Yaya Kake Tsai da Shawarwari?
‘Ku ci gaba da fahimtar ko mene ne nufin Ubangiji.’—AFIS. 5:17.
WAƘOƘI: 69, 57
1. Waɗanne dokoki ne Jehobah ya ba mu a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma ta yaya bin su yake amfanar mu?
JEHOBAH ya ba mu umurni da dama a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ya haramta zina da bautar gumaka da sata da kuma maye. (1 Kor. 6:9, 10) Ƙari ga haka, Yesu Kristi Ɗan Allah ya ba wa mabiyansa wani gagarumin aiki mai ƙayatarwa, ya ce: “Ku tafi, . . . ku almajirtar da dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku: ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.” (Mat. 28:19, 20) Bin waɗannan umurni da dokoki yana kāre mu kuma yana ya sa mu kula da kanmu da kyau, yana kāre lafiyarmu kuma ya sa mu da iyalinmu farin ciki sosai. Mafi muhimmanci, bin dokokin Jehobah wanda ya haɗa da yin wa’azin bishara yana sa Jehobah ya albarkace mu kuma ya amince da mu.
2, 3. (a) Me ya sa Littafi Mai Tsarki bai ba mu dokoki game da kowane yanayi a rayuwa ba? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
2 Amma, akwai abubuwa da yawa da Littafi Mai Tsarki bai ba da umurni a kansu ba. Alal misali, Littafi Mai Tsarki bai ba da takamammun dokoki game da irin tufafin da ya kamata Kiristoci su riƙa sakawa ba. Hakan ya nuna cewa Jehobah mai
hikima ne. Ta yaya? Irin tufafin da mutane suke sakawa da kuma al’adu sun bambanta a wurare dabam-dabam a faɗin duniya kuma hakan yana canjawa da shigewar lokaci. Da a ce Littafi Mai Tsarki ya ambaci jerin tufafin da Kiristoci za su riƙa sakawa, da an daina yayin waɗannan tufafi a yau. Hakazalika, Kalmar Allah ba ta ba da dokoki game da aiki da irin kiwon lafiya da kuma shaƙatawa da ya kamata Kirista ya yi ba. Mutane da kuma magidanta suna da ’yancin yanke shawarwari a kan waɗannan batutuwan da kansu.3 Shin hakan yana nufin cewa tsai da shawarwari a kan waɗannan batutuwan ba shi da muhimmanci a gaban Jehobah ne, musamman ma idan hakan zai shafi rayuwarmu sosai? Shin Ubanmu na sama zai amince da duk wata shawara da muka tsai da muddin ba ta saɓa wa dokar Littafi Mai Tsarki ba? Idan Littafi Mai Tsarki bai ba da doka a kan wani batu ba, ta yaya za mu san abin da ya kamata mu yi da zai faranta wa Jehobah rai?
SHAWARWARINKA SUNA SHAFANKA DA KUMA WASU
4, 5. Ta yaya shawarwarinmu za su iya shafan mu da kuma ’yan’uwanmu?
4 Wasu suna ganin cewa za mu iya yin abin da muka ga dama. Amma idan muna so mu tsai da shawarwarin da za su faranta wa Jehobah rai, wajibi ne mu yi la’akari da dokokinsa da kuma ƙa’idodinsa da ke cikin Kalmarsa, kuma mu yanke shawarwarin da suka jitu da su. Alal misali, wajibi ne mu bi dokar da Allah ya ba da game da jini. (Far. 9:4; A. M. 15:28, 29) Addu’a za ta taimaka mana mu yanke shawarwarin da suka jitu da dokoki da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.
5 Shawarwari masu muhimmanci da muke yi sukan shafi dangantakarmu da Jehobah. Duk wata shawarar da muka tsai da za ta iya kyautata ko kuma ɓata dangantakarmu da Jehobah. Ƙari ga haka, idan muka yanke shawara marar kyau, hakan zai iya damun ’yan’uwanmu ko ya su sanyin gwiwa a ibadarsu ko kuma ya haddasa rashin haɗin kai a cikin ikilisiya. Hakika, shawarwarin da muke yi za su iya shafanmu da kuma wasu.—Karanta Romawa 14:19; Galatiyawa 6:7.
