Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA MALA’IKU?

Kana da Mala’ikan da Ke Kāre Ka?

Kana da Mala’ikan da Ke Kāre Ka?

Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa kowannenmu yana da mala’ikan da ke kāre shi ba. Gaskiya ne cewa Yesu ya taɓa ce: “Ku yi hankali kada ku rena wani a cikin waɗannan ƙanƙanana [mabiyan Yesu]; gama ina ce maku, cikin sama kullum mala’ikunsu suna duban fuskar Ubana wanda ke cikin sama.” (Matta 18:10) Amma hakan ba ya nufin cewa dukanmu muna da mala’ikan da ke kāre mu. A maimakon haka, Yesu yana nufin cewa mala’iku suna ƙaunar kowane ɗaya daga cikin mabiyansa. Saboda haka, Kiristoci na gaskiya ba sa yin abu da gangan kuma su yi tunanin cewa mala’ikun Allah za su kāre su.

Hakan yana nufin cewa mala’iku ba sa taimaka ma ’yan Adam ne? A’a. (Zabura 91:11) Wasu suna da tabbaci cewa Allah ya yi amfani da mala’ikunsa wajen taimaka musu. Kenneth wanda aka ambata a shafi na uku ma ya yi tunanin haka. Ko da yake ba mu san gaskiyar lamarin ba, amma wataƙila abin da ya faɗa gaskiya ne. Shaidun Jehobah suna yawan ganin abubuwan da ke tabbatar musu da cewa mala’iku suna taimaka musu a wa’azin da suke yi. Amma tun da yake ba ma ganin mala’iku, ba mu san yadda Allah yake amfani da su wajen taimaka wa kowane ɗayanmu ba. Duk da haka, ba laifi ba ne mu gode wa Allah don yadda yake taimaka mana.​—Kolosiyawa 3:15; Yaƙub 1:​17, 18.