Darussa Daga Tsuntsaye
Ka “tambayi . . . tsuntsayen sararin sama za su koya maka. A cikin dukan waɗannan, wane ne a cikinsu bai sani cewa hannun Yahweh ne ya yi su ba?” —Ayuba 12:7, 9, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.
FIYE da shekaru 3,000 da suka shige, Ayuba ya gane cewa za mu iya koyan darussa da yawa daga tsuntsayen da Allah ya halitta. Yanayin rayuwarsu ya sa ana yawan amfani da su wajen yin kwatanci da kuma adon magana. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da tsuntsaye don ya koya mana darussa masu kyau game da rayuwa da kuma dangantakarmu da Allah. Bari mu bincika kaɗan daga cikinsu.
GIDAN TSATTSEWA
Mazaunan Urushalima sun san cewa tsuntsuwar nan tsattsewa tana yin gidanta a ƙarƙashin rufin gidajen mutane. Wasu sun yi gidajensu a haikalin Sulemanu. Wataƙila waɗannan tsuntsayen da suke yin gidajensu a haikali a kowace shekara suna yin ‘ya’ya a wurin kuma babu wanda yake damunsu.
Wani ɗan Korah da ya rubuta Zabura ta 84, wanda ke hidimar mako ɗaya a haikali bayan kowane wata shida ya lura da gidajen waɗannan tsuntsayen a haikalin. Ya so ya zama kamar waɗannan tsuntsayen da ke zama dindindin a haikalin Jehobah. Ya ce: “Ina misalin daɗin mazaunanka, Ya Ubangiji mai-runduna! Raina yana marmari, har ya yi yaushi domin muradin gidajen Ubangiji.” Har “tsada ta sami wa kanta gida, Tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa inda za ta ajiye ya’yanta, bagadinka ke nan, ya Ubangiji mai-runduna, Sarkina, Allahna.” (Zabura 84:1-3) Shin mu da yaranmu muna marmarin zuwa gidan Ubangiji inda mutanen Allah suke?—Zabura 26:8, 12.
ZALƁE TA SAN LOKACINTA
Annabi Irmiya ya ce: “Ko zalɓe cikin sama tana sane da kwanakinta.” Babu shakka, ya san yadda zalɓe suke wucewa ta Ƙasar Alkawari. A lokacin sanyi, an ce fararen zalɓe fiye da 300,000 suna ƙaura daga Afirka zuwa Arewacin Turai ta Kwarin Urdun. Suna da wani abu da aka yi su da shi da ke sa su san lokacin ƙaura. Kamar yadda wasu tsuntsayen sararin sama suke, zalɓe “suna lura da lokacin zuwansu.”—Irmiya 8:7.
Littafin nan Collins Atlas of Bird Migration ya ce: “Wani abin mamaki game da tsuntsaye shi ne yadda suke sanin lokacin ƙaura.” Jehobah ya ba tsuntsaye basirar sanin lokacin ƙaura, amma ya ba mutane hikimar sanin lokatai. (Luka 12:54-56) Hikimar da aka halicci mutane da ita tana sa su san cewa muna kwanaki na ƙarshe kuma wannan hikimar ba ɗaya take da basirar da zalɓe take da ita ba. Isra’ilawa a zamanin Irmiya sun yi kunnen kashi ga waɗannan alamun. Allah ya gaya musu matsalarsu, ya ce: “Sun ƙi maganar Ubangiji; wace irin hikima ke garesu fa.”—Irmiya 8:9.
A yau, muna da dalilai da yawa na gaskata da cewa muna rayuwa ne a lokacin da Littafi Mai Tsarki ya kira “kwanaki na ƙarshe.” (2 Timotawus 3:1-5) Shin za ka yi koyi da zalɓe kuma ka san alamun zamanin da muke ciki?
GAGGAFA TANA HANGEN NESA
An ambaci gaggafa sau da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki kuma ana yawan ganin wannan tsuntsuwar a Ƙasar Alkawari. Gaggafa takan “hangi ganima” ko abinci daga gidanta kuma “daga nesa idanunta sukan tsinkayo” ko gano abubuwa. (Ayuba 39:27-29) Idanun gaggafa suna ganin abubuwan da ke nesa, shi ya sa take iya ganin zomo da ke nisan kilomita ɗaya.
Kamar yadda idanun gaggafa suke hango abu “daga nesa,” Jehobah yana iya sanin abin da zai faru a nan gaba. Jehobah ya ce shi: “Mai-bayana ƙarshe [ne] tun daga mafarin, tun zamanin dā kuma al’amuran da ba a rigaya an aika ba tukuna.” (Ishaya 46:10) Za mu kasance da hikima da kuma basira idan muka bi umurnin Jehobah.—Ishaya 48:17, 18.
Littafi Mai Tsarki ya kwatanta waɗanda suka dogara ga Jehobah da gaggafa. Ya ce: “Waɗanda ke sauraro ga Ubangiji za su sabonta ƙarfinsu; da fukafukai kamar gaggafa za su tashi sama.” (Ishaya 40:31) Gaggafa tana shawagi da taimakon iska mai ɗumi. Da zarar ta sami wannan iskar, sai ta baza fukafukanta kuma ta riƙa haurawa sama. Idan babu iska, gaggafa ba za ta iya tashi sama ba. Ba za ta iya yin kome da ƙarfin kanta ba. Hakazalika, ya kamata waɗanda suka dogara ga Jehobah su riƙa neman taimakonsa kuma kada su manta cewa shi ne ya yi alkawarin tanadar musu da “mafificin girman iko.”—2 Korintiyawa 4:7, 8.
‘YADDA KAZA TAKAN TATTARA ‘YA’YANTA’
Yesu ya tsaya ya kalli babban birnin Yahudawa, jim kaɗan kafin a kashe shi kuma ya ce: “Ya Urushalima, Urushalima, wanda kike kisan annabawa, kina jejjefe waɗanda an aiko a gareki! Sau nawa ina so in tattara ‘ya’yanki, kamar yadda kaza takan tattara ‘yan tsākinta ƙarƙashin fikafikanta, amma ba ku yarda ba!”—Matta 23:37.
Wani abu kuma da tsuntsaye suke yi sosai shi ne kāre ‘ya’yansu. Tsuntsayen da ba sa tashi sama, kamar kaji suna mai da hankali sosai wajen kāre ‘ya’yansu daga haɗari. Idan kaza ta ga shaho yana zagayawa kusa da inda take, tana kiran ‘ya’yanta maza-maza kuma ta saka su a ƙarƙashin fukafukanta. Ƙananan kaji da ba su da wayo za su iya ɓoyewa a ƙarƙashin fukafukan uwarsu idan ana rana da kuma ruwan sama. Hakazalika, Yesu ya so ya kāre mazaunan Urushalima kuma ya ba su wurin fakewa. Haka ma a yau, Yesu yana kiranmu mu zo don mu sami wurin hutu daga wahala da muke sha a wannan duniyar.—Matta 11:28, 29.
Akwai darussa da yawa da za mu iya koya daga waɗannan tsuntsayen. Yayin da kake kallonsu sa’ad da suke yin abubuwa, ka yi ƙoƙari ka tuna da wasu kwatancin da aka yi game da su a cikin Littafi Mai Tsarki. Bari tsuntsuwar nan tsattsewa ta sa ka daraja gidan Jehobah. Zai dace mu dogara ga begen da Jehobah yake ba mu don mu riƙa tashi kamar gaggafa. Ƙari ga haka, bari mu zo wurin Yesu don ya kāre mu kamar yadda kaza takan kāre ‘ya’yanta. A ƙarshe, bari tsuntsuwar nan zalɓe ta tuna mana cewa ya kamata mu riƙa kasancewa a faɗake da yake muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe.