“Fansarku Ta Kusa”!
“Ku duba bisa, ku ta da kanku; gama fansarku ta kusa.”—LUK. 21:28.
WAƘOƘI: 133, 43
1. Waɗanne abubuwa ne suka faru a shekara ta 66 bayan haihuwar Yesu? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
A CE kana raye a Urushalima a shekara ta 66 bayan haihuwar Yesu kuma kana ganin abubuwa da yawa suna faruwa. Da farko, babban ma’aikacin Roma mai suna Florus ya saci talanti 17 daga ma’ajin haikali. Nan da nan, Yahudawa suka soma hayaniya kuma suka kashe sojojin Roma da ke Urushalima. Ƙari ga haka, suka sanar cewa sun sami ’yancin kai daga mulkin Roma. Amma, sojojin Roma suka ɗauki mataki nan da nan. Cikin watanni uku, Cestius Gallus, wani gwamnan Roma da ke shugabancin Suriya ya ja-goranci sojoji 30,000 kuma suka kewaye Urushalima. A sakamakon haka, Yahudawa da suka yi tawaye suka ɓoye a cikin ginin da ke kāre haikali. Amma sojojin Roma suka soma ɓata katangar haikalin, kuma duk mutane da ke cikin birnin suka soma tsoro. Yaya za ka ji sa’ad da ka ga dukan waɗannan abubuwa suna faruwa?
2. Wane mataki ne Kiristoci da ke raye a shekara ta 66 bayan haihuwar Yesu suka ɗauka, kuma mene ne ya sa suka sami damar yin hakan?
2 Yesu ya gargaɗi almajiransa cewa: “Sa’anda kuka ga Urushalima Mat. 24:22) Yanzu kana da zarafin bin umurnin Yesu, kuma nan da nan kai da sauran amintattun Kiristoci da ke cikin birnin da kewayensa kuka tsere zuwa duwatsun da ke hayin Kogin Urdun. * Sa’annan, a shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu, sabon rukunin sojojin Roma suka koma Urushalima kuma suka halaka birnin. Amma ka tsira domin ka bi umurnin Yesu.
tana kewaye da dāgar yaƙi, sa’annan ku sani rushewarta ta kusa.” (Luk. 21:20) Amma, za ka iya cewa, ‘Ta yaya zan bi umurnin da Yesu ya bayar sa’ad da yake ba da wannan gargaɗin?’ Yesu ya daɗa cewa: “Sa’annan waɗanda ke cikin Yahudiya su gudu zuwa duwatsu; waɗanda suke cikin tsakiyarta su fita waje; waɗanda ke cikin ƙauyuka kada su shigo ciki.” (Luk. 21:21) Shin ta yaya za ka bar Urushalima da yake sojoji da yawa sun kewaye ta? Sai wani abin mamaki ya faru. Farat ɗaya, sojojin Roma suka janye! Kamar yadda aka annabta, an “gajartar da” harinsu. (3. Wane yanayi ne Kiristoci za su fuskanta ba da daɗewa ba, kuma mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 Nan ba da daɗewa ba, kowannenmu zai fuskanci irin wannan yanayin. Yesu ya gargaɗi Kiristoci cewa za a halaka Urushalima kuma ya yi amfani da abubuwan da suka faru a ƙarni na farko don ya nuna abin da zai faru a lokacin “ƙunci mai-girma.” (Mat. 24:3, 21, 29) Hakika, abin farin ciki ne cewa “taro mai-girma” za su tsira daga wannan bala’i da zai addabi dukan duniya. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 7:9, 13, 14.) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da waɗannan abubuwa da ke nan tafe? Muna bukata mu san amsar wannan tambayar, don hakan zai sa mu tsira. Bari yanzu mu tattauna yadda waɗannan abubuwan da za su faru a nan gaba za su shafi kowannenmu.
YADDA ZA A SOMA ƘUNCI MAI GIRMA
4. Mene ne zai nuna cewa an soma ƙunci mai girma, kuma ta yaya hakan zai faru?
4 Ta yaya za a soma ƙunci mai girma? Littafin Ru’ya ta Yohanna ya ba da amsar ta wajen bayyana yadda za a halaka “Babila Babba.” (R. Yoh. 17:5-7) An kwatanta dukan addinan ƙarya da karuwa. Me ya sa aka yi hakan? Don suna goyon bayan gwamnatocin ’yan Adam maimakon su goyi bayan Yesu da Mulkinsa. Ƙari ga haka, sun yi watsi da ƙa’idodin Allah don su saka hannu a harkokin siyasa. Ibadarsu tana da aibi, ba kamar na shafaffu masu tsarki da suke kama da budurwai ba. (2 Kor. 11:2; Yaƙ. 1:27; R. Yoh. 14:4) Amma, wane ne zai halaka wannan ƙungiya mai kama da karuwa? Jehobah Allah zai sa dabba da ‘launinta ja wur’ ce mai “ƙahoni goma” ta yi “nufinsa.” Waɗannan ƙahonin suna wakiltar dukan rukunin siyasa da ke goyon bayan dabba mai ‘launi ja wur,’ wato Majalisar Ɗinkin Duniya.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 17:3, 16-18.
5, 6. Me ya sa muka ce ba za a halaka dukan mutane masu bin addinai a lokacin da za a halaka Babila Babba ba?
5 Shin hakan zai sa mu kammala cewa za a kashe dukan mambobin addinin ƙarya a lokacin da za a halaka Babila Babba? A’a. Ta wajen ja-gorar ruhu mai tsarki, annabi Zakariya ya rubuta abin da zai faru a lokacin. Ya ambata cewa wani da a dā yake bin addinin ƙarya zai ce: “Ni ba annabi ba ne, ni manomi ne, Zak. 13:4-6, Littafi Mai Tsarki) Hakan ya nuna cewa wasu limamai za su bar addininsu kuma su yi mūsu cewa ba su taɓa bin waɗannan addinan ƙarya ba.
gama ƙasa abar mallakata ce tun ina yaro.’ Idan wani ya tambaye shi cewa, ‘Waɗannan raunukan da ke a hannuwanka fa?’ Zai ce, ‘Ai, raunuka ne da aka yi mini a gidan abokaina.’” (6 Mene ne zai faru da mutanen Allah a wannan lokacin? Yesu ya bayyana cewa: ‘Da ba domin an gajerta da waɗannan kwanaki ba, da ba mai-rai da za ya tsira ba: amma sabili da zaɓaɓɓu za a gajertar da su.’ (Mat. 24:22) Kamar yadda muka tattauna ɗazu, an “gajartar da” ƙunci da ya faru a shekara ta 66 bayan haihuwar Yesu. Hakan ya ba “zaɓaɓu,” wato shafaffu Kiristoci zarafin tsere daga Urushalima da kuma kewayenta. Hakazalika, za a “gajartar da” ƙunci mai girma da zai faru a nan gaba domin “zaɓaɓu.” Ba za a ƙyale ‘ƙahoni goma,’ wato rukunin siyasa su halaka mutanen Allah ba. Maimakon haka, za a sami salama na ɗan lokaci.
LOKACIN GWAJI DA KUMA HUKUNCI
7, 8. Wane zarafi ne za mu samu bayan an halaka ƙungiyoyin addinan ƙarya, kuma yaya amintattun bayin Allah za su kasance dabam a wannan lokacin?
7 Mene ne zai faru bayan a halaka addinan ƙarya? Lokaci ne da za mu nuna ainihin abin da ke cikin zuciyarmu. Yawancin mutane za su nemi mafaka a ƙungiyoyin ’yan Adam da aka kwatanta da “fannun duwatsu.” (R. Yoh. 6:15-17) Amma, a alamance mutanen Allah za su nemi mafaka a wurin Jehobah. Lokacin da aka gajartar da ƙunci mai girma a ƙarni na farko ba lokaci ba ne da Yahudawa za su tuba kuma su zama Kiristoci ba. Amma, dama ce ga Kiristoci su ɗauki mataki kuma su yi biyayya ga umurnin Yesu. Hakazalika, kada mu yi tunani cewa gajartar da ƙunci mai girma da za a yi a nan gaba zai sa mutane da yawa su tuba kuma su soma bauta wa Jehobah. Maimakon haka, masu bauta wa Jehobah za su yi amfani da wannan zarafi su nuna cewa suna ƙaunar Jehobah kuma su goyi bayan ’yan’uwan Kristi.—Mat. 25:34-40.
8 Ko da yake ba mu san ainihin dukan abubuwan da za su faru a wannan lokacin gwaji ba, amma mun san cewa za mu yi wasu sadaukarwa. A ƙarni na farko, Kiristoci sun bar mallakarsu kuma suka jimre mawuyacin yanayi don su tsira. (Mar. 13:15-18) Shin muna a shirye mu yi asara dukiyoyinmu don mu kasance da aminci? Za mu kasance a shirye mu yi duk abin da ake bukata a gare mu don mu kasance da aminci ga Jehobah? Ka yi tunani, a lokacin mu kaɗai ne za mu riƙa bauta wa Allah kamar annabi Daniyel na dā ko da wane irin yanayi ne muke ciki.—Dan. 6:10, 11.
9, 10. (a) Wane saƙo ne mutanen Allah za su yi shelarsa a wannan lokacin? (b) Wane mataki ne magabtan mutanen Allah za su so su ɗauka?
9 Wannan ba zai zama lokacin yin wa’azin ‘bishara ta mulki’ ba. Lokacin yin wa’azi ya wuce, domin ƙarshen zamani zai zo ba da daɗewa ba! (Mat. 24:14) Hakika, mutanen Allah za su yi shelar hukunci da zai shafi dukan mutane. Wataƙila za a yi shelar cewa an kusan halaka wannan mugun zamanin Shaiɗan. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wannan saƙon da ƙanƙara, ya ce: “Ƙanƙara kuma manya manya suka faɗo daga sama bisa mutane, kowane guda nauyinsa ya yi wajen talent ɗaya: mutane fa suka yi saɓon Allah domin alobar ƙanƙara, gama tsananinta da girma ne ƙwarai.”—R. Yoh. 16:21. *
10 Magabtanmu za su ji wannan shelar. Ta wajen ja-gorar ruhu mai tsarki, annabi Ezekiyel ya bayyana abin da Gog na Magog, wato al’ummai da suka haɗa kai za su yi. Ya ce: “Ubangiji Allah ya ce, “a wannan rana tunani zai shiga cikin zuciyarka, za ka ƙirƙiro muguwar dabara, ka ce, ‘Zan haura, in faɗa wa mutanen da ke zama cikin salama, dukansu kuwa suna zaman lafiya, garuruwansu ba garu, ba su da ko ƙyamare,’ don in washe su ganima, in fāda wa wuraren da aka ɓarnatar waɗanda ake zaune a cikinsu yanzu, in kuma fāɗa wa jama’ar da aka tattaro daga cikin al’ummai waɗanda suka sami shanu da dukiya, suna zaune a cibiyar duniya.’” (Ezek. 38:10-12, LMT) Mutanen Allah za su fita dabam, kamar suna cibiyar duniya. Al’ummai za su hasala, kuma zai yi marmarin kai hari ga shafaffu da kuma waɗanda suke goyon bayansu.
11. (a) Mene ne muke bukatar mu tuna game da yadda abubuwa za su faru a lokacin ƙunci mai girma? (b) Mene ne mutane za su yi sa’ad da suka ga alamu a sama?
11 Yayin da muke tattauna abin da zai faru bayan haka, ya kamata mu tuna cewa Kalmar Allah ba ta bayyana dalla-dalla yadda abubuwa za su faru bi da bi ba. Wataƙila wasu abubuwa za su faru kusan a lokaci ɗaya. Sa’ad da Yesu yake annabci game da ƙarshen wannan zamani, ya ce: “A cikin rana da wata da taurari za a ga alamu; a kan duniya al’ummai suna ciwon rai, sun ruɗe saboda rurin teku da ambaliyu; mutane suna suma don tsoro, domin tsammanin al’amuran da ke auko wa duniya kuma: gama za a raurawadda ikokin sammai. Sa’an nan za su ga Ɗan mutum yana zuwa a cikin girgije tare da iko da babbar daraja.” (Luk. 21:25-27; karanta Markus 13:24-26.) Shin za a yi alamu masu ban tsoro da kuma wasu aukuwa a sararin sama a lokacin da wannan annabci zai cika? Wataƙila. Amma sai lokacin ya yi za mu san abin da zai faru. Abin da muka sani shi ne cewa waɗannan alamu za su tsoratar da magabtan Allah kuma ya sa su rikice.
