Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana Shaida Ikon Allah a Rayuwarka Kuwa?

Kana Shaida Ikon Allah a Rayuwarka Kuwa?

“Hannun Ubangiji kuma za ya sanu ga wajen bayinsa.ISHA. 66:14.

WAƘOƘI: 65, 26

1, 2. Wane tunani ne wasu suke yi game da Allah?

MUTANE da yawa sun ɗauka cewa Allah bai damu da abin da suke yi ba. Ƙari ga haka, wasu sun gaskata cewa Allah bai damu da abin da yake faruwa ga ’yan Adam ba. Bayan da wata mahaukaciyar guguwar Haiyan ta addabi wani sashen ƙasar Filifin a watan Nuwamba ta shekara ta 2013, magajin wani babban birni ya ce: “Allah yana wani waje dabam.”

2 Wasu mutane kuma suna tunanin cewa Allah ba ya ganin abin da suke yi. (Isha. 26:10, 11; 3 Yoh. 11) Halinsu ɗaya ne da waɗanda manzo Bulus ya kwatanta cewa “ba su lamunta su riƙe Allah a cikin saninsu ba.” Irin waɗannan mutane suna yawan “rashin adalci, mugunta, ƙyashi” da kuma “ƙeta.”—Rom. 1:28, 29.

3. (a) Waɗanne tambayoyi ne za mu yi wa kanmu game da Allah? (b) A Littafi Mai Tsarki, mene ne ‘hannun’ Jehobah yake nufi?

3 Mu kuma fa? Ba ma tunani kamar mutane da aka ambata ɗazu don mun san cewa Jehobah yana lura da kome da muke yi. Amma, shin mun gaskata cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana taimakon mu? Ƙari ga haka, muna cikin waɗanda Yesu ya ce za su “ga Allah”? (Mat. 5:8) Za mu sami amsar waɗannan tambayoyin idan muka yi la’akari da labaran Littafi Mai Tsarki game da wasu da suka shaida ikon Allah da kuma waɗanda suka ƙi yin haka. Bayan haka, za mu tattauna yadda kasancewa da bangaskiya za ta taimaka mana mu shaida ikon Allah a rayuwarmu. Yayin da muke tattauna waɗannan darussan, kada mu manta cewa a Littafi Mai Tsarki, ‘hannun’ Allah yana nufin ikon Allah. Yana amfani da ikonsa don ya taimaka wa bayinsa kuma ya kawar da magabtansa.—Karanta Kubawar Shari’a 26:8.

SUN ƘI SHAIDA IKON ALLAH

4. Me ya sa magabtan Isra’ila suka ƙi shaida ikon Allah?

4 A dā mutane da yawa sun shaida yadda Allah ya yi amfani da ikonsa a madadin Isra’ila. Jehobah ya yi abubuwan al’ajabi don ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar kuma bayan haka, ya halaka sarakuna da yawa a madadinsu. (Josh. 9:3, 9, 10) Sarakunan da ke gabashin Urdun sun shaida kuma sun ji waɗannan labaran, amma duk da haka “suka tattaru, domin su yi yaƙi da Joshua da Isra’ila, baki ɗaya.” (Josh. 9:1, 2) Bayan sun soma yaƙin, sun ƙara shaida ikon Allah. Jehobah ya umurci “rana kuwa ta tsaya kurum, wata kuma ya jima, har jama’ar ta ɗauki fansa a bisa magabtansu.” (Josh. 10:13) Amma Jehobah “ya taurara zukatansu [magabtan] har da za su tasar wa Isra’ilawa da yaƙi.” (Josh. 11:20, Littafi Mai Tsarki) Magabtan Isra’ila sun ƙi su amince cewa Allah yana yaƙi a madadin mutanensa kuma hakan ya sa an halaka su.

5. Mene ne mugun Sarki Ahab ya ƙi ya amince da shi?

5 Shekaru da yawa bayan haka, Allah ya ba wa Sarki Ahab damar shaida ikonsa sau da yawa. Iliya ya gaya masa: “Ba za a yi rāɓa ko ruwa ba cikin waɗannan shekaru, sai da cewata.” (1 Sar. 17:1) Jehobah ne ya faɗi wannan maganar ta bakin Iliya, amma Ahab ya ƙi ya amince da hakan. Daga baya, sai Ahab ya ga wuta ya sauko daga sama sa’ad da Iliya ya yi addu’a cewa wuta ya ci hadayarsa. Iliya ya ambata cewa Jehobah zai kawo ƙarshen fārin kuma ya gaya wa Ahab: “Ka gangara, ka da ruwa ya tare ka.” (1 Sar. 18:22-45) Ahab ya ga duka waɗannan abubuwan amma ya ƙi ya amince cewa ikon Allah ne. Wannan misalin da kuma wanda ya gabata suna koya mana darasi mai muhimmanci, sa’ad da Allah yake amfani da ikonsa, wajibi ne mu fahimci hakan.