6. Mene ne ya kamata mu yi la’akari da shi kafin mu yanke shawara?
6 Shin mene ne ya kamata mu yi idan muna so mu yanke shawara a kan wani batu da Littafi Mai Tsarki bai ba da takamaiman doka a kai ba? Ya kamata mu yi bincike da kyau don mu sami cikakken bayani game da batun kafin mu yanke shawara. Yin hakan zai taimaka mana mu yanke shawara mai kyau, wato shawarar da za ta faranta wa Jehobah rai. Ƙari ga haka, Jehobah zai albarkaci irin wannan shawara.—Karanta Zabura 37:5.
KA FAHIMCI NUFIN JEHOBAH
7. Idan Littafi Mai Tsarki bai ambaci takamaiman doka game da wani batu ba, ta yaya za mu san abin da Jehobah yake son mu yi?
7 Za ka iya yin tunani, ‘Ta yaya za mu iya sanin abin da Jehobah ya amince da shi idan Kalmarsa ba ta ba da wani takamaiman doka a kan batun ba?’ Littafin Afisawa 5:17 ta ce: ‘Ku ci gaba da fahimtar ko mene ne nufin Ubangiji.’ Idan Littafi Mai Tsarki bai yi magana a kan batun ba, ta yaya za mu san nufin Allah? Ta wajen yin addu’a da kuma amincewa da ja-gorar da yake mana ta wurin ruhu mai tsarki.
8. Ta yaya Yesu ya fahimci nufin Jehobah? Ka ba da misali.
8 Ka yi la’akari da yadda Yesu ya fahimci nufin Jehobah. Sau biyu, Yesu ya yi addu’a ga Jehobah kuma ya yi mu’ujiza don ciyar da jama’a masu yawa. (Mat. 14:17-20; 15:34-37) Amma ya ƙi ya mai da duwatsu su zama gurasa sa’ad da Iblis ya jarabce shi a daji. (Karanta Matta 4:2-4.) Da yake Yesu ya san ra’ayin Ubansa, ya san cewa bai kamata ya mai da duwatsu su zama gurasa a wannan yanayin ba. Ya san cewa ba nufin Allah ba ne ya yi mu’ujiza don ya amfani kansa. Matakin da ya ɗauka ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah ya yi masa ja-gora kuma ya kula da shi.
9, 10. Mene ne zai taimaka mana mu yanke shawarwarin da suka dace? Ka ba da misali.
9 Idan muna so mu yanke shawarwarin da suka dace, wajibi ne mu dogara ga Jehobah ya ja-gorance mu. Muna bukata mu bi wannan shawarar: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka. Kada ka ga kanka mai-hikima ne: Ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da mugunta.” (Mis. 3:5-7) Sanin ra’ayin Jehobah ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu san ko mene ne nufin Jehobah a wani yanayi. Idan muka ci gaba da koyan abubuwa game da Jehobah, hakan zai yi mana sauƙi mu yanke shawarwarin da za su faranta wa Jehobah rai. Ta hakan, za mu riƙa son bin ja-gorarsa a kowane lokaci.—Ezek. 11:19.
10 Alal misali, a ce wata mata tana sayayya kuma ta ga wasu takalma da take so, amma suna da tsada sosai. Sai ta tambayi kanta, ‘Yaya mijina zai ji idan na kashe kuɗi mai yawa haka?’ Ta riga ta san amsar, duk da cewa mijinta ba ya wurin. Me ya sa? Don ta san yadda mijinta zai so su yi amfani da ɗan kuɗin da suke da shi. Saboda haka, ta fahimci cewa ba zai so ta sayi wannan takalma mai tsada ba. Hakazalika, yayin da muke ƙara sanin ra’ayin Jehobah da kuma al’amuransa, hakan zai taimaka mana mu fahimci abubuwan da zai so mu yi a yanayi dabam-dabam.
TA YAYA ZA KA IYA SANIN RA’AYIN JEHOBAH?
11. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu sa’ad da muke karanta ko kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki? (Ka duba akwatin nan “ Sa’ad da Kake Nazarin Kalmar Allah, Ka Tambayi Kanka.”)
11 Muna bukatar mu ɗauki yin nazarin Littafi Mai Tsarki da muhimmanci sosai idan muna so mu san ra’ayin Jehobah. Sa’ad da muke karanta ko kuma yin nazarin Kalmar Allah, za mu iya tambayar kanmu, ‘Mene ne wannan bayani yake koya min game da Jehobah?’ Zai dace mu kasance da irin halin Dauda, marubucin Zabura da ya ce: “Ya Ubangiji, ka nuna mini tafarkunka; Ka koya mani hanyoyinka. Ka bishe ni cikin gaskiyarka, ka koya mani; Gama kai ne Allah na cetona; a gareka na ke sauraro dukan yini.” (Zab. 25:4, 5) Yayin da kake bimbini a kan wani nassi, za ka iya yin tunani a kan waɗannan tambayoyin: ‘Ta yaya zan yi amfani da wannan darasin a rayuwata? A ina ne zan iya amfani da shi? A gida? A wurin aiki? A makaranta? Sa’ad da na fita wa’azi?’ Idan muka san inda ya kamata mu yi amfani da darasin da muka koya, hakan zai sa mu fahimci yadda za mu iya yin amfani da shi.
12. Ta yaya littattafanmu da abubuwan da muke koya a taro za su taimaka mana mu san ra’ayin Jehobah a kan batutuwa dabam-dabam?
12 Wata hanya da za mu iya ƙara sanin ra’ayin Jehobah ita ce ta mai da hankali sosai ga ja-gorar da Allah yake tanadar mana ta ƙungiyarsa. Alal misali, an wallafa littattafan nan, Watch Tower Publications Index da kuma Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah don su taimaka mana mu san ra’ayin Jehobah sa’ad da muke so mu yanke shawara a yanayi dabam-dabam. Ƙari ga haka, za mu amfana sosai idan muka saurari abubuwan da ake koyarwa a taro kuma
muka saka hannu a shirye-shiryen taron. Yin bimbini a kan abubuwan da muke koya zai taimaka mana mu ƙara sanin ra’ayin Jehobah kuma mu yi tunani kamar yadda Jehobah yake tunani. Ta wajen yin amfani da abubuwan da Jehobah yake tanadarwa don ƙarfafa dangantakarmu da shi, za mu ƙara sanin al’amuransa. A sakamako, za mu iya yanke shawarwarin da Jehobah zai amince da su.KA YANKE SHAWARWARI DA SUKA JITU DA RA’AYIN JEHOBAH
13. Ka ba da misalin da ya nuna yadda za mu iya yanke shawara mai kyau sa’ad da muka yi la’akari da ra’ayin Jehobah.
13 Ka yi la’akari da wani misalin da ke nuna yadda ra’ayin Jehobah zai taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. Wataƙila za mu so mu soma hidimar majagaba. Don mu cim ma wannan maƙasudin, za mu soma rage yin wasu abubuwa. Duk da haka, za mu iya soma damuwa cewa idan ba mu da wasu abubuwan jin daɗin rayuwa, ba za mu yi farin ciki ba. Hakika, babu wata doka a cikin Littafi Mai Tsarki da ta ce mu yi hidimar majagaba. Za mu iya ci gaba da bauta wa Jehobah a matsayinmu na amintattun bayin Allah. Amma, Yesu ya tabbatar mana cewa waɗanda suka yi sadaukarwa saboda Mulkin Allah za mu sami albarka sosai. (Karanta Luka 18:29, 30.) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa idan muka ba da “hadayu na yardan rai” don mu yabe Jehobah kuma muka yi iya ƙoƙarinmu don mu bauta masa, hakan yana faranta masa rai. (Zab. 119:108; 2 Kor. 9:7) Idan muka yi bimbini a kan waɗannan ayoyin Littafi Mai Tsarki kuma muka yi addu’a Jehobah ya yi mana ja-gora, za mu fahimci nufin Jehobah. Yin hakan zai sa mu yanke shawara mai kyau kuma Jehobah zai yi mana albarka.
14. Ta yaya za ka sani ko Jehobah ya amince da wani irin kayan da kake sakawa?
14 Ka yi la’akari da wani misali: A ce kana son wata tufa amma idan ka saka tufar, za ta iya damun lamirin ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Duk da haka, ka san cewa babu wani takamaiman dokar Littafi Mai Tsarki da ta ce kada a saka wannan tufar. Shin mene ne ra’ayin Jehobah game da wannan batun? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mata kuma su riƙa sa tufafin da ya dace da su saboda kunya da kamunkai, ba adon kitso, ko kayan zinariya, ko lu’ulu’u, ko tufafi masu tsada ba, sai dai su yi aiki nagari, yadda ya dace da mata masu bayyana shaidar ibada tasu.” 1 Tim. 2:9, 10, Littafi Mai Tsarki) Wannan ƙa’idar ta shafi mazajen Kirista har ila. Muna so mu riƙa saka kayan da muke so, amma a matsayinmu na masu bauta wa Jehobah, ya kamata mu riƙa mai da hankali don kada kayan da muke sakawa ya sa mutane tuntuɓe. Tawali’u da ƙauna za su sa mu yi la’akari da ra’ayin ’yan’uwanmu masu bi don kada mu sa su damuwa ko kuma mu ɓata musu rai. (1 Kor. 10:23, 24; Filib. 3:17) Idan muka yi tunani a kan abin da nassi ya ce, za mu fahimci ra’ayin Jehobah a wannan al’amari kuma hakan zai taimaka mana mu yanke shawarar da za ta faranta masa rai.
(15, 16. (a) Yaya Jehobah yake ji idan muka ci gaba da yin tunanin lalata? (b) Ta yaya za mu san abin da zai faranta wa Jehobah rai sa’ad da muke so mu shaƙata? (c) Yaya ya kamata mu yanke shawarwari masu muhimmanci?
15 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ba ya farin ciki idan mutane suka bi mugun tafarki kuma idan ‘kowacce shawara ta tunanin zuciyarsu mugunta ce kaɗai kullayaumi.’ (Karanta Farawa 6:5, 6.) Ta hakan, za mu san cewa yin tunanin lalata ba shi da kyau don zai iya sa mu yin zunubi mai tsanani, wato abin da Littafi Mai Tsarki ya haramta. Ta ja-gorar ruhu mai tsarki, Yaƙub ya ce, ‘Hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce da fari, bayan wannan mai-salama ce, mai-sauƙin hali, . . . tana cike da jinƙai da kyawawan ’ya’ya, marar-kokanto, marar-riya.’ (Yaƙ. 3:17) Ya kamata sanin hakan ya sa mu guji duk wata irin shaƙatawa da za ta iya sa mu yin tunanin da bai dace ba. Kiristoci masu basira ba sa bukata su yi tambaya ko ya dace su karanta wani littafi ko su kalli wani fim ko kuma su yi wani wasan da ke ɗaukaka abin da Jehobah ya haramta. Sun fahimci ra’ayin Jehobah game da waɗannan batutuwan ta wurin Kalmarsa.
16 Sa’ad da muke so mu yanke shawara a kan wani abu, muna da zaɓi dabam-dabam da za mu iya yi da za su faranta wa Jehobah rai. Amma idan ya zo ga shawarwari masu muhimmanci, zai dace mu nemi shawarar dattawa ko kuma wasu Kiristoci da suka manyanta. (Tit. 2:3-5; Yaƙ. 5:13-15) Hakika, ba zai dace mu ce wa wasu su yanke mana shawara ba. Wajibi ne Kiristoci su horar da hankalinsu da Littafi Mai Tsarki kuma su yi amfani da shi wajen tsai da shawarwari. (Ibran. 5:14) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama kowane mutum za ya ɗauki kayan kansa.”—Gal. 6:5.
17. Ta yaya muke amfana sa’ad da muka yanke shawarwarin da suke faranta wa Jehobah rai?
17 Idan muka saba da yanke shawarwarin da suka jitu da ra’ayin Jehobah, hakan zai sa mu kusace shi. (Yaƙ. 4:8) Zai amince da mu kuma zai yi mana albarka. A sakamako, za mu ƙara ba da gaskiya ga Ubanmu na sama. Saboda haka, bari mu riƙa bin dokoki da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don hakan zai sa mu fahimci ra’ayin Jehobah a yanayi dabam-dabam. Hakika ba za mu daina koyan sababbin abubuwa game da Jehobah ba. (Ayu. 26:14) Amma idan muka yi ƙwazo yayin da muke ƙoƙarin sanin ra’ayinsa game da abubuwa, za mu kasance da hikima da ilimi da kuma basirar da za su taimaka mana mu yanke shawarwarin da suka dace. (Mis. 2:1-5) Ɗan Adam ajizi yakan canja ra’ayinsa da shirye-shiryensa, amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shawarar Ubangiji ta tabbata har abada, tunanin zuciyarsa kuma har tsararaki duka,” wato har abada. (Zab. 33:11) A bayyane yake cewa za mu iya yanke shawarwari masu kyau idan ra’ayinmu da halayenmu sun jitu da na Allahnmu, Jehobah, wanda ya fi kowa hikima.