Ka Sani?
Ƙasar Isra’ila ta dā tana da daji sosai kamar yadda labaran Littafi Mai Tsarki suka nuna?
AN AMBATA a cikin Littafi Mai Tsarki cewa wasu wurare a Ƙasar Alkawari suna da daji sosai da kuma itatuwa da “yawa.” (1 Sar. 10:27; Josh. 17:15, 18) Duk da haka, da yake babu daji a wurare da yawa a ƙasar a yau, wasu mutane za su iya yin shakka ko abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne.
Littafin nan Life in Biblical Israel ya bayyana cewa “akwai daji a ƙasar Isra’ila ta dā sosai fiye da yanzu.” Itatuwan Aleppo pine (Pinus halepensis) da oak (Quercus calliprinos), da kuma terebinth (Pistacia palaestina) ne suka fi yawa a tuddan ƙasar. Ƙari ga haka, akwai itatuwan ɓaure da yawa (Ficus sycomorus) a kwarin da ake kira Shephelah, wato daga jerin tuddan da ke tsakiyar ƙasar zuwa gaɓar Bahar Rum.
Littafin nan Plants of the Bible ya ce babu itatuwa ko kaɗan a wasu yankunan Isra’ila yanzu. Me ya jawo hakan? Littafin ya bayyana cewa hakan ya soma faruwa a hankali. Ya ce: “’Yan Adam sun ci gaba da kawar da wannan dajin don su faɗaɗa gonakinsu da wuraren kiwon dabbobi. Ƙari ga haka, suna yanke itatuwa don yin gine-gine da kuma dahuwa.”