Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hulda Ta Samu Abin da Take So

Hulda Ta Samu Abin da Take So

A TSIBIRIN Sangir Besar na ƙasar Indonisiya, akwai wasu ꞌyanꞌuwa mata guda uku da suke aiki tare a gaɓar teku. Mutane sun san su sosai a tsibirin domin yadda suke koya wa mutane Kalmar Allah. Amma wannan karon, wani aiki dabam suke yi a gaɓar tekun, ba waꞌazi ba.

Tsirbirin Sangir Besar da ke arewancin Indonisiya

Da farko, sukan shiga cikin tekun kuma su ɗibi duwatsu. Wasu duwatsun girmansu ya kai na ƙwallon ƙafa. Bayan sun kwashi duwatsun, sai su zauna a kan kujera kuma su farfasa su zuwa ƙanana-ƙanana yadda girmansu ba zai kai na kwan kaji ba. Bayan haka, sai su sa duwatsun a cikin bokitin ruba kuma su kai su gida. Idan suka isa gida, sai su zuba duwatsun a cikin manyan buhuhuna don a iya loda su a cikin manyan motoci, kuma a yi amfani da su wajen yin hanya.

Hulda tana kwashe duwatsu a gaɓar teku

Ɗaya daga cikin ꞌyanꞌuwa matan sunanta Hulda. Yanayin da take ciki ya sa tana yin aikin fiye da sauran. Dā ma tana amfani da kuɗin da take samu daga aikin don ta biya bukatun iyalinta. Amma yanzu tana so ta ɗan yi ajiya don ta yi wani abu dabam. Tana so ta sayi babbar waya don ta iya sauƙar da manhajar JW Library®. Hulda ta san cewa bidiyoyi da littattafan da ke manhajar za su iya taimaka mata ta iya yin waꞌazi da kyau, kuma ta ƙara fahimtar Littafi Mai Tsarki.

Hulda ta yi wata ɗaya da rabi tana aiki na saꞌoꞌi biyu kowace safiya don ta iya fasa duwatsu da yawa da za su iya cika ƙaramar tirela. A-kwana-a-tashi, ta samu kuɗin da za ta iya siyan babbar waya.

Hulda da babbar wayarta

Hulda ta ce, “Ko da yake na gaji sosai don farfasa duwatsu da na yi, da na sayi wayar, na manta da dukan wahalar da na sha. Yanzu wayar tana taimaka min in iya yin waꞌazi da kyau kuma in iya yin shiri da kyau kafin in je taro.” Ta kuma ce wayar ta taimaka mata sosai saꞌad da ake annobar korona domin a lokacin ana yin taro da waꞌazi ta waya ne. Muna taya Hulda murna don ta samu abin da take so.