane da yawa suna keɓe awa ɗaya ko sama da hakan kowane mako don su yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma ba lallai sai an kai awa ɗaya ba. Wasu suna yin nazarin na mintoci 10 ko 15 a kowane mako.
Nawa ake biya don nazarin?
Ba a biyan ko sisi. Hakan ya yi daidai da abin da Yesu ya ce wa almajiransa: “Kyauta kuka karɓa, sai ku bayar kyauta.”—Matta 10:8.
Nazarin zai ɗauki tsawon wata nawa?
Kai ne za ka zaɓi tsawon lokacin da kake so ka yi nazarin. Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? yana ɗauke da darussa 19. Za ka iya kammala kowane darasi a tsawon lokacin da ya dace da kai.
Wajibi ne in zama Mashaidin Jehobah bayan nazarin?
A’a. Mun fahimci cewa kowane mutum yana da ’yanci ya zaɓi addinin da yake so. Amma mutumin da ya fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa zai iya yin zaɓi mai kyau.
A ina ne zan sami ƙarin bayani?
Dandalinmu na jw.org/ha yana ɗauke da bayani a kan abubuwan da Shaidun Jehobah suka yi imani da su da kuma ayyukansu.
Ta yaya zan ce a yi nazari da ni?
-
Ka cika fom a dandalin www.isa4310.com/ha.
-
Za ka iya tambayar Shaidun Jehobah da ke yankinku.
^ sakin layi na 4 A yawancin lokaci, ana yin nazari da mutane ɗai-ɗai ko kuma mutane da yawa.
^ sakin layi na 9 Shaidun Jehobah ne suka wallafa. An buga littafin nan fiye da kofi miliyan 230 a harsuna sama da 260.