TARIHI
Na Yanke Shawarwari da Za Su Faranta Ran Jehobah
WATA rana sa’ad da nake zuwa aiki da safe, a 1984, na yi ta tunanin abin da na karanta a wani talifin Hasumiyar Tsaro da ba ta jima da fitowa ba. Talifin ya yi magana a kan yadda maƙwabtanmu suke ɗaukanmu. A lokacin, muna zama a unguwar masu kuɗi a birnin Caracas, a ƙasar Benezuwela. Na dubi gidajen da ke unguwarmu kuma na tambayi kaina: ‘Shin maƙwabtana suna mini kallon ma’aikacin banki da yake da kuɗi ne kawai? Ko suna mini kallon mai wa’azin Kalmar Allah da ke aiki a banki don ya taimaka wa iyalinsa?’ Na fahimci cewa maƙwabtana suna gani na a matsayin ma’aikacin banki da yake da kuɗi, kuma ban so hakan ba. Sai na ɗau mataki don in yi abin da ya fi hakan muhimmanci.
An haife ni a ranar 19 ga Mayu, 1940, a garin Amioûn, a ƙasar Labanan. Bayan wasu shekaru, iyalinmu ta ƙaura zuwa birnin Tripoli, kuma a wurin ne na girma. Muna ƙaunar juna da Jehobah kuma muna zaman lafiya a iyalinmu. Mu yara biyar ne, mata uku da maza biyu kuma ni ne ɗan auta. Iyayena ba su sa neman kuɗi a gaba ba. Mun fi mai da hankali ga yin nazarin Littafi Mai Tsarki da halartan taro da kuma yin wa’azi.
A lokacin, akwai shafaffun Kiristoci da yawa a ikilisiyarmu. Ɗaya daga cikinsu mai suna Michel Aboud ne yake gudanar da Taron Rukunin Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Ya koyi gaskiya a birnin New York, kuma bayan ya koma Labanan a 1921, ya soma wa’azi. Na tuna yadda ya taimaka da kuma daraja ’yan’uwa mata biyu da suka sauke karatu a makarantar Gilead kuma aka tura su Labanan, wato Anne da Gwen Beavor. Sun zama abokanmu na kud da kud. Bayan shekaru da yawa, na yi farin cikin sake haɗuwa da Anne a Amirka. Bayan wani lokaci, na sake haɗuwa da Gwen wadda ta auri Wilfred Gooch kuma a lokacin suna hidima a reshen ofishinmu da ke birnin Landan.
YIN WA’AZI A LABANAN
A lokacin da nake matashi, Shaidun Jehobah ba su da yawa a Labanan. Amma mukan yi wa’azi da ƙwazo. Mun yi hakan duk da hamayya daga wasu malaman addinai. Na tuna wasu abubuwan da suka faru da mu.
Wata rana ni da ’yar’uwata mai suna Sana muna yin wa’azi a wani gidan bene, sai wani fāda ya zo inda muke wa’azi. Mai yiwuwa wani ne ya kira shi. Sai fādan ya soma zagin ’yar’uwata. Ya yi fushi sosai kuma ya ture ta har ƙasa, sai ta ji rauni. Wani ya kira ’yan sanda, kuma da suka zo, sai suka sa a taimaka wa Sana. Sun kama fādan suka kai shi ofishinsu kuma a wurin suka gano cewa yana ɗauke da bindiga. Shugaban ’yan sandan ya tambaye shi cewa: “Kana koya wa mutane game da Allah ne ko kuma kana koya musu yadda za su yi mugunta?”
Wani abu kuma da na tuna shi ne lokacin da ikilisiyarmu ta yi hayar mota don mu je yin wa’azi a wani ƙauye mai nisa. Muna cikin jin daɗin wa’azin, sai wani fāda ya ji cewa muna wa’azi. Fādan ya je ya taro ’yan iska don su kawo mana hari. Sun zazzage mu, kuma suka jejjefe mu da duwatsu, har mahaifina ya ji rauni. Na tuna yadda fuskarsa take fid da jini bayan da aka jejjefe shi. Shi da mamata sun koma cikin mota kuma mu ma muka bi su. Amma ba zan taɓa mantawa da abin da mamata ta faɗa sa’ad da take wanke ma babana fuska ba. Ta ce: “Jehobah ka gafarta musu. Ba su san abin da suke yi ba.”
Akwai wani lokaci kuma da muka je mu gai da danginmu a wani gari. Mun haɗu da wani bishop a gidan kakana. Bishop ɗin ya san cewa iyayena Shaidun Jehobah ne. Ko da yake shekaruna shida ne kawai a lokacin, ya so ya kunyatar da ni. Sai ya tambaye ni, ya ce: “Kai, me ya sa ba ka yi baftisma ba?” Na ce masa ni yaro ne, kuma kafin in yi baftisma, ina bukatar in san Littafi Mai Tsarki da kyau kuma in kasance da bangaskiya. Bai ji daɗin amsar da na ba shi ba, sai ya gaya wa kakana cewa ba na daraja manya.
