Tambaya Mai Sauƙi da Za Ka Iya Yi
ꞌYarꞌuwa Mary da mai gidanta John, a suna zama a wata ƙasa da mutane da yawa daga Filipin suna zuwa su yi aiki, kuma ita da mai gidanta suna jin daɗin yi musu waꞌazi. A lokacin annobar korona, Mary ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a ƙasarsu da kuma a wasu ƙasashe. Ta yaya ta yi hakan?
Mary takan tambayi ɗalibanta cewa, “Kin san wata da za ta so ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki?” Idan suka ce e, sai ta ce, zan so ki haɗa ni da su. Yin wannan tambayar mai sauƙi yakan kawo sakamako mai kyau. Me ya sa muka ce hakan? A yawancin lokuta, mutanen da suke jin daɗin abin da suke koya daga Littafi Mai Tsarki suna son gaya wa ꞌyan gidansu da abokansu game da abin da suke koya. Mene ne ya faru saꞌad da Mary take yi wa ɗalibanta wannan tambayar?
Wata ɗalibar Mary mai suna Jasmin ta haɗa ta da mutane huɗu da suke so su yi nazari. Ɗaya daga cikinsu mai suna Kristine ta ji daɗin nazarin sosai har ta gaya wa Mary cewa su riƙa nazari sau biyu a maƙo. Saꞌad da Mary ta tambaye ta ko ta san wata da za ta so ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki, Kristine ta ce, “E, zan haɗa ki da abokaina.” Ba da daɗewa ba, Kristine ta haɗa Mary da abokanta huɗu da suke son su yi nazari. Daga baya, Kristine ta sake haɗa ta da wasu abokanta, abokan kuma suka haɗa ta da abokansu.
Kristine ta so ꞌyan iyalinta da ke Filipin ma su soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Sai ta gaya wa ꞌyarta Andrea game da nazarin. Da farko dai, Andrea ta ɗauka cewa, ‘Shaidun Jehobah ꞌyan ƙungiyar asiri ne, ba su gaskata da Yesu ba, kuma suna amfani da Tsohon Alkawari ne kawai.’ Amma bayan sun yi nazari sau ɗaya kawai, ta gano cewa abubuwan da take tunani game da Shaidun Jehobah ba gaskiya ba ne. A duk lokacin da ta koyi wani sabon abu daga Littafi Mai Tsarki, takan ce, “Da yake yana cikin Littafi Mai Tsarki, gaskiya ne!”
Da shigewar lokaci, Andrea ta haɗa Mary da abokanta biyu da wata da suke aiki tare, kuma sun soma nazari. Ƙari ga haka, saꞌad da Mary da Andrea suke nazari, ashe ꞌyarꞌuwar mahaifin Andrea mai suna Angela da ba ta gani tana sauraron su, amma Mary ba ta sani ba. Ana nan sai Angela ta gaya wa Andrea ta haɗa ta da Mary don a soma nazari da ita. Angela ta ji daɗin abin da take koya sosai. A cikin wata ɗaya, ta haddace nassosi da yawa kuma ta so a yi nazari da ita sau huɗu a maƙo! Da taimakon Andrea, Angela ta soma halartan taro babu fashi ta bidiyo.
Da Mary ta gano cewa mijin Kristine mai suna Joshua yana zama kusa saꞌad da suke nazari, sai ta tambaye shi ko zai so ya yi nazari da shi. Joshua ya ce, “Zan zauna in saurara amma kada ki yi min wata tambaya, idan kika yi min tambaya, zan tafi.” A cikin minti biyar bayan sun soma nazarin, ya yi tambayoyi fiye da matarsa Kristine, kuma ya so ya ci-gaba da nazarin.
Wannan tambaya mai sauƙi da Mary ta yi ya sa an soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Da yake suna da yawa sosai, ta gaya wa wasu ꞌyanꞌuwa su taimaka mata. Duka-duka, Mary ta soma nazari da mutane 28 daga ƙasashe huɗu.
Ɗalibarta na farko wato Jasmin da aka ambata a wannan labarin, ta yi baftisma a watan Afrilu 2021. Kristine ta yi baftisma a Mayu 2022 kuma ta koma ƙasar Filipin don ta kasance da iyalinta. Ɗalibai biyu da Kristine ta haɗa su da Mary ma sun yi baftisma. Bayan ꞌyan watanni, Angela ma ta yi baftisma kuma ta zama majagaba na kullum. Mijin Kristine wato Joshua da ꞌyarsu Andrea da wasu ɗalibai da yawa suna samun ci-gaba.
A ƙarni na farko, mutane da yawa sun gaya wa iyalinsu da abokansu abubuwan da suka koya game da Yesu. (Yoh. 1:41, 42a; A. M. 10:24, 27, 48; 16:25-33) Don haka, ka tambayi ɗalibanka ko sun san wani da yake so ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Yin wannan tambayar zai iya sa ka sami mutane da yawa da za su so su yi nazarin Littafi Mai Tsarki.
a An canja sunayen.