Sun Hangi Abubuwan da Aka Yi Alkawarinsu
‘Ba su rigaya sun amshi alkawarai ba, amma daga nesa suka [hange] su.’—IBRAN. 11:13.
1. Ta yaya za mu amfana ta wurin yin tunanin abubuwan da za su faru? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
ALLAH ya ba mu baiwar yin tunanin abubuwan da ba mu gani ba. Hakan yakan sa mu tsai da shawarwari masu kyau kuma mu sa rai a abubuwa masu kyau da za su faru a nan gaba. Jehobah yana iya sanin abubuwan da za su faru, kuma a cikin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana wasu abubuwa da za su faru a nan gaba. Muna iya yin tunanin abubuwan da za su faru, kuma yin hakan zai taimaka mana mu kasance da bangaskiya.—2 Kor. 4:18.
2, 3. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu yi tunani a kan abubuwan da za su faru da gaske? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 Hakika, mukan yi tunanin abubuwan da ba za su taɓa faruwa ba. Alal misali, ƙaramar yarinya tana iya yin tunanin hawan malam-buɗe-littafi, hakan wasiƙar jaki ce. Amma sa’ad da Hannatu take tunanin lokacin da za ta kai ɗanta Sama’ila hidima a mazauni, ta tabbata cewa hakan zai faru. Ta yi wannan tunanin bisa abin da ta tsai da shawara za ta yi, kuma hakan ya taimake ta ta cika alkawarin da ta yi wa Jehobah. (1 Sam. 1:22) Idan muna bimbini a kan abin da Allah ya yi mana alkawarinsa, hakan ba wasiƙar jaki ba ce.—2 Bit. 1:19-21.
3 Babu shakka, amintattu da yawa a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki sun yi tunani a kan abubuwan da Allah ya yi musu alkawarinsu. Ta yaya waɗannan mutane suka amfana ta wurin yin hakan? Kuma ta yaya mu ma za mu amfana ta yin tunani a kan abubuwa masu ban al’ajabi da Allah ya ce zai yi wa ’yan Adam?
YIN TUNANI A KAN ALKAWURAN ALLAH YA ƘARFAFA BANGASKIYARSU
4. Me ya taimaka wa Habila ya yi tunani cewa Allah zai cika alkawarinsa?
4 Habila ne mutum na farko da ya kasance da bangaskiya ga abubuwan da Jehobah ya yi alkawarinsa. Ya san abin da Jehobah ya gaya wa macijin bayan Adamu da Hawwa’u suka yi zunubi: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: Shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Far. 3:14, 15) Habila bai san yadda hakan zai faru ba. Amma, ya yi tunani sosai a kan wannan alkawarin kuma ya fahimci cewa za a ‘ƙuje duddugen’ wani don ’yan Adam su zama kamiltattu kamar yadda Adamu da Hawwa’u suke kafin su yi zunubi. Habila ya ba da gaskiya cewa Jehobah zai cika alkawarinsa, kuma saboda haka, Allah ya amince da hadayarsa.—Karanta Farawa 4:3-5; Ibraniyawa 11:4.
5. Me ya sa yin tunanin abin da zai faru a nan gaba ya ƙarfafa Anuhu?
5 Anuhu wani ne da ya ba da gaskiya ga Allah. Ya yi rayuwa tsakanin mugaye da suka yi maganganun banza game da Allah. Anuhu ya yi annabci cewa Jehobah: ‘Da rundunan tsarkakansa, garin ya hukumta shari’a bisa dukan mutane, domin shi kayar da dukan masu-fajirci kuma a kan dukan ayyukansu na fajirci da suka yi cikin fajircinsu, da dukan maganganu na bātanci waɗanda masu-zunubi masu-fajirci suka ambace shi da su.’ (Yahu. 14, 15) A matsayinsa na wanda yake da bangaskiya, wataƙila Anuhu ya yi tunanin yadda duniya za ta zama idan babu mugunta.—Karanta Ibraniyawa 11:5, 6.
