Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana Barin Littafi Mai Tsarki Ya Kyautata Halayenka Har Ila?

Kana Barin Littafi Mai Tsarki Ya Kyautata Halayenka Har Ila?

“Amma ku bar halinku ya sake ta wurin sabunta hankalinku.”—ROM. 12:2, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 61, 52

1-3. (a) Waɗanne halaye ne za su iya zama da wuyar canjawa bayan mun yi baftisma? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi game da halayenmu? (Ka duba hotunan da ke shafin nan.)

BAYAN Kevin [1] ya koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, burinsa shi ne ya ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah. Shekaru da dama da suka shige, ya yi caca, ya yi shaye-shaye kuma hakan ya haɗa da taba da ƙwayoyi. Kevin ya daina waɗannan abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya haramta don ya sami amincewar Jehobah. Ya yi nasara don ya dogara ga Jehobah da kuma Kalmarsa da ke da ikon sa mutum ya canja halayensa.—Ibran. 4:12.

2 Shin Kevin ya daina canja halayensa bayan ya yi baftisma ne? A’a, yana bukatar ya ci gaba da ƙoƙartawa don ya kyautata halayensa kuma ya kafa misali mai kyau a matsayinsa na Kirista. (Afis. 4:31, 32) Alal misali, shi mai saurin fushi ne, kuma kyautata halinsa a wannan fannin bai kasance masa da sauƙi ba. Kevin ya ce, “Daina saurin fushi ya yi min wuya fiye da barin halayen banza!” Amma Kevin ya yi nasara ta wajen yin addu’a da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki sosai.

3 Kamar Kevin, da yawa daga cikin mu mun yi wasu canje-canje kafin mu yi baftisma don mu yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Amma bayan baftisma, mun ga cewa muna bukatar mu ci gaba da yin wasu canje-canje don mu yi koyi da Allah da kuma Yesu. (Afis. 5:1, 2; 1 Bit. 2:21) Alal misali, wataƙila mun lura cewa mu masu kūshe mutane ne ko masu fargaba ko kuma masu gulma, da dai sauran su. Shin kyautata halayenmu a waɗannan fannoni ya yi mana wuya fiye da yadda muka zata ne? Idan hakan ne, kana iya yin tunani cewa: ‘Me ya sa daina waɗannan halayen yake da wuya? Mene ne zan yi don Littafi Mai Tsarki ya ci gaba da taimaka min in canja halayena?’

ZA KA IYA FARANTA WA JEHOBAH RAI

4. Me ya sa ba a kowane lokaci ba ne za mu iya faranta wa Jehobah rai?

4 Muna ƙaunar Jehobah sosai, hakan ya sa muna so mu faranta masa rai da dukan zuciyarmu. Amma ba za mu iya faranta wa Jehobah rai a kowane lokaci ba saboda mu ajizai ne. A wani lokaci muna ji kamar manzo Bulus da ya ce: ‘Niyyar yin abin da ke daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu.’—Rom. 7:18, LMT; Yaƙ. 3:2.

5. Waɗanne canje-canje ne muka yi kafin mu yi baftisma, amma waɗanne kasawa ne za mu ci gaba da fama da su?

5 Kafin mu soma bauta wa Jehobah, mun daina yin abubuwan da Jehobah ba ya so. (1 Kor. 6:9, 10) Duk da haka, mu ajizai ne. (Kol. 3:9, 10) Saboda haka, bai kamata mu ɗauka cewa bayan mun yi baftisma, ko kuma bayan mun yi shekaru da yawa muna bauta wa Jehobah, ba za mu riƙa yin kurakure ba ko kuma ba za mu kasance da halayen da ba su dace ba. Wataƙila, za mu yi shekaru da yawa kafin mu shawo kan wasu halaye marasa kyau.

6, 7. (a) Mene ne ya sa muka zama abokan Jehobah duk da cewa mu ajizai ne? (b) Me ya sa bai kamata mu yi jinkirin yin addu’a Jehobah ya gafarta mana zunubanmu ba?

6 Bai kamata mu bar ajizancinmu ya hana mu bauta wa Jehobah ko kuma ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi ba. Alal misali: Sa’ad da Jehobah ya amince da mu mu zama abokansa, ya san cewa za mu yi kuskure a wasu lokatai. (Yoh. 6:44) Tun da Allah ya san kasawarmu da kuma abin da ke cikin zuciyarmu, hakan yana nufin cewa ya san halayen da za su zama mana ƙashi a wuya. Ƙari ga haka, ya san cewa za mu riƙa yin kurakurai a wasu lokatai. Duk da haka, Jehobah yana so mu zama abokansa.

7 Jehobah yana ƙaunarmu sosai, shi ya sa ya ba da hadayar Ɗansa a madadinmu. (Yoh. 3:16) Saboda haka, a duk lokacin da muka yi zunubi, za mu iya roƙan gafara daga wurin Jehobah, kuma mun tabbata cewa ba zai yi watsi da mu ba. Za mu ci gaba da zama abokansa. (Rom. 7:24, 25; 1 Yoh. 2:1, 2) Shin ya kamata mu yi jinkirin neman gafara daga wurin Jehobah saboda muna ganin cewa mu masu zunubi ne? A’a! Yin hakan yana kamar ƙin wanke hannayenmu sa’ad da suka yi datti. Ƙari ga haka, Yesu ya mutu a madadin waɗanda suka yi zunubi kuma suka tuba. Saboda wannan hadayar, za mu iya more dangantaka ta kud da kud da Jehobah duk da cewa mu ajizai ne.—Karanta 1 Timotawus 1:15.

8. Me ya sa bai kamata mu yi watsi da kasawarmu ba?

8 Hakika, bai kamata mu riƙa yin watsi da kasawarmu ba. Jehobah ya riga ya gaya mana abin da yake so mu yi. Saboda haka, idan muna so mu ƙulla dangantaka da Jehobah, muna bukata mu yi koyi da shi da kuma Kristi. (Zab. 15:1-5) Hakan ya ƙunshi yin iya ƙoƙarinmu don mu guji halayen da ba su dace ba. Ko da ba mu daɗe da yin baftisma ba ko kuma mun yi shekaru da yawa muna bauta wa Jehobah, wajibi ne mu ci gaba da gyara halayenmu.—2 Kor. 13:11.

9. Ta yaya muka san cewa za mu iya ci gaba da kasancewa da sabon hali?

9 Muna bukatar mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu gyara halayenmu kuma mu yafa “sabon mutum” ko kuma sabon hali. Bulus ya gaya wa ’yan’uwa masu bi cewa: “Kun tuɓe tsohon mutum tare da ayyukansa, kun yafa kuma sabon mutum, wanda ake sabunta shi zuwa ilimi bisa ga surar mahaliccinsa.” (Kol. 3:9, 10) Furucin nan, “wanda ake sabunta shi” yana nufin cewa za mu ci gaba da sabunta halayenmu. Hakan yana da ban ƙarfafa domin ya nuna mana cewa ko da mun yi shekaru da yawa muna bauta wa Jehobah, muna bukatar mu ci gaba da kyautata halayenmu a matsayinmu na Kiristoci. Hakika, za mu ci gaba da barin Littafi Mai Tsarki ya gyara halayenmu.

ME YA SA YIN GYARA YAKE DA WUYA?

10. Mene ne ya kamata mu yi don mu ci gaba da gyara halayenmu da taimakon Littafi Mai Tsarki, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi?

10 Wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ƙyale Kalmar Allah ta ci gaba da gