ꞌYanꞌuwa Sun Nuna Musu Kauna Ta Gaskiya
YOMARA da ꞌyanꞌuwanta Marcelo da Hiver suna zama a wani ƙauye da ke ƙasar Guatemala. Sai Yomara ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, daga baya ꞌyanꞌuwanta ma sun soma nazarin. Amma akwai wata matsala. Dukansu makafi ne kuma ba su iya karanta littafin makafi ba. Don haka, wanda yake nazari da su ne yake karanta musu littafin da suke nazari da shi da kuma ayoyin Littafi Mai Tsarki.
Wata matsala kuma da suka fuskanta ita ce zuwa taro. Ba za su iya zuwa Majamiꞌar Mulki da kansu ba wanda yake da nisan minti 40. Amma ꞌyanꞌuwa sun shirya yadda za su riƙa kai dukansu taron. Da waɗannan ɗaliban suka soma yin ayyuka a taron tsakiyar mako, ꞌyanꞌuwan suna taimaka musu su haddace ayyukan da aka ba su.
A watan Mayu, 2019, an soma yin taron ikilisiya a ƙauyensu. A lokacin, wasu maꞌaurata da majagaba ne sun ƙaura zuwa ƙauyen. Maꞌauratan ba su san yadda ake rubuta da karanta littafin makafi ba, amma suna so su koya ma waɗannan ɗaliban su san yadda za su yi hakan. Don haka, sun je sun nemo littattafai na makafi don su san yadda za su koya ma wasu su yi amfani da shi.
A cikin ꞌyan watanni, waɗannan ɗalibai uku sun iya karanta littafin makafi kuma hakan ya taimaka musu su sami ci gaba a ibadarsu ga Jehobah. a Yanzu haka, ꞌyarꞌuwa Yomara da ɗanꞌuwa Marcelo da Hiver suna hidimar majagaba. Marcelo bawa ne mai hidima. Dukan su suna yin hidimarsu da ƙwazo koyaushe. Kuma hakan ya sa sauran ꞌyanꞌuwa suka soma yin hidimarsu da ƙwazo.
Ɗalibai ukun nan suna godiya sosai don taimakon da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya suka yi musu. Yomara ta ce: “Tun daga ranar da muka fara haɗuwa da Shaidun Jehobah, sun nuna mana ƙauna ta gaskiya da Kirista ya kamata ya kasance da ita.” Marcelo ya ce: “Muna da abokan kirki a ikilisiyarmu kuma muna da ꞌyanꞌuwa maza da mata a duk faɗin duniya.” Yomara da ꞌyanꞌuwanta suna marmarin ganin lokacin da duniya za ta zama aljanna.—Zab. 37:10, 11; Isha. 35:5.
a Akwai wata ƙasida mai jigo Learn to Read Braille da aka tsara don ya taimaka wa makafi ko kuma waɗanda ba sa gani sosai su koyi rubutu da karanta yaren makafi.