Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Ta yaya za a koyar da yara su ƙaunaci Allah?

Ka yi amfani da halittu wajen taimaka wa ɗanka ya san Allah kuma ya ƙaunace shi

Sai yaranku sun ga tabbaci cewa Allah ya wanzu da gaske kuma yana ƙaunarsu kafin su koyi yadda za su ƙaunace shi. Suna bukatar su san Allah kafin su ƙaunace shi. (1 Yohanna 4:8) Alal misali, suna bukatar su san: Dalilin da ya sa Allah ya halicci mutum, abin da ya sa Allah yake barin mutane su sha wahala, da kuma abin da Allah zai yi wa ’yan Adam a nan gaba.—Karanta Filibiyawa 1:9.

Idan kana so ka taimaki yaranka su ƙaunaci Allah, wajibi ne ka nuna musu cewa kana ƙaunar Allah. Idan sun ga hakan, za su bi misalinka.—Karanta Kubawar Shari’a 6:5-7; Misalai 22:6.

Ta yaya za ka ratsa zuciyar yaranka?

Kalmar Allah tana da iko sosai. (Ibraniyawa 4:12) Saboda haka, ka taimaka wa yaranka su san muhimman koyarwar da ke cikinta. Sa’ad da Yesu yake neman ya ratsa zuciyar mutane, ya yi tambaya, ya saurara, kuma ya bayyana Nassosi. Hakazalika, idan kana so ka ratsa zuciyar yaranka, wajibi ne ka yi koyi da yadda Yesu ya yi koyarwa.—Karanta Luka 24:15-19, 27, 32.

Ƙari ga haka, labaran Littafi Mai Tsarki a kan yadda Allah ya bi da mutane a dā zai iya taimaka wa yara su san Allah kuma su ƙaunace shi. Akwai littattafai da aka shirya don hakan a dandalin www.isa4310.com/ha.—Karanta 2 Timotawus 3:16.