ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA KARƁI KYAUTA MAFI DARAJA DAGA ALLAH?
Kyautar da Babu Kamarta
WATAƘILA wannan abin feƙe fensir mai kama da jirgin ruwa da ake miƙa wa Jordan bai da daraja a gare mu. Duk da haka, abin yana ɗaya daga cikin abubuwan da Jordan ya ɗauka da tamani sosai. Jordan ya ce: “Russell ne ya ba ni wannan kyautar sa’ad da nake yaro kuma shi dattijo ne da kuma abokin iyalinmu.” Bayan mutuwar Russell, sai Jordan ya ji cewa Russell ya taimaka wa kakansa da kuma iyayensa sosai sa’ad da suke cikin mawuyacin yanayi. Sai Jordan ya ce: “Yanzu da na san game da Russell, hakan ya sa wannan ƙaramar kyautar ta ƙara kasancewa da daraja a gare ni.”
Kamar yadda labarin Jordan ya nuna, akwai kyautar da wasu ba sa ɗaukan ta da daraja. Amma kyautar tana da tamani sosai ga wanda aka ba wa. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki yake kwatanta wata kyauta da babu kamarta, ya ce: ‘Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya, ya aiko da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.’
Wannan kyautar za ta iya sa mutum ya sami rai na har abada! Shin akwai wata kyauta da ta fi wannan? Ko da yake wasu ba sa daraja wannan kyautar, amma Kiristoci suna ɗaukan ta da “daraja” sosai. (Zabura 49:8; 1 Bitrus 1:
Manzo Bulus ya faɗi dalilin sa’ad da ya ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane.” (Romawa 5:12) Mutum na farko, wato Adamu ya yi zunubi ta wajen yi wa Allah rashin biyayya kuma hakan ya janyo masa wahala da kuma mutuwa. Ta wurin Adamu, dukan ‘yan Adam sun gāji mutuwa.
“Hakkin zunubi mutuwa ne; amma kyautar Allah rai na har abada ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.” (Romawa 6:23) Me ya sa Jehobah ya aiko da Ɗansa, Yesu Kristi zuwa duniya? Domin ya yi amfani da kamiltaccen ransa wajen ‘yantar da ‘yan Adam daga mutuwa. Ta wurin wannan hadayar da ake kira “fansa,” mutane za su iya samun rai na har abada idan suka gaskata da Yesu.
Bulus ya yi wannan furucin don albarkar da Jehobah zai yi wa bayinsa ta wurin Yesu. Ya ce: “Godiya ga Allah domin kyautarsa wadda ta fi gaban magana.” (2 Korintiyawa 9:15) Hakika, wannan fansar abin ban al’ajabi ce kuma ba za mu iya kwatanta ta ba. Amma me ya sa a cikin dukan abubuwan da Allah ya yi wa ‘yan Adam, wannan ce ta fi daraja sosai? Me ya sa kyauta ce da babu kamar ta? * Ta yaya za ka nuna godiya don kyautar? Muna so ka karanta talifofi na gaba don ka ga amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya bayar ga tambayoyin.
^ sakin layi na 4 Yesu ne kaɗai Allah ya halitta da kansa, shi ya sa ake ce da shi ‘makaɗaicin Ɗan’ Allah. Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan: “Me Ya Sa Ake Ce da Yesu Ɗan Allah?” a dandalin jw.org/ha. Ka duba ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > AN AMSA TAMBAYOYIN LITTAFI MAI TSARKI.
^ sakin layi na 8 Ba a tilasta wa Yesu ya “ba da ransa” ba. (1 Yohanna 3:16) Amma tun da wannan hadayar tana ɗaya daga cikin nufin Allah, wannan talifofin za su mai da hankali a kan Wanda ya yi tanadin fansar, wato Allah.