SUN SHAIDA IKON JEHOBAH

6, 7. Mene ne mazauna Gibiyon da Rahab suka amince da shi?

6 Akasin waɗannan mugayen sarakunan, wasu sun shaida ikon Allah duk da cewa yanayinsu da na waɗanda muka ambata ɗazu ɗaya ne. Alal misali, mazauna Gibiyon sun ƙi yaƙi da Isra’ila kamar yadda yawancin ƙasashen suka yi. A maimakon haka, sun yi sulhu da Isra’ila. Me ya sa? Sun ce: “Bayinka sun zo sabili da sunan Ubangiji Allahnka: gama mun ji labarin ɗaukakarsa, da dukan abin da ya yi.” (Josh. 9:3, 9, 10) Sun yi hikima don sun amince cewa Allah na gaskiya ne yake goyon bayan Isra’ila.

7 Rahab ma ta shaida ikon Allah a abubuwan da suka faru a zamaninsu kuma ta amince da shi. Bayan ta ji labarin yadda Jehobah ya ceci mutanensa, sai ta gaya wa Isra’ilawa biyu da suka je leƙen asiri cewa: “Na sani Ubangiji ya rigaya ya ba ku ƙasar.” Ko da yake matakin da ta ɗauka yana tattare da haɗari, ta gaskata cewa Jehobah zai iya ceton ta da ’yan gidansu.—Josh. 2:9-13; 4:23, 24.

8. Ta yaya wasu Isra’ilawa suka amince da ikon Allah?

8 Akasin mugun Sarki Ahab, wasu Isra’ilawa da suka ga wuta ya sauko daga sama sa’ad da Iliya ya yi addu’a sun amince cewa Allah ne ya nuna ikonsa. Sun ce: “Ubangiji, shi ne Allah; Ubangiji shi ne Allah.” (1 Sar. 18:39) Sun tabbata cewa abin da ya faru ikon Allah ne.

9. Ta yaya za mu iya sanin yadda Jehobah taimakon mutane a yau?

9 Waɗannan misalai masu kyau da marasa kyau da muka tattauna sun taimaka mana mu san yadda muke shaida taimakon Allah. Yayin da muke ƙara sanin Allah da kuma halayensa, da ‘idanun zuciyarmu,’ za mu ga yadda yake taimakonmu. (Afis. 1:18) Hakika, za mu so mu yi koyi da waɗanda a dā da kuma a yau suka amince cewa Jehobah yana goyon bayan mutanensa. Amma, mun tabbata cewa Allah yana taimakon mutane a yau kuwa?

YADDA ALLAH YAKE NUNA IKONSA A YAU

10. Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana taimakon mutane a yau? (Ka duba hoton da ke shafi na 4.)

10 Muna da dalilai da yawa da suka nuna cewa Allah yana taimakon mutanensa. Mun sha jin labaran mutane da suka yi addu’a Allah ya taimake su da kuma yadda Allah ya amsa addu’arsu. (Zab. 53:2) Wani Mashaidi mai suna Allan ya haɗu da wata mata sa’ad da yake wa’azi gida-gida a wani tsibiri da ke Filifin. Bayan ya ce shi Mashaidi ne, sai ta fashe da kuka. Ya ce: “Ta yi addu’a ga Jehobah da safiyar cewa ya turo Shaidunsa. Sa’ad da take matashiya, Shaidun Jehobah sun yi nazari da ita amma bayan ta yi aure kuma ta ƙaura zuwa tsibirin, ba ta sake haɗuwa da su ba. Ga shi Allah ya amsa addu’arta ba tare da ɓata lokaci ba. Hakan ne ya sa ta soma kuka.” A cikin shekara ɗaya, ta ba da kanta ga Jehobah kuma ta yi baftisma.

