Idan Muna da Halin Kirki, Shi Ke Nan Rayuwarmu Za Ta Yi Kyau?
Mutane sun daɗe suna ganin cewa idan mutum yana da halin kirki, zai more rayuwa. Alal misali, mutanen gabas suna daraja abin da wani malamin falsafa mai suna Confucius (551-479 kafin haihuwar Yesu) ya faɗa cewa: “Abin da ba ka so a yi maka, kar ka yi ma wani.” *
ZAƁIN MUTANE DA YAWA
A yau ma, mutane da yawa sun gaskata cewa idan suka zama da halin kirki, za su more rayuwa. Suna iya ƙoƙari su daraja mutane, kuma su zama da hali mai kyau. Ba sa rigima don sun san iyakarsu, kuma ba sa yin abin da zai sa zuciyarsu ta dame su. Wata mata mai suna Linh daga ƙasar Vietnam ta ce: “Na yi imani cewa idan ina yin gaskiya a koyaushe, zan sami albarka.”
Wasu suna ƙoƙarin su dinga yin abu mai kyau don abin da addininsu take koya musu ke nan. Wani mai suna Hsu-Yun da ke zama a ƙasar Taiwan ya ce: “An koya min cewa idan na yi abu mai kyau, zan ji daɗi bayan na mutu. Amma idan ban yi abu mai kyau yanzu ba, in na mutu zan sha azaba.”
WANE SAKAMAKO AKA SAMU?
A gaskiya idan muna wa mutane kirki, za mu amfana a hanyoyi da dama. Amma akwai mutane da yawa a yau da suka yi ƙoƙari su yi wa mutane alheri, sai dai a ƙarshe sun ga cewa wasu ba sa kyautata musu. Wata mai suna Shiu Ping daga Hong Kong ta ce: “Abin da ya faru a rayuwata ya koya min cewa ba a koyaushe yin alheri yake sa mutum ya sami albarka a rayuwa ba. Na yi iya ƙoƙari in kula da iyalina kuma in yi alheri, duk da haka na yi fama da matsaloli a aurena. A ƙarshe, maigidana ya yasar da mu.”
Mutane da yawa kuma sun lura cewa ba dukan masu addini suke da halin kirki ba. Wata mata mai suna Etsuko daga Japan ta ce: “Na shiga wani addini, har na zama mai ja-gorar ayyukan matasa. Amma na yi mamaki sosai da na ga irin lalata da gwagwarmayar neman matsayi da kuma sata kuɗi da suke yi.”
“Na yi iya ƙoƙari in kula da iyalina kuma in yi alheri, duk da haka na yi fama da matsaloli a aurena. A ƙarshe, maigidana ya yasar da mu.”—SHIU PING, DAGA HONG KONG
Wasu masu bin addini tsakani da Allah sun yi bakin ciki sosai da suka ga cewa munanan abubuwa suna faruwa da su, duk da alherin da suke yi. Abin da ya faru ke nan da wata mai suna Van daga ƙasar Vietnam. Ta ce: “Na yi ta sayan ’ya’yan itace da furanni da abinci ina kai in ajiye ma kakannina da suka mutu. Na yi zaton cewa hakan zai sa rayuwata ta yi albarka. Amma duk da ayyukan kirki da ibada da na yi shekaru da yawa ina yi, maigidana ya kamu da wata muguwar cuta. ’Yata ma da ta je karatu a ƙasar waje ta rasu tana ’yar shekara ashirin.”
Idan zama mai kirki ba zai iya ba mutum tabbaci cewa zai ji daɗin rayuwa ba, to mene ne zai yi hakan? Don mu sami amsar, muna bukatar shawara daga wurin wani mai hikima, wanda zai gaya mana abin da ya sa rayuwa ta zama yadda take a yau, da kuma abin da za mu yi don mu more rayuwa a nan gaba. A ina za mu samu irin wannan shawarar?
^ sakin layi na 2 Don ka sami ƙarin bayani a kan koyarwar Confucius, ka duba littafin nan Mankind’s Search for God babi na 7, sakin layi na 31-35, Shaidun Jehobah ne suka wallafa littafin kuma za ka iya samunsa a dandalinmu na www.isa4310.com.