12, 13. (a) Mene ne zai faru sa’ad da Yesu ya zo “da iko da ɗaukaka mai-girma”? (b) Mene ne bayin Allah za su yi a lokacin?
12 Mene ne zai faru a lokacin da Yesu zai zo “da iko da ɗaukaka mai-girma”? Wannan zai zama lokacin sāka wa masu aminci da kuma hukunta marasa aminci. (Mat. 24:46, 47, 50, 51; 25:19, 28-30) A littafin Matta, Yesu ya yi amfani da almarar tumaki da awaki don ya bayyana hakan dalla-dalla, ya ce: “Sa’an da Ɗan mutum za ya zo cikin darajarsa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’annan za ya zauna bisa kursiyin darajarsa: a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai: shi kuwa za ya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi yakan rarraba tumaki da awaki: kuma za ya sanya tumaki ga hannun damansa, amma awaki ga hagu.” (Mat. 25:31-33) Wane hukunci ne za a yi wa tumaki da awaki? Ya kammala almarar da wannan bayanin game da awakin: “Waɗannan kuwa za su tafi cikin hukunci [halaka, New World Translation] na har abada: amma masu-adalci cikin rai na har abada.”—Mat. 25:46.
13 Mene ne awakin za su yi sa’ad da suka san cewa za a halaka su “har abada”? Za su “yi baƙinciki.” (Mat. 24:30) Amma, yaya ’yan’uwan Kristi da abokansu masu aminci za su aikata a wannan lokacin? Tun da sun ba da gaskiya sosai ga Jehobah Allah da kuma Ɗansa, Yesu Kristi, za su bi umurnin Yesu: “Sa’anda waɗannan al’amura suka soma faruwa, ku duba bisa, ku ta da kanku; gama fansarku ta kusa.” (Luk. 21:28) Hakika, za mu kasance da ra’ayin da ya dace da kuma tabbaci cewa cetonmu ya kusa.
ZA SU YI HASKE A MULKIN
14, 15. Wane aikin tattarawa ne za a yi bayan Gog na Magog sun soma kai wa mutanen Allah hari, kuma mene ne wannan aikin ya ƙunsa?
14 Mene ne zai faru sa’ad da Gog na Magog sun soma kai wa mutanen Allah hari? Littafin Matta da na Markus sun ce: “[Ɗan mutum] za ya aike mala’iku, za ya tattara zaɓaɓunsa daga ƙusurwoyi huɗu, daga iyakar nisan duniya zuwa iyakar nisan sama.” (Mar. 13:27; Mat. 24:31) Wannan tattarawa ba ya nufin lokacin da aka fara zaɓan shafaffu kuma ba ya nufin hatimi na ƙarshe da za a yi wa shafaffu da suka rage a duniya. (Mat. 13:37, 38) Za a buga musu wannan hatimi kafin a soma ƙunci mai girma. (R. Yoh. 7:1-4) Wane aikin tattarawa ne Yesu ya ambata a nan? Lokaci ne da raguwar shafaffu da ke duniya za su sami ladarsu na zuwan sama. (1 Tas. 4:15-17; R. Yoh. 14:1) Hakan zai faru bayan Gog na Magog ya soma kai wa mutanen Allah hari. (Ezek. 38:11) A lokacin ne waɗannan kalmomin Yesu za su cika: ‘Sa’annan masu-adalci za su haskaka kamar rana a cikin Mulkin Ubansu.’—Mat. 13:43. *
15 Mutane da yawa a Kiristendam sun gaskata cewa za a kai Kiristoci sama da jikinsu na zahiri. Kuma suna ganin cewa za su ga lokacin da Yesu zai dawo ya yi mulki da duniya. Amma, Littafi Mai Tsarki ya nuna dalla-dalla cewa dawowar Mat. 24:30) Littafi Mai Tsarki ya kuma ce “nama da jini ba su da iko su gāji mulkin Allah ba.” Saboda haka, za a sauye kamanin waɗanda za su je sama “farat ɗaya, da ƙyaftar ido, da ƙarar ƙaho na ƙarshe.” * (Karanta 1 Korintiyawa 15:50-53.) Farat ɗaya, za a tattara shafaffu da suke duniya a lokacin.
