Ka Kulla Dangantaka ta Kud da Kud da Jehobah Kuwa?
“Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” —YAƘ. 4:8.
1. Me ya sa muke bukatar mu ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah?
IDAN kai Mashaidin Jehobah ne da ya yi baftisma, kana da wani abu mai tamani, wato dangantakarka da Allah. Amma da yake muna cikin duniyar Shaiɗan kuma muna fama da ajizancinmu, dangantakarmu da Allah tana cikin haɗari. Dukan Kiristoci ne suke fuskantar wannan mawuyacin yanayi. Saboda haka, wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu wajen ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah.
2. Ta yaya za mu ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah?
2 Shin ka ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah? Za ka so ka ƙarfafa ta? Yaƙub 4:8 ta gaya mana yadda za mu yi hakan: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” Ka lura cewa Jehobah ya ce zai ɗauki mataki kuma ya bukace mu ma mu ɗauki mataki. Idan muka ɗauki mataki don mu kusaci Allah, shi ma zai yi hakan. Idan ka ci gaba da yin hakan, Jehobah zai zama amini a gare ka kuma dangantakarku za ta yi danƙo. Ƙari ga haka, za ka ji yadda Yesu ya ji sa’ad da ya ce: ‘Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, . . . Na san shi.’ (Yoh. 7:28, 29) Waɗanne matakai na musamman ne za ka ɗauka don ka kusaci Jehobah?
3. A waɗanne hanyoyi ne muke tattaunawa da Jehobah?
3 Sadarwa da Jehobah a kai a kai tana da muhimmanci idan muna so mu kusace shi. Ta yaya za ka iya sadarwa da Allah? Ta yaya za ka iya sadarwa da wani aboki da ke zama a wuri mai nisa? Wataƙila, za ku riƙa rubuta wa juna wasiƙa ko kuma ku riƙa magana ta waya. Kana yi wa Jehobah magana ta yin addu’a a kai a kai. (Karanta Zabura 142:2.) Idan kana karanta Kalmar Allah kullum kuma kana yin bimbini a kai, tamkar kana ba wa Jehobah damar tattaunawa da kai. (Karanta Ishaya 30:20, 21.) Bari mu tattauna yadda irin wannan abota tsakanin mutane biyu zai ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah kuma ya sa mu kusace shi sosai.
JEHOBAH YANA MAGANA DA MU TA NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI
4, 5. Ta yaya Jehobah yake tattaunawa da kai ta Kalmarsa? Ka ba da misali.
4 Babu shakka, ka amince cewa abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki saƙo ne daga Allah zuwa ga ’yan Adam. Shin Littafi Mai Tsarki ya ambaci matakan da za ka ɗauka don ka kusaci Jehobah ne? Ƙwarai kuwa! Ta yaya? Yayin da kake karanta da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki, ka yi la’akari da yadda kake bin abin da ya fada kuma ka yi tunanin yadda za ka yi amfani da abin da ya ce a yanayinka, idan ka yi hakan, tamkar kana sauraron Jehobah yayin da yake maka magana ta Kalmarsa. Hakan zai sa ka zama amininsa.—Ibran. 4:12; Yaƙ. 1:23-25.
5 Alal misali, ka karanta kuma ka yi bimbini a kan waɗannan kalaman Yesu: “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya.” Idan kana ganin ka saka al’amura na Mulki kan gaba a rayuwa, za ka tabbata cewa Jehobah ya amince da kai. Amma, idan kana ganin cewa kana bukata ka sauƙaƙa rayuwarka kuma ka mai da hankali ga biɗan al’amura na Mulki, to Jehobah yana gaya maka inda kake bukatar ka yi gyara don ka kusace shi.—Mat. 6:19, 20.
6, 7. (a) Ta yaya nazarin Littafi Mai Tsaki yake shafan yadda muke ƙaunar Jehobah da kuma yadda yake ƙaunar mu? (b) Wace manufa ce ya kamata mu kasance da ita sa’ad da muke nazari?
6 Yin nazarin Littafi Mai Tsarki yana sa mu san inda muke bukatar mu yi 1 Korintiyawa 8:3.
gyara a ibadarmu. Yana kuma sa mu san halayen Jehobah masu ban sha’awa kuma mu ƙara ƙaunarsa. Idan muka so Jehobah sosai, shi ma zai ƙara ƙaunarmu kuma hakan zai sa mu kasance da dangantaka ta kud da kud da shi.—Karanta7 Idan muna so mu kusaci Jehobah sosai, yana da muhimmanci mu kasance da kyakkyawar manufa yayin da muke nazarin Kalmarsa. Yohanna 17:3 ta ce: ‘Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.’ Saboda haka, ba kawai mu sami ilimi game da Jehobah ba amma ya kamata mu kasance da manufar ‘sanin’ halayensa da kyau.—Karanta Fitowa 33:13; Zab. 25:4.
8. (a)Wane irin tunani ne za mu iya yi game da yadda Jehobah ya bi da Sarki Azariah, kamar yadda aka bayyana a 2 Sarakuna 15:1-5? (b) Ta yaya sanin Jehobah zai sa mu daina shakka game da yadda yake yin abubuwa?
8 Yayin da muke ƙara sanin Jehobah, ba za mu damu ainun ba idan ba mu fahimci dalilin da sa ya ɗauki wasu matakai kamar yadda aka ambata a wasu labaran Littafi Mai Tsarki ba. Alal misali, sa’ad da ka karanta labarin Sarki Azariah na Yahuda da kuma yadda Jehobah ya bi da shi, yaya kake ji? (2 Sar. 15:1-5) Ka lura cewa a zamaninsa “jama’a suna yanka hadaya suna ƙona turare a cikin masujadai,” amma Azariah da kansa ya ci gaba da “aika nagarta a gaban Ubangiji.” Duk da haka, “Ubangiji kuwa ya bugi sarkin, ya zama kuturu har ran mutuwarsa.” Me ya sa? Ba a bayyana dalilin a cikin labarin ba. Shin ya kamata mu damu ne ko mu ɗauka cewa Jehobah ya yi masa horo ba gaira ba dalili? Idan muka san halayen Jehobah sosai, ba za mu yi irin wannan tunanin ba. Don Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana ba da ‘horo’ yadda ya dace. (Irm. 30:11) Sanin hakan zai tabbatar mana cewa Jehobah yana shari’a bisa adalci ko da ba mu san dalilin da ya sa ya yi wa Azariah horo ba.
9. Wane ƙarin bayani ne ya sa muka san dalilin da ya sa Jehobah ya addabe Azariah da kuturta?
9 Muna da ƙarin bayani game da wannan labarin a wani sashen Littafi Mai Tsarki. Sarki Azariah yana da wani suna dabam. (2 Sar. 15:7, 32) Shi ne Sarki Uzziah da aka ambata a 2 Labarbaru 26:3-5, 16-21. Ko da yake, Uzziah ya yi abin da ya dace a gaban Jehobah, daga baya “zuciyarsa ta habaka, ya kuwa jawo halakarsa.” Saboda fahariya, sarkin ya so ya yi aikin da Allah ya danƙa wa firistoci kaɗai. Firistoci tamanin da ɗaya suka gaya masa cewa abin da yake so ya yi ba daidai ba. Shin ya ji shawararsu ne? A’a. A maimakon haka, fahariya ta sa ya “hasala.” Shi ya sa Jehobah ya addabe shi da kuturta!
10. Me ya sa bai kamata mu riƙa bukatar bayani a kowane abin da Jehobah ya yi ba, kuma ta yaya za mu ƙara tabbata cewa a kowane lokaci al’amuran Jehobah suna da kyau?
10 Wane darasi mai muhimmanci ne muka koya? Ba a bayyana wasu labaran Littafi Mai Tsarki dalla-dalla kamar wannan ba. Shin idan kana karanta irin waɗannan labaran, za ka yi tunani cewa abin da Allah ya yi ba daidai ba ne? Ko kuma za ka yi tunani cewa Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da isashen bayani da ya tabbatar mana cewa Jehobah yana yin abin da ya dace a koyaushe kuma ya fi kowa sanin nagarta da mugunta? (K. Sha. 32:4) Yayin da muke ƙara sanin Jehobah, za mu so shi sosai kuma ba za mu riƙa bukatar bayani a kan yadda yake bi da kowane al’amari ba don mun amince da shi sosai. Za ka ƙara son Jehobah ta wurin nazari da yin bimbini a kan yadda yake sa mutane su san shi yayin da suke karanta Kalmarsa. (Zab. 77:12, 13) A sakamako, dangantakarka da Jehobah za ta daɗa yin danƙo.
KA RIƘA YIN MAGANA DA JEHOBAH TA YIN ADDU’A
11-13. Ta yaya ka san cewa Jehobah yana jin addu’a? (Ka duba shafi na 19.)
11 Za mu kusaci Jehobah idan muna yin addu’a. Idan muna yabonsa muna masa godiya, kuma muna roƙonsa ya ja-gorance mu. (Zab. 32:8) Amma idan kana so ka kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah, wajibi ne ka gaskata cewa shi mai jin addu’a ne.
