Ka Yi Koyi da Wanda Ya Yi Mana Alkawarin Rai na Har Abada
“Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.” —AFIS. 5:1.
1. Wace baiwa ce za ta taimaka mana mu yi koyi da halayen Allah?
JEHOBAH ya halicce mu da wata baiwa, wato yadda za mu iya saka kanmu a cikin yanayin wasu. Saboda haka, za mu iya sanin yadda wani yanayi zai iya kasancewa ko da ba mu taɓa samun kanmu a cikin yanayin ba. (Karanta Afisawa 5:1, 2.) Ta yaya za mu yi amfani da wannan baiwar yadda ya dace? Mene ne ya kamata mu yi don kada ta zama illa a gare mu?
2. Ta yaya wahalar da muke sha yake shafan Jehobah?
2 Hakika, muna farin ciki cewa Allah ya yi wa shafaffu masu aminci alkawari cewa za su je sama, kuma “waɗansu tumaki” na Yesu za su zauna a aljanna a duniya. (Yoh. 10:16; 17:3; 1 Kor. 15:53) A lokacin, ba wanda zai fuskanci irin wahalar da muke fama da ita a yau. Jehobah ya san irin wahalar da muke fuskanta a yau. A lokacin da Isra’ilawa suka sha wahala a ƙasar Masar, Jehobah bai ji daɗi ba sam. “Cikin dukan ƙuncinsu ya ƙuntata.” (Isha. 63:9) Ƙarnuka bayan haka, magabtan Yahudawa sun yi ƙoƙarin hana su gina haikali, amma Allah ya ƙarfafa su sa’ad da ya ce: ‘Gama shi wanda ya taɓa ku, ya taɓa ƙwayar idona.’ (Zak. 2:8) Kamar yadda mahaifiya take ƙaunar jaririnta, Jehobah yana ƙaunar mutanensa kuma yana ɗaukan mataki don ya cece su. (Isha. 49:15) Jehobah zai iya sa kansa cikin yanayin da mutane suke ciki, kuma idan muka yi hakan, muna koyi da shi.—Zab. 103:13, 14.
YESU YA YI KOYI DA JEHOBAH KUMA YA SO MUTANE
3. Mene ne ya nuna cewa Yesu ya ji tausayin mutane?
3 Yesu ya fahimci yanayin mutane da ke cikin mawuyacin hali, ko da bai taɓa samun kansa a yanayinsu ba. Alal misali, yawancin mutane a lokacin suna tsoron shugabannin addini da suka kafa musu dokoki da suka wuce gona da iri. (Mat. 23:4; Mar. 7:1-5; Yoh. 7:13) Ba a taɓa yaudarar Yesu ba kuma shi ba mai tsoro ba, amma ya fahimci yanayin mutane ko da yake bai taɓa samun kansa a cikin yanayinsu ba. Saboda haka, “sa’ad da ya ga taron, ya yi juyayi a kansu, domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Mat. 9:36) Yesu yana ƙaunar mutane kuma yana tausayinsu kamar Ubansa.—Zab. 103:8.
4. Wane mataki ne Yesu ya ɗauka sa’ad da ya ga yadda mutane suke wahala?
4 Sa’ad da Yesu ya ga irin wahalar da mutane suke sha, hakan ya motsa shi ya taimaka musu. Kamar Ubansa, Yesu ya so mutane. Bayan da Yesu da manzanninsa suka je wa’azi a wuri mai nisa, sun tsai da shawarar zuwa inda babu mutane don su huta. Da yake Yesu ya ji tausayin mutanen da suke jiransa, ya ba da kansa don ya “koya masu abu da yawa.”—Mar. 6:30, 31, 34.
KA SO MUTANE KAMAR YADDA JEHOBAH YA SO SU
5, 6. Ta yaya za mu bi da mutane idan muna so mu yi koyi da Allah? Ka ba da misali. (Ka duba hoton da ke shafi na 24.)
