Ka Tuna?
Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka bincika ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
Mene ne za a halaka, sa’ad da ƙarshen duniya ya zo?
Wasu abubuwan da za a kawo ƙarshensu su ne gwamnatin ’yan Adam da yaƙe-yaƙe da rashin adalci da addinan da suka ƙi yin nufin Allah kuma suka cutar da ’yan adam da kuma mutanen da suke jawo matsaloli a yau.—7/1, shafuffuka na 3-5.
Wane ne Gog na Magog da aka ambata a littafin Ezekiyel?
Gog na Magog ba ya wakiltar Shaiɗan, amma yana nufin ƙasashen da suka haɗa kai don kai wa mutanen Allah hari gab da ƙarshen ƙunci mai girma.—5/15, shafuffuka na 29-30.
Ta yaya mu’ujizai da Yesu ya yi suka nuna cewa shi mai karimci ne?
A wani bikin aure da aka yi a Kan’ana, Yesu ya mai da ruwa wajen lita 380 zuwa ruwan anab mai-kyau. A wani lokaci kuma ya ciyar da fiye da mutane 5,000 ta hanyar mu’ujiza. (Mat. 14:14-21; Yoh. 2:6-11) A duk waɗannan lokatan, Yesu ya yi koyi da Ubansa mai karimci.—6/15, shafuffuka na 4-5.
Duk da cewa mu ajizai ne, me ya sa muke da tabbaci cewa za mu iya faranta wa Allah rai?
Mutane kamar su Ayuba da Lutu da kuma Dauda sun yi kura-kurai. Duk da haka, sun so su bauta wa Allah, sun yi da-na-sani don kura-kuransu kuma suka tuba. Saboda haka, sun sami tagomashin Allah, kuma mu ma za mu iya samun amincewarsa.—9/1, shafuffuka na 12-13.
Shin za a kashe dukan mambobin addinin ƙarya a lokacin da za a halaka Babila Babba?
A’a, domin Zakariya 13:4-6 ya nuna cewa wasu limamai za su bar addininsu kuma su yi mūsu cewa ba su taɓa bin waɗannan addinan ƙarya ba.—7/15, shafuffuka na 15-16.
Waɗanne abubuwa ne Kirista zai iya yin bimbini a kansu?
Wasu abubuwa da Kirista zai iya yin bimbini a kai su ne abubuwan da Jehobah ya halitta da kalmarsa da ya hure da gatan da muke da shi na yin addu’a da kuma tanadin fansa.—8/15, shafuffuka na 10-13.
Ta yaya guje wa tarayyar banza ya shafi fita zance?
Ko da muna son mu yi wa waɗanda ba sa bauta wa Jehobah alheri, ba zai dace wani ya riƙa fita zance da wanda bai yi baftisma ba da kuma waɗanda ba sa bin ƙa’idodin Jehobah. (1 Kor. 15:33)—8/15, shafi na 25.
Ta yaya Bitrus ya ƙarfafa bangaskiyarsa a lokacin da ya soma nitsewa?
A lokacin da manzo Bitrus ya kasance da bangaskiya, ya yi tafiya a kan ruwa don ya je ya sami Yesu. (Mat. 14:24-32) Amma Bitrus ya ji tsoro sa’ad da ya kalli guguwar iska. Sai ya sake mai da hankali ga Yesu don ya cece shi.—9/15, shafuffuka na 16-17.
A littafin Ayyukan Manzanni 28:4 an ce mutanen Malita sun ga kamar Bulus mai kisan-kai ne. Me ya sa suka yi tunani haka?
Sa’ad da maciji mai dafi ya sari Bulus, sun kammala cewa Dike wato allahiyar adalci ce take hukunta Bulus.—11/1, shafi na 9.
Wane darasi ne muka koya a yadda Martha ta bar hidimomi da yawa suka raba hankalinta?
Hankalin Martha ya rabu da yake ta shagala tana dafe-dafen abinci mai yawa. Yesu ya ce ’yar’uwarta Maryamu ta zaɓi abu mafi kyau da yake ta zauna, tana sauraron koyarwarsa. Ya kamata mu mai da hankali don kada abubuwa da ba su da muhimmanci su raba hankalinmu daga abubuwa da suka shafi bautarmu ga Jehobah.—10/15, shafuffuka na 18-20.