Kana ganin tabbacin cewa Jehobah yana taimakon mutanensa a yau? (Ka duba sakin layi na 11-13)

11, 12. (a) A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake taimaka wa bayinsa? (b) Ka bayyana yadda Jehobah ya taimaka wa wata ’yar’uwa?

11 Bayin Jehobah da yawa a yau sun shaida ikonsa sa’ad da suka yi gwagwarmaya don su daina halayen banza kamar shan taba ko miyagun kwayoyin ko kuma kallon hotunan batsa. Wasu sun ce sun sha yin ƙoƙari su daina amma ba su yi nasara ba. Amma sa’ad da suka nemi taimakon Jehobah, ya ba su “mafificin . . . iko,” kuma sun daina halayen banza.—2 Kor. 4:7; Zab. 37:23, 24.

12 Jehobah ya sha taimaka wa bayinsa da yawa don su jure da kalubale da suke fuskanta. Alal misali, wata ’yar’uwa mai suna Amy ta fuskanci ƙalubale sa’ad da aka ce ta taimaka wajen gina Majami’ar Mulki da kuma gidan da masu wa’azi a ƙasashen waje za su zauna a wani ƙaramin tsibirin Tekun Fasifik. Ta ce: “Mun sauka a wani ƙaramin hotal kuma kowace rana mukan bi wata hanyar da ke cike da ruwa idan za mu je wajen aiki.” Ba a cika samun ruwa da wutar lantarki a wajen. Ƙari ga haka, Amy tana bukatar ta saba da al’adar mutanen wurin. Ta ƙara cewa: “Abubuwa sun daɗa muni sa’ad da na tsawata wa wata ’yar’uwa da ke aiki tare da mu. A ranar, na koma masaukina ina baƙin ciki ƙwarai. Sa’ad da na shiga cikin ɗakin hotal da na sauka, sai na yi addu’a ga Jehobah ya taimake ni.” Daga baya, aka kawo wutar lantarki, sai Amy ta ɗauki wata mujallar Hasumiyar Tsaro kuma ta karanta wani talifi game da taron sauke makarantar Gilead. An tattauna dukan abubuwan da take fama da su a cikin talifin, wato sabawa da al’adar wasu mutane da yadda za a daina kewar gida da kuma bi da mutanen wata al’ada. Ta ce: “Sai na ji kamar Jehobah ne yake yi min magana da daddaren. Hakan ya ƙarfafa ni in ci gaba da hidimata.”—Zab. 44:25, 26; Isha. 41:10, 13.

13. Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana taimaka wa mutanensa a “kariyar bishara da tabbatar da ita”?

13 Wata hanya da Jehobah yake taimaka wa mutanensa ita ce ta yadda yake sa su yi nasara a “kāriyar bishara da tabbatar da ita.” (Filib. 1:7, LMT) A wasu ƙasashe, an yi yunkurin hana Shaidun Jehobah wa’azin bishara gaba ɗaya. Amma idan muka yi la’akari da nasarori guda 268 da Shaidun Jehobah suka yi a manyan kotuna da kuma guda 24 da suka yi a Kotun Turai na Kāre Hakkin Ɗan Adam daga shekara ta 2000, a bayyane yake cewa babu wanda zai iya hana Allah taimakon bayinsa.—Isha. 54:17; karanta Ishaya 59:1.

14. Mene ne ya sa muka tabbata cewa Allah ne yake taimaka mana a wa’azin da muke yi a faɗin duniya da kuma haɗin kai da muke da shi?

14 Wa’azin bishara da ake yi a faɗin duniya wata hujja ce da ke nuna cewa Allah yana taimakon mutanensa. (Mat. 24:14; A. M. 1:8) Ƙari ga haka, ikon Allah ne yake tabbatar da haɗin kai tsakanin mutanen Jehobah duk da cewa sun fito daga ƙasashe dabam-dabam, kuma hakan ya sa mutane suna cewa Allah yana tare da mu. (1 Kor. 14:25) Hakika, muna da tabbaci sosai cewa Allah yana taimakon mutanensa. (Karanta Ishaya 66:14.) Amma, mene ne ra’ayinka? Shin kana da tabbaci cewa Allah yana taimakonka?

KANA SHAIDA IKON ALLAH A RAYUWARKA KUWA?

15. Ka bayyana dalilin da ya sa ba ma gane yadda Jehobah yake taimakonmu a wani lokaci.

15 Waɗanne dalilai ne za su iya hana mu sanin cewa Jehobah yana taimakonmu? Matsalolin rayuwa za su iya sha kanmu kuma mu manta da yadda Jehobah ya taimaka mana a dā. Sa’ad da sarauniya Jezebel take so ta kashe Iliya, annabin ya ji tsoro kuma ya manta da yadda Jehobah ya taimaka masa a dā. Littafi Mai Tsarki ya ce Iliya “ya yi roƙo domin kansa, shi mutu.” (1 Sar. 19:1-4) Mene ne ya taimaka wa Iliya? Ya dogara ga Jehobah don ya ƙarfafa shi.—1 Sar. 19:14-18.

16. Mene ne muke bukata mu yi don mu ga Allah kamar yadda Ayuba ya gan shi?

16 Ayuba ya kasa fahimtar dalilin da ya sa Jehobah ya bar masifa su faɗa masa don ya damu ainun da matsalolinsa. (Ayu. 42:3-6) Hakazalika, a wani lokaci matsalolinmu za su iya sa mu kasa fahimtar yadda Allah yake taimakonmu. Mene ne zai taimaka mana mu ga taimakon Allah? Wajibi ne mu yi bimbini a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da matsalolinmu. Hakan zai sa mu gane yadda Jehobah yake taimakonmu kuma za mu kusaci Jehobah sosai. Kamar Ayuba, za mu iya ce: ‘Na ji labarinka, . . . amma yanzu idona ya gan ka.’

Shin Jehobah yana amfani da kai wajen taimaka wa mutane su san shi? (Ka duba sakin layi na 17, 18)

17, 18. (a) A waɗanne hanyoyi ne za mu iya sanin cewa Jehobah yana taimaka mana? (b) Ka ba da labarin da ya nuna cewa Allah yana taimakonmu a yau.

17 Ta yaya za mu san cewa Jehobah yana taimakonmu a yau? Ga wasu misalai: Wataƙila kana gani cewa Allah ne ya ja-gorance ka don ka soma bauta masa. Shin ka taɓa sauraron wani jawabi a taro kuma ka ce: “Abin da nake bukata ke nan”? Ko kuma ka shaida yadda Jehobah ya amsa addu’arka. Wataƙila ka tsai da shawarar ƙara ƙwazo a hidimarka kuma ka shaida yadda Jehobah ya taimaka maka ka cim ma burinka. Ko kuma ka yi murabus da aikin da kake yi don ka inganta ibadarka kuma ka shaida gaskiyar alkawarin da ya yi cewa: “Daɗai kuwa ba ni yashe ka ba.” (Ibran. 13:5) Idan muka kusaci Jehobah sosai, za mu fahimci yadda ya taimake mu a hanyoyi dabam-dabam.

18 Wata ’yar’uwa a Kenya mai suna Sarah ta ce: “Na yi addu’a game da wata da ba ta ɗaukan nazarin Littafi Mai Tsarki da nake yi da ita da muhimmanci. Na roƙi Jehobah ya taimaka min in fahimci ko ya dace in daina yin nazarin da ita. Nan da nan bayan na ce ‘Amin,’ sai ɗalibar ta kira ni kuma ta ce tana so ta halarci taro da ni. Hakan ya ba ni mamaki!” Idan ka mai da hankali ga dangantakarka da Allah, kai ma za ka gane yadda Jehobah yake taimaka maka a rayuwarka. Wata ’yar’uwa mai suna Rhonna da ke zama a Asiya ta ce: “Kana bukata ka natsu sosai kafin ka san yadda Jehobah yake taimakonka. Amma idan ka yi hakan, za ka san cewa yana ƙaunar mu ba kaɗan ba!”

19. Mene ne kuma ake bukata daga waɗanda za su ga Allah?

19 Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya: gama su za su ga Allah.” (Mat. 5:8) Ta yaya za mu iya kasancewa da zuciya mai tsabta? Wajibi ne mu kasance da tsarki a tunaninmu kuma mu guji duk wani mugun hali. (Karanta 2 Korintiyawa 4:2.) Idan muka yi aiki tuƙuru don mu kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah kuma muna yin abubuwan da suka dace, hakan zai taimaka mana mu ga Allah. A talifi na gaba, za a tattauna yadda kasancewa da bangaskiya zai sa mu fahimci yadda Allah yake taimakonmu.