5 Bi da mutane yadda ya kamata yana nuna cewa muna bin misalin Allah. Alal misali, a ce wani mai suna Ali, yana la’akari da wani tsoho da ba ya iya karatu don ba ya gani sosai. Har ila, zuwa wa’azi gida-gida yana masa wuya. Ali ya tuna da furucin Yesu cewa: “Kamar yadda kuke so mutane su yi maku, ku yi masu hakanan kuma.” (Luk. 6:31) Saboda haka, Ali ya tambayi kansa, ‘Me nake so mutane su riƙa yi mini?’ Sai ya ce, ‘Ina so su buga ƙwallo tare da ni!’ Amma tsohon ba zai iya buga ƙwallo ba. Abin da Yesu yake nufi a nan shi ne ya dace mu yi wa kanmu wannan tambayar, ‘Mene ne zan so mutane su yi mini da a ce ina cikin yanayinsu?’
6 Ali bai tsufa ba, amma zai iya tunanin yadda yanayinsa zai kasance idan ya tsufa. A ce Ali ya yi la’akari da wannan tsohon kuma ya saurare shi sa’ad da yake masa magana. Babu shakka, hakan ya taimaka masa ya fahimci dalilin da ya sa yake yi wa tsofaffi wuya su karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yi wa’azi gida-gida. Da Ali ya fahimci halin da ɗan’uwan yake ciki, sai ya ga cewa yana bukatar taimako kuma yana so ya taimaka masa. Mu ma za mu iya yin hakan. Muna yin koyi da ƙaunar Allah idan muka fahimci yanayin ’yan’uwanmu kuma muka taimaka musu.—1 Kor. 12:26.
7. Ta yaya za mu fahimci yanayin da ’yan’uwanmu suke ciki?
7 Bai da sauƙi mu fahimci yanayin da wasu mutane suke fama da shi. Mutane da yawa suna fama da matsalolin da ba mu sani ba. Wasu suna wahala saboda rashin lafiya ko wani rauni da suka ji ko Romawa 12:15; 1 Bitrus 3:8.
kuma tsufa. Har ila, wasu suna fama da baƙin ciki ko kuma yawan alhini don an ci zarafinsu. Ƙari ga haka, mambobin wasu ’yan’uwa ba sa bauta wa Jehobah kuma wasu ’yan’uwa suna rainon yaransu ba tare da taimakon abokin aurensu ba. Kowane mutum yana da nasa damuwa da wataƙila ba mu taɓa fuskanta ba. Ta yaya za mu yi koyi da ƙaunar Allah a irin waɗannan yanayin? Ta wurin sauraron mutane a hankali kuma mu yi ƙoƙari don mu fahimci yanayinsu. Hakan zai sa mu yi koyi da ƙaunar Jehobah kuma mu ɗauki mataki don a taimaka musu. Yanayin mutane da suke bukatar taimako ya bambanta, duk da haka, za mu iya ƙarfafa su kuma mu taimaka musu a wasu hanyoyi.—KarantaKA ZAMA MAI KIRKI KAMAR JEHOBAH
8. Mene ne ya taimaka wa Yesu ya yi alheri?
8 Yesu ya ce: “Gama shi [Maɗaukaki] mai-alheri ne ga marasa-godiya da miyagu.” (Luk. 6:35) Hakika, Yesu ya yi koyi da Allah a yin alheri. Mene ne ya taimaka wa Yesu ya yi hakan? Ya bi da mutane da alheri ta wurin yin la’akari da yadda furucinsa da ayyukansa za su shafi yadda mutane suke ji. Alal misali, wata mace da aka san ta da yin zunubi ta zo wurin Yesu tana kuka kuma tana share ƙafafun Yesu da hawayenta. Yesu ya fahimci cewa wannan matar ta tuba kuma ya san cewa idan bai nuna mata alheri ba, za ta yi baƙin ciki sosai. Saboda haka, ya yabe ta kuma ya gafarta mata zunubanta. Sa’ad da wani Ba-farisi ya nuna cewa bai ji daɗin abin da Yesu ya yi ba, Yesu ya yi masa magana da sanin yakamata.—Luk. 7:36-48.
9. Mene ne zai taimaka mana mu yi koyi da yadda Allah yake alheri? Ka ba da misali.
9 Ta yaya za mu yi koyi da misalin Allah wajen yin alheri? Manzo Bulus ya ce: “Kada bawan Ubangiji kuwa ya yi husuma, amma sai ya yi nasiha ga duka, mai-sauƙin koyarwa, mai-haƙuri.” (2 Tim. 2:24) Mutane masu nasiha ko basira suna tunanin yadda za su bi da wasu yanayoyi ba tare da ɓata wa mutane rai ba. Ka yi la’akari da yadda za mu nuna basira sa’ad da muka sami kanmu a waɗannan yanayi dabam-dabam: A ce shugabanka a wurin aiki ba ya aikinsa yadda ya kamata. Mene ne za ka yi? Wani ɗan’uwa ya halarci taro bayan ya yi watanni bai halarta ba. Me za ka gaya masa? A ce kana so ka yi wa wani wa’azi sai ya gaya maka cewa: “Ban da lokaci yanzu ina aiki.” Za mu nuna masa sanin yakamata kuwa? Idan matarka ta tambaye ka, “Me ya sa ba ka gaya min shirin da ka yi game da ranar Asabar ba?” Za ka ba da amsa da sanin yakamata kuwa? Ta wurin saka kanmu a yanayin mutane da kuma fahimtar yadda furucinmu zai shafe su, za mu san yadda za mu yi musu magana da kuma matakan da za mu ɗauka da za su nuna mu masu kirki ne kamar Jehobah.—Karanta Misalai 15:28.
KA ZAMA MAI HIKIMA KAMAR JEHOBAH
10, 11. Mene ne zai taimaka mana mu yi koyi da hikimar Allah? Ka ba da misali.
10 Yin tunani a kan abubuwan da ba su taɓa faruwa da mu ba zai taimaka mana mu yi koyi da hikimar Jehobah kuma mu san yadda wani mataki da za mu ɗauka zai iya shafan wasu. Hikima tana ciki halayen Jehobah na musamman, kuma idan ya ga dama, zai iya sanin sakamakon wasu abubuwan da za su faru. Ko da yake ba za mu iya yin hakan ba, amma muna iya yin tunanin sakamakon wani mataki da muke so mu ɗauka. Isra’ilawa ba su yi la’akari da abin da zai faru idan suka yi K. Sha. 31:29, 30; 32:28, 29.
wa Allah rashin biyayya ba. Duk da abubuwa masu kyau da Allah ya tanadar musu, Musa ya san cewa za su yi wa Jehobah rashin biyayya. Saboda haka, Musa ya yi wannan waƙar a gaban jama’ar Isra’ila duka: “Gama su al’umma ne mara-hangen gaba, babu basira kuma a cikinsu. Da ma suna da hikima, har da za su gane wannan, su lura da ƙarƙonsu!”—11 Idan muna so mu yi koyi da Allah a nuna hikima, ya kamata mu yi tunanin abubuwan da za su faru idan muka ɗauki wasu matakai. Alal misali, idan muna fita zance, zai dace mu san cewa sha’awar juna za ta iya zama mana tarko. Saboda haka, ba za mu tsai da shawara ko kuma mu yi wani abin da zai sa mu ɓata dangantakarmu da Jehobah ba. Maimakon haka, zai dace mu bi wannan shawarar Littafi Mai Tsarki: “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya ɓuya: Amma wawaye sukan bi ciki, su sha wuya.”—Mis. 22:3.
KA GUJI YIN TUNANIN BANZA
12. Ta yaya yin tunanin banza yake tattare da illa?
12 Mutum mai hikima ya san cewa yin tunani zai iya zama kamar wuta. Idan muka yi amfani da wuta da kyau, zai iya dafa mana abinci. Amma wuta zai iya ƙone gida har ya halaka waɗanda ke ciki idan ba a mai da hankali wajen yin amfani da ita ba. Hakazalika, tunani yana da kyau idan yana taimaka mana mu yi koyi da halayen Jehobah. Amma tunanin banza yana tattare da hadari. Alal misali, idan muka mai da hankali ga tunanin banza, hakan zai iya sa mu aikata abin da bai da kyau. Hakika, yin tunani a kan abubuwa marasa ɗa’a zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah.—Karanta Yaƙub 1:14, 15.
13. Wace irin rayuwa ce Hawwa’u ta yi tunaninta?
13 Ka yi la’akari da yadda mace na farko Hawwa’u ta yi sha’awar cin “itace na sanin nagarta da mugunta.” (Far. 2:16, 17) Macijin ya gaya mata: “Ba lallai za ku mutu ba: gama Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su buɗe, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.” Hawwa’u ta “lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu.” Saboda haka, “sai ta ɗiba ’ya’yansa, ta ci; ta kuma ba mijinta tare da ita, shi kuwa ya ci.” (Far. 3:1-6) A ra’ayin Hawwa’u, akwai wani abu mai kyau a maganar da Shaiɗan ya yi mata. Wato, za ta iya tsai da shawara wa kanta a batun nagarta da mugunta maimakon wani ya gaya mata. Irin wannan tunanin ya jawo mummunar sakamako. Littafi Mai Tsarki ya ce ta wurin mijin Hawwa’u, wato Adamu, “zunubi ya shigo cikin duniya . . . mutuwa kuwa ta wurin zunubi.”—Rom. 5:12.
14. Ta yaya Littafi Mai Tsarki yake taimaka mana mu guji lalata?
14 Zunubin da Hawwa’u ta yi a Lambun Adnin ba zina ba ne. Duk da haka, Yesu ya yi gargaɗi game da tunanin banza. Ya ce: “Dukan wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Mat. 5:28) Ƙari ga haka, Bulus ya yi gargaɗi: “Kada kuwa a shirya ma jiki kafa da za a bi sha’awoyinsa.”—Rom. 13:14.
15. Wace irin dukiya ce ya kamata mu ajiye, kuma me ya sa?
15 Wani tunanin banza kuma shi ne mutum ya riƙa tunanin zama mai arziki ba tare da yin la’akari da ibadarsa ga Jehobah ba. Hakika, dukiyar mutum a tunaninsa, yana kama da “ganuwa mai-tsawo” da ke kāre shi. (Mis. 18:11) Yesu ya ba da labari don ya nuna mugun yanayin mutum “mai-ajiye wa kansa dukiya, shi kuwa ba mawadaci ba ne ga Allah.” (Luk. 12:16-21) Jehobah yana farin ciki idan muka yi abin da yake faranta masa rai. (Mis. 27:11) Hakika, za mu yi farin ciki sosai idan muka ajiye wa kanmu “dukiya cikin sama.” (Mat. 6:20) Kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah ita ce dukiya mafi tamani.
KA DAINA DAMUWA
16. Mene ne zai iya taimaka mana mu rage alhini?
16 Idan muna yawan tunanin tara wa kanmu “dukiya a duniya” za mu riƙa yin alhini. (Mat. 6:19) Yesu ya yi amfani da kwatanci don ya nuna cewa “ɗawainiyar duniya, da ruɗin dukiya” za su iya hana mu saka Mulkin Allah farko. (Mat. 13:18, 19, 22) Wasu kuma suna yawan tunani a kan munanan abubuwan da za su iya faruwa da su. Amma yawan yin alhini zai sa mu ciwo kuma ya ɓata dangantakarmu da Allah. Bari mu dogara ga Jehobah kuma mu tuna cewa “damuwa takan hana wa mutum farin ciki, amma kalmomin alheri za su sa shi ya yi murna.” (Mis. 12:25, Littafi Mai Tsarki) Maganar alheri daga wani da ya fahimci yanayinmu zai sa mu yi murna. Bayyana ra’ayinka wa iyaye masu bi ko abokin aure ko kuma wani amini mai dangantaka mai kyau da Allah zai sa ka dogara ga Allah kuma ka rage yin alhini.
17. Ta yaya Jehobah yake taimakonmu sa’ad da muke alhini?
17 Jehobah ne kaɗai ya fahimci yanayinmu da kyau. Manzo Bulus ya ce: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filib. 4:6, 7) Zai dace mu yi tunani a kan waɗanda suke taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da aminci. Waɗannan sun ƙunshi ’yan’uwa da dattawa da bawan nan mai aminci da mala’iku da Yesu da kuma Jehobah.
18. Ta yaya yin tunani zai iya taimaka mana?
18 Kamar yadda muka riga muka tattauna, yin tunani zai taimaka mana mu yi koyi da halayen Allah kamar ƙauna. (1 Tim. 1:11; 1 Yoh. 4:8) Za mu yi farin ciki idan muka so mutane kuma muka yi la’akari da yadda ayyukanmu za su shafi wasu kuma idan muka daina yin alhini da zai iya sa mu baƙin ciki. Bari mu yi amfani da baiwar nan da Allah ya ba mu don mu yi tunani game da begenmu kuma mu yi koyi da halayen Jehobah kamar su ƙauna da alheri da hikima da kuma farin ciki.—Rom. 12:12.