Yesu a alamance ne ba a zahiri ba. Ya ce: “Alama ta Ɗan mutum za ta bayyana a sama” kuma Yesu zai zo “bisa gizagizai na sama.” (16, 17. Mene ne zai faru kafin a yi auren Ɗan rago a sama?
16 Za a soma shirye-shirye na ƙarshe don auren Ɗan ragon muddin dukan shafaffu 144,000 sun tafi sama. (R. Yoh. 19:9) Amma, wani abu zai faru kafin wannan aure mai ban farin ciki. Ka tuna cewa kafin sauran shafaffu da suka rage a duniya su tafi sama, Gog zai kai wa mutanen Allah hari. (Ezek. 38:16) Ta yaya mutanen Allah za su kasance? A duniya, zai zama kamar mutanen Allah ba su da kāriya. Za su bi umurnin da aka ba da a zamanin Sarki Jehoshaphat: “Babu bukata ku yi wannan yaƙi: ku yi shiri, ku tsaya shuru, ku ga ceton Ubangiji a wurinku, ya Yahuda da Urushalima; kada ku ji tsoro, kada ku yi fargaba.” (2 Laba. 20:17) Amma, yanayin zai kasance dabam a sama. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki yake magana game da lokacin da dukan shafaffu 144,000 sun je sama, Ru’ya ta Yohanna 17:14 ta ambata abin da magabtan mutanen Allah za su yi: ‘Waɗannan kuma za su yi gāba da Ɗan Rago, Ɗan Rago kuma za ya ci su, gama shi ne Ubangijin iyayengiji, da Sarkin sarakuna: su kuma waɗanda ke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, masu-aminci, za su yi nasara.’ Yesu tare da shafaffu 144,000 abokan sarautarsa za su ceci mutanen Allah da ke duniya.
17 Bayan yaƙin Armageddon, za a ɗaukaka suna mai tsarki na Jehobah. (R. Yoh. 16:16) A wannan lokacin, za a yanke wa dukan masu kama da awaki “hukunci na har abada.” Za a kawar da dukan mugunta daga duniya, kuma taro mai girma za su tsira daga sashe na ƙarshe na ƙunci mai girma. A ƙarshe, za a yi auren Ɗan rago da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna. (R. Yoh. 21:1-4) * Dukan waɗanda suka tsira za su sami amincewar Allah kuma za su amfana daga ƙaunarsa da karimcinsa. Hakika, za a ji daɗin wannan bikin auren! Muna ɗokin ganin abin da zai faru a wannan ranar, ko ba haka ba?—Karanta 2 Bitrus 3:13.
18. Tun da yake abubuwa masu ban farin ciki suna nan tafe, me ya kamata mu ƙudura niyyar yi?
18 Tun da yake waɗannan abubuwa masu ban farin ciki za su faru a nan gaba, me ya kamata kowannenmu ya riƙa yi a yanzu? Ta wajen ja-gorar ruhu mai tsarki, manzo Bitrus ya ce: “Da ya ke fa dukan waɗannan abu za su narke haka nan, waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma? Kuna sauraron ranar Allah, kuna kuwa marmarin zuwanta ƙwarai . . . Domin wannan, ƙaunatattu, tun da kuke sauraron waɗannan al’amura, sai ku ba da anniya a tarar da ku cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi a gabansa.” (2 Bit. 3:11, 12, 14) Bari mu ƙudura niyyar kasancewa da tsarki a bautarmu kuma mu goyi bayan Sarkin Salama.
^ sakin layi na 2 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2012, shafuffuka na 25 zuwa 26.
^ sakin layi na 9 Talent wani ma’aunin gwada nauyi da kuma darajar kuɗi ne a zamanin Manzo Yohanna. Kilo 20.4 shi ne talent ɗaya. Ka duba littafin nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah, sashe na 18.
^ sakin layi na 14 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, shafuffuka na 13 zuwa 14.
^ sakin layi na 15 Shafaffu da suke raye a duniya a lokacin ba za su tafi da jikinsu na zahiri zuwa sama ba. (1 Kor. 15:48, 49) Wataƙila za a kawar da jikinsu yadda aka kawar da jikin Yesu.
^ sakin layi na 17 A cikin Zabura ta 45, an ambata yadda waɗannan abubuwa za su faru bi da bi. Da farko Sarkin zai yi yaƙin, bayan hakan za a yi bikin auren.