12 Wasu mutane suna da’awa cewa addu’a tana da amfani ne kawai don tana kwantar mana da hankali. Sun ce ba wai Allah yana jin addu’o’i ba. Kana magance matsalarka ne don wasu matakai na musamman da kake ɗaukawa. Ko da yake irin wannan tunani yana taimakawa, amma ta yaya za ka san cewa tabbas Jehobah yana amsa addu’o’inka?
13 Alal misali, kafin Yesu ya zo duniya, ya lura cewa Jehobah ya amsa addu’o’in bayinsa da ke duniya. A lokacin da yake hidima a duniya, Yesu ya bayyana ra’ayinsa ga Ubansa ta yin addu’a. Akwai lokacin da ya soma addu’a daga dare har safe. Da ya yi hakan ne da ce ya dauka cewa Jehobah ba ya sauraronsa? (Luk. 6:12; 22:40-46) Shin da zai koya wa almajiransa yadda ake yin addu’a ne, idan ya dauka cewa Jehobah ba ya jin addu’a? Hakika, Yesu ya san cewa Jehobah yana jin addu’a. Akwai lokacin da Yesu ya ce: “Uba, na gode maka da ka ji ni. Ko dā ma na sani kana ji na kullum.” Saboda haka, mu kasance da tabbaci cewa Jehobah “mai jin addu’a” ne.—Yoh. 11:41, 42; Zab. 65:2.
14, 15. (a) Ta yaya muke amfana idan muka ambaci ainihin abubuwa da ke damunmu a cikin addu’a? (b) Ta yaya addu’a ta taimaka wa wata ’yar’uwa ta ƙarfafa dangantakarta da Jehobah?
14 Idan kana ambata wasu abubuwa na musamman sa’ad da kake addu’a, za ka fahimci yadda Jehobah yake amsa addu’o’inka. Hakan zai sa mu dogara ga Jehobah
sosai. Ƙari ga haka, yayin da kake ƙara gaya wa Jehobah duk abubuwan da ke damunka, za ka kusace shi sosai.15 Ka yi la’akari da abin da ya faru da Kathy. * Ba ta jin daɗin wa’azi ko da yake tana fita wa’azi a kai a kai. Ta ce: “Ba na sha’awar yin wa’azi. Abin nufi, ba na sha’awarsa ko kaɗan. Sa’ad da na yi ritaya daga aiki, wani dattijo ya ƙarfafa ni na soma hidimar majagaba na kullum, har ya ba ni fom na cika. Na tsai da shawara na soma hidimar majagaba, kuma kullum ina yin addu’a cewa Jehobah ya sa sha’awar yin wa’azi ta shiga zuciyata.” Shin Jehobah ya ji addu’arta ne? Ta ce: “Na yi shekara uku yanzu ina hidimar majagaba. A hankali, na inganta yadda nake wa’azi domin ina yawan fita wa’azi kuma wasu ’yan’uwa mata suna taimaka mini sosai. Yanzu, yadda nake ji game da wa’azi ya wuce so, ma’ana, ina jin daɗinsa sosai. Ƙari ga haka, yanzu na fi kasancewa kusa da Jehobah.” Hakika, Jehobah ya ji addu’ar Kathy kuma hakan ya sa ta ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi.
MU YI IYA ƘOƘARINMU
16, 17. (a) Mene ne ya kamata mu yi don mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah? (b) Wane ƙalubale na musamman ne za mu tattauna a talifi na gaba?
16 Ya kamata mu riƙa inganta dangantakarmu da Jehobah a kowane lokaci. Idan muna so Allah ya kusace mu, wajibi ne mu ɗauki mataki don mu kusace shi. Saboda haka, bari mu ci gaba da tattaunawa da Allah ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma addu’a. Idan muka yi hakan, dangantakarmu da Jehobah za ta yi danƙo, kuma hakan zai taimaka mana mu jimre matsaloli.
17 Amma, a wani lokaci mukan fuskanci wani gwaji na musamman duk da cewa muna yin addu’a a kai a kai. Hakan yana iya sa mu daina dogara da Jehobah. Za mu iya ɗauka cewa ba ya jin addu’o’inmu ko kuma ba ya ganin mu da mutunci. Mene ne za mu yi a irin wannan yanayin don mu kasance da tabbaci cewa muna da dangantaka ta kud da kud da Allah? Za mu tattauna wannan batun a talifi na gaba.
^ sakin layi na 15 An canja sunan.