Mutane kaɗan ne kawai suka yi hamayya da mu. Yawancin mutanen Labanan suna da kirki da kuma karimci. Don haka, mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa.
MUN ƘAURA ZUWA WATA ƘASA
Sa’ad da nake makarantar firamare, wani ɗan’uwa daga Benezuwela ya ziyarci Labanan. Yakan halarci taro a ikilisiyarmu kuma ta haka ne ya san ’yar’uwata mai suna Wafa. Daga baya sun yi aure kuma suka koma zama a Benezuwela. Ta yi ta rubuta wa mahaifinmu wasiƙu, tana ƙarfafa shi ya ƙaurar da dukanmu zuwa Benezuwela. Ta yi hakan ne don yadda take kewar mu. A ƙarshe, mun amince kuma muka ƙaura!
Da muka isa Benezuwela a 1953, mun zauna a birnin Caracas, kusa da fādar shugaban ƙasa. Da yake a lokacin ni matashi ne, nakan ji daɗin kallon shugaban ƙasa yana wucewa da motarsa mai tsada. Amma bai yi wa iyayena sauƙi su saba da ƙasar da al’adar da abinci da kuma yanayin wurin ba. Sun soma sabawa da wurin ke nan sai wani mummunan abu ya faru.
WANI MUMMUNAN ABU YA FARU
Wata rana, mahaifina ya soma rashin lafiya. Hakan ya ba mu mamaki, domin shi mutum ne mai ƙoshin lafiya. Kafin ya soma wannan rashin lafiyar, ya jima bai yi rashin lafiya ba. An gano cewa yana da cutar kansa kuma aka yi masa tiyata. Amma ya mutu mako ɗaya bayan tiyatar.
Ba zan iya bayyana irin baƙin cikin da muka yi ba. Shekaruna 13 a lokacin kuma mun ji kamar namu ya ƙare. Mamata ta yi shekaru tana baƙin ciki. Amma mun ga cewa dole ne mu ci gaba da rayuwa, kuma Jehobah ya taimaka mana mu jimre. Na gama makarantar sakandare sa’ad da nake shekara 16. Kuma a lokacin, na so in taimaka ma iyalinmu sosai.
’Yar’uwata Sana ta auri wani ɗan’uwa mai suna Rubén Araujo, wanda ya kammala karatu a makarantar Gilead kuma ya koma zama a Benezuwela. Daga baya, sun ƙaura zuwa birnin New York a ƙasar Amirka. Iyalinmu sun ce in je makarantar jami’a, don haka, na je birnin New York don in zauna da ’yar’uwata da maigidanta yayin da nake makarantar. ’Yar’uwata da maigidanta sun taimake ni in kusaci Jehobah sosai. A lokacin, muna da ’yan’uwa da suka manyanta a ikilisiyarmu ta Sifanisanci a Brooklyn kuma su ma sun taimaka mini. Biyu daga cikinsu su ne Milton Henschel da Frederick Franz kuma a lokacin suna hidima a Bethel da ke Brooklyn.
Da na kusa gama shekara ta farko a jami’a, sai na soma tunanin abin da nake yi da rayuwata. Na karanta kuma na yi tunani a kan talifofin Hasumiyar Tsaro da suka yi magana a kan ’yan’uwa da suka yi ayyuka da yawa a ƙungiyar Jehobah. Na ga yadda majagaba da masu hidima a Bethel da suke ikilisiyarmu suke farin ciki, kuma na so in zama kamar su. Ba da daɗewa ba, na ga cewa ina bukatar in soma bauta ma Jehobah da dukan zuciyata. Sai na yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma na yi baftisma a ranar 30 ga Maris, 1957.
NA YANKE SHAWARWARI MASU MUHIMMANCI
Bayan na yi baftisma, sai na soma tunanin yin hidimar majagaba. Na so in zama majagaba, amma na ga cewa yin hakan zai yi mini wuya sosai. Ta yaya zan yi wannan hidimar tun da yake ina makarantar jami’a? Ni da iyalinmu mun yi ta aika wa juna wasiƙu game da matakin da nake so in ɗauka na barin jami’a, don in soma hidimar majagaba a Benezuwela.
Na koma birnin Caracas a watan Yuni na 1957. Amma na ga cewa iyalinmu suna fama da rashin kuɗi kuma za su bukaci taimako. Me zan yi don in taimaka musu? Na sami aiki a banki. Duk da haka, hidimar majagaba ba ta fita daga zuciyata ba. Dalilin da ya sa na koma gida ke nan. Na so in yi hidimar da kuma aiki a banki. Na yi shekaru da yawa ina aiki a banki da kuma hidimar majagaba. A lokacin, ayyuka sun yi mini yawa sosai, amma na yi farin ciki.
Na daɗa farin ciki sa’ad da na auri wata ’yar’uwa ’yar Jamus mai suna Sylvia. Sylvia tana ƙaunar Jehobah sosai. Tana zama a Benezuwela da iyayenta. Da shigewar lokaci, mun haifi yara biyu, namiji mai suna Michel (Mike), da kuma tamace mai suna Samira. Ƙari ga haka, na soma kula da mahaifiyata kuma na ɗauke ta ta soma zama da mu. Ko da yake na daina yin hidimar majagaba, na ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo. A duk lokacin da muka sami hutu, ni da matata mukan yi hidimar majagaba na ɗan lokaci.
NA SAKE ƊAUKAN WANI MATAKI MAI MUHIMMANCI
Labarin da na bayar a farkon wannan talifin, ya faru ne sa’ad da yarana suke makarantar firamare. Gaskiyar ita ce a lokacin, muna jin daɗin rayuwarmu kuma ana daraja ni a wurin aikina. Duk da haka, na fi so mutane su ɗauke ni a matsayin bawan Jehobah. Na yi ta tunanin abin da zan yi don mutane su san cewa abin da ya fi muhimmanci a gare ni shi ne bauta wa Jehobah. Ni da matata mun lissafta adadin kuɗin da muke samu. Idan na yi murabus daga bankin, za a biya ni kuɗi mai yawa. Da yake mun sauƙaƙa rayuwarmu kuma ba a bin mu bashi, kuɗin zai ishe mu na dogon lokaci.
Ɗaukan wannan matakin bai yi mini sauƙi ba, amma mahaifiyata da matata sun goyi baya na. Na ga cewa zai yiwu in sake yin hidimar majagaba. Hakan ya sa ni murna ba kaɗan ba. Ina shirye in soma hidimar majagaba, sai muka sami wani labari mai ban mamaki.
WANI ABIN BAN MAMAKI YA FARU!
Wata rana likita ya gaya mana cewa Sylvia ta yi juna biyu. Hakan ya ba mu mamaki sosai! Ko da yake abin farin ciki ne, na yi tunanin ko zai hana ni yin hidimar majagaba. Mun yi canje-canje a rayuwarmu kuma muka yi shiri domin jaririn da za ta
haifa. Amma na ci gaba da yin tunanin yadda zan yi hidimar majagaba.Bayan mun tattauna, sai muka tsai da shawara cewa zan yi hidimar majagabar. An haifi ɗanmu Gabriel a watan Afrilu 1985. Na yi murabus daga aikin banki kuma na sake soma yin hidimar majagaba a watan Yuni 1985. Daga baya, na zama memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a Benezuwela. Amma ofishin ba ya birnin Caracas, don haka, nakan yi tafiyar wajen kilomita 80 zuwa wurin aiki sau biyu ko uku a mako.
MUN SAKE ƘAURA
Da yake ofishin yana garin La Victoria, ni da iyalina mun yanke shawarar ƙaura zuwa garin don mu zauna kusa da ofishin. Hakan babban canji ne. Iyalina sun burge ni kuma ina musu godiya don yadda suka goyi bayana. ’Yar’uwata mai suna Baha ta yarda cewa za ta kula da mahaifiyarmu. Ɗana Mike ya riga ya yi aure a lokacin, amma Samira da Gabriel suna zama tare da mu har ila. Don haka, in sun ƙaura za su yi kewar abokansu da ke birnin Caracas. Matata Sylvia ta saba da zama a birnin Caracas, don haka, zama a ƙaramin gari bai yi mata sauƙi ba. Kuma dukanmu mun koma zama a ƙaramin gida maimakon babba. Hakika ba ƙaramin canji muka yi da muka bar Caracas kuma muka koma La Victoria ba.
Amma abubuwa sun sake canjawa. Gabriel ya yi aure, Samira kuma ta koma zama ita kaɗai. A shekara ta 2007, an gayyace ni da matata mu soma zama a cikin Bethel kuma inda muke zama ke nan har wa yau. Mike, ɗanmu na fari dattijo ne kuma yana yin hidimar majagaba tare da matarsa Monica. Gabriel ma dattijo ne kuma shi da matarsa Ambra suna zama a Italiya. Samira tana yin hidimar majagaba kuma tana taimaka wa ofishinmu daga gida.
BA NA YIN DA-NA-SANI
Ko da yake na yi canje-canje da yawa a rayuwata, ba na yin da-na-sani. Zan sake ɗaukan matakan da na ɗauka in na sami dama. Ina godiya ga Jehobah don dukan ayyukan da ya ba ni in yi a ƙungiyarsa. Da shigewar lokaci, na ga muhimmancin kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah. Ko da wane irin mataki ne muke so mu ɗauka, kome girmansa ko ƙanƙancinsa, Jehobah zai ba mu ‘salama irin wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam.’ (Filib. 4:6, 7) Ni da matata Sylvia muna jin daɗin hidimar da muke yi a Bethel kuma mun san cewa Jehobah yana mana albarka domin shi muka saka farko a rayuwarmu.