6. Mene ne wataƙila Nuhu ya ci gaba da tunaninsa bayan Rigyawa?
6 Da yake Nuhu yana da bangaskiya, ya tsira a lokacin da aka yi Rigyawa. (Ibran. 11:7) Bayan Rigyawar, ya miƙa hadayar dabbobi ga Jehobah domin bangaskiyarsa. (Far. 8:20) Kamar Habila, ya tabbata cewa lokaci yana zuwa da Allah zai kawar da zunubi da mutuwa. Nuhu ya kasance da bangaskiya da bege har a lokacin da Nimrod ya soma sarauta kuma ya sa mutane su yi wa Jehobah rashin biyayya. (Far. 10:8-12) Wataƙila, abin da ya ƙarfafa Nuhu shi ne tunanin lokacin da Allah zai kawar da mulkin danniya, da zunubi da kuma mutuwa. Mu ma za mu iya yin bimbini game da irin wannan yanayin kuma lokacin ya kusa!—Rom. 6:23.
SUN YI TUNANIN LOKACIN DA ALKAWURAN ALLAH ZA SU CIKA
7. Wane yanayi ne Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu suka yi bimbini a kai?
7 Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu sun yi bimbini a kan rayuwa da za su yi a nan gaba domin Allah ya yi musu alkawari cewa dukan al’umman duniya za su sami albarka ta wurin zuriyarsu. (Far. 22:18; 26:4; 28:14) ’Ya’yansu za su yi yawa sosai kuma za su zauna a Ƙasar Alkawari da Allah ya ba su. (Far. 15:5-7) Domin Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu sun san cewa Allah zai cika alkawarinsa, sun yi tunanin yadda iyalansu za su zauna a wannan ƙasar. Ƙari ga haka, tun lokacin da Adamu da Hawwa’u suka yi zunubi, Jehobah ya taimaka wa bayinsa masu aminci su fahimci cewa zai sake ba wa ’yan Adam damar yin rayuwa har abada.
8. Mene ne ya taimaka wa Ibrahim ya kasance da bangaskiya sosai?
8 Wataƙila yadda Ibrahim ya yi tunanin alkawuran da Allah ya yi masa ne ya taimake shi ya yi ayyuka da suka nuna yana da bangaskiya sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce ko da yake Ibrahim da wasu bayin Allah masu aminci ba “su rigaya sun amshi alkawarai” lokacin da suke da rai ba amma ‘daga nesa suka [hange] su, suka yi masu maraba.’ (Karanta Ibraniyawa 11:8-13.) Ibrahim ya san cewa Jehobah ya cika alkawuransa a dā kuma ya tabbata cewa dukan alkawuran da ya yi don nan gaba za su cika.
9. Ta yaya kasancewa da bangaskiya ya amfani Ibrahim?
9 Ibrahim ya yi nufin Allah don ya ba da gaskiya cewa Jehobah zai cika alkawarin da ya yi masa. Alal misali, ya bar birnin Ur kuma ya ƙi ya yi zaman dindindin a biranen Kan’ana. Za a halaka waɗannan biranen domin sarakunansu kamar sarakunan Ur ba sa bauta wa Jehobah. (Josh. 24:2) A dukan rayuwarsa, Ibrahim “yana tsumayen birnin da ke da tussa, wanda mai-sifansa da mai-aikinsa Allah ne.” (Ibran. 11:10) Ibrahim ya hangi kansa yana zaune a ƙarƙashin gwamnati na dindindin da Jehobah ne mai sarauta. Habila da Anuhu da Nuhu da Ibrahim da kuma wasu kamar su sun ba da gaskiya cewa Allah zai ta da matattu kuma sun yi ɗokin yin rayuwa a duniya a ƙarƙashin Mulkin Allah, wato “birnin da ke da tussa.” Yin tunanin a kan samun wannan albarka ya sa sun ƙara kasancewa da bangaskiya ga Jehobah.—Karanta Ibraniyawa 11:15, 16.
10. Ta yaya alkawarin ɗa da aka yi wa Ibrahim ya amfani Saratu?
10 Alal misali, Saratu matar Ibrahim, sa’ad da take shekara 90 ba ta haifi yara ba. Amma ta kasance da ra’ayin da ya dace kuma ta ba da gaskiya ga alkawuran da Jehobah ya yi. Ta yi tunanin yadda zuriyarta za su more abubuwan da Jehobah ya yi alkawarinsu. (Ibran. 11:11, 12) Me ya sa ta kasance da irin wannan tabbaci? Jehobah ya gaya wa mijinta: “Ni ma zan albarkace ta, im ba ka ɗa kuma daga gareta: hakika, zan albarkace ta, za ta zama uwar al’ummai kuma: sarakunan al’ummai za su kasance daga gareta.” (Far. 17:16) Bayan Allah ya sa Saratu ta haifi Ishaƙu, ta tabbata cewa sauran alkawuran da Jehobah ya yi wa Ibrahim za su cika. Mu ma za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu idan muka yi tunanin dukan abubuwa masu ban al’ajabi da Jehobah ya yi mana alkawari!
YA MAI DA HANKALI GA LADAR
11, 12. Ta yaya Musa ya ci gaba da ƙaunar Jehobah?
11 Wani mutum kuma da ya ba da gaskiya kuma ga Jehobah shi ne Musa. Ya so Jehobah da dukan zuciyarsa. Musa ya girma a gidan sarkin Masar kuma da hakan ya sa ya yi sha’awar sarauta da dukiya. Amma, iyayen Musa sun koya masa game da Jehobah da nufinsa cewa zai ’yantar da Ibraniyawa kuma ya kai su Ƙasar Alkawari. (Far. 13:14, 15; Fit. 2:5-10) Musa ya yi tunanin yadda Allah zai yi wa mutanensa albarka kuma hakan ya taimaka masa ya so Jehobah kuma ya yi watsi da dukiya da sarauta.
12 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Ta wurin bangaskiya Musa, sa’anda ya yi girma, ya ƙi yarda a ce da shi ɗan ɗiyar Fir’auna; yana gwammace a wulakance shi tare da mutanen Allah, da ya ji daɗin nishatsin zunubi domin ’yan kwanaki; yana maida zargi domin Kristi wadata ne mafi girma bisa ga dukiyar Masar: Ibran. 11:24-26.
gama yana sauraron sakamakon.”—13. Ta yaya Musa ya amfana ta wajen yin tunani game da alkawarin da Allah ya yi?
13 Yayin da Musa ya yi tunani sosai a kan abin da Jehobah ya yi alkawari zai yi wa Isra’ilawa, hakan ya sa ya ƙara ba da gaskiya ga Allah kuma ya so shi sosai. Kamar sauran ’yan Adam masu tsoron Allah, wataƙila ya yi bimbini game da lokacin da Jehobah zai kawar da mutuwa. (Ayu. 14:14, 15; Ibran. 11:17-19) Shi ya sa Musa ya so Allahn da ya ji tausayin Ibraniyawa da kuma sauran ’yan Adam. Musa ya ci gaba da bauta wa Allah a dukan rayuwarsa domin ya ba da gaskiya ga Jehobah kuma ya so shi sosai. (K. Sha. 6:4, 5) Har a lokacin da Fir’auna ya ce zai kashe Musa, bai ji tsoro ba domin ya san cewa Jehobah zai albarkace shi a nan gaba.—Fit. 10:28, 29.
KA YI TUNANI A KAN ABUBUWAN DA MULKIN ALLAH ZAI YI
14. Wane irin tunani marar amfani ne mutane suke yi a yau?
14 Mutane da yawa a yau suna tunani game da abubuwan da ba za su taɓa faruwa ba. Alal misali, ko da yake talakawa ne, suna tunanin yadda za su yi arziki sosai da kuma samun kwanciyar rai duk da cewa rayuwa yanzu tana cike da “wahala . . . da baƙin ciki.” (Zab. 90:10) Suna tunani cewa za su yi rayuwa ba tare da alhini ba a gwamnatin ’yan Adam, amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Mulkin Allah ne kawai zai magance matsalolin ’yan Adam. (Dan. 2:44) Mutane da yawa suna ganin cewa Allah ba zai halaka wannan mugun zamani ba, amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za a kawo ƙarshen gwamnatin ’yan Adam. (Zaf. 1:18; 1 Yoh. 2:15-17) Irin wannan tunani da mutane suke yi wasiƙar jaki ce.
15. (a) Ta yaya Kiristoci za su amfana ta wajen yin bimbini game da begensu? (b) Ka ambata wani abu da kake so ka gani sa’ad da Allah ya cika alkawuransa.
15 A matsayinmu na Kiristoci, ana ƙarfafa mu mu yi tunanin begenmu, ko na zuwa sama ne ko kuma na yin rayuwa a cikin aljanna a duniya. Shin kana ganin kanka kana more dukan abubuwan da Allah ya yi mana alkawarinsa? Babu shakka, yin bimbini a kan abin da za ka yi a lokacin da Allah zai cika alkawuransa zai sa ka farin ciki. Wataƙila kana ganin kanka kana rayuwa har abada. Ka yi tunanin yadda kake aiki tare da wasu don mai da wannan duniya ta zama aljanna. Maƙwabtanka suna ƙaunar Jehobah kamar yadda kake ƙaunarsa. Kana da ƙoshin lafiya da kuzari kuma kana jin daɗin rayuwa. Waɗanda suke kula da aikin mai da duniya aljanna suna faranta maka rai domin suna ƙaunar ka sosai. Kuma kana farin cikin yin amfani da iyawarka da baiwarka domin dukan abubuwan da kake yi suna amfanar mutane da kuma girmama Allah. Alal misali, kana taimakon waɗanda aka ta da daga matattu kuma kana koya musu game da Jehobah. (Yoh. 17:3; A. M. 24:15) Irin wannan tunanin ba mafarki ba ne. Waɗannan abubuwan za su faru tabbas domin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ke nan.—Isha. 11:9; 25:8; 33:24; 35:5-7; 65:22.
DALILIN DA YA SA MUKE TATTAUNA BEGENMU
16, 17. Ta yaya za mu amfana ta wajen yin magana game da begenmu?
16 Sa’ad da muke gaya wa ’yan’uwanmu abin da za mu so mu yi a sabuwar duniya, muna taimaka wa juna mu yi tunanin wannan kyakkyawan yanayi. Ko da yake babu wani a cikinmu da ya san ainihin yadda yanayinsa zai kasance a sabuwar Rom. 1:11, 12.
duniya, amma idan muka tattauna abubuwan da muke so mu yi a lokacin, muna ƙarfafa juna kuma muna nuna cewa mun ba da gaskiya ga alkawuran Allah. Sa’ad da manzo Bulus ya kai wa ’yan’uwansa a Roma ziyara, babu shakka sun ji daɗin ‘ƙarfafa’ juna kuma muna bukatar yin hakan a wannan mawuyacin zamani.—17 Yin tunani game da alkawarin da Jehobah ya yi zai taimaka mana mu rage yin alhini. Wataƙila irin wannan damuwa ne ya sa manzo Bitrus ya ce wa Yesu: “Mun bar abubuwa duka, mun bi ka; me za mu samu fa?” Yesu ya taimaka wa Bitrus da sauran almajiran da ke tare da shi su yi tunani game da alkawarin da Allah ya yi sa’ad da ya ce: “Gaskiya ni ke ce maku, ku da kuka biyo ni, cikin sabonta sa’ad da Ɗan mutum za ya zauna bisa kursiyin darajarsa, ku kuma za ku zauna bisa kursiyi goma sha biyu, kuna mallakar kabilai goma sha biyu na Isra’ila. Kuma kowanene ya bar gidaje, ko ’yan’uwa maza, ko ’yan’uwa mata, ko uba, ko uwa, ko ’ya’ya, ko ƙasashe, sabili da sunana, za ya sami riɓi ɗari; za ya kuma gāji rai na har abada.” (Mat. 19:27-29) Bitrus da wasu almajirai suna iya yin tunanin aikin da za su yi a gwamnati da za ta yi sarauta bisa duniya kuma su taimaka wa ’yan Adam da ke duniya su zama kamiltattu.
18. Ta yaya yin tunani game da cikar alkawuran Allah zai amfane mu a yau?
18 Bayin Jehobah da ke duniya suna amfana ta wajen yin tunani game da cikar alkawuran Allah. Habila ya yi tunani game da alkawarin Jehobah, hakan ya sa ya ba da gaskiya kuma ya kasance da tabbataccen bege. Ibrahim ya kasance da bangaskiya sosai ga Jehobah domin ya yi tunanin yadda annabci game da ‘zuriya’ da Allah ya yi alkawarinsa zai cika. (Far. 3:15) Musa ya ‘saurari sakamakon,’ wato ya sa rai ga ladar da zai samu, shi ya sa ya so Jehobah kuma ya ba da gaskiya gare shi. (Ibran. 11:26) Yin tunani baiwa ce kuma yayin da muke yin tunanin yadda Jehobah zai cika alkawuransa, za mu so Jehobah sosai kuma za mu daɗa ba da gaskiya gare shi. Za mu tattauna yadda za mu yi amfani da wannan baiwar da kyau a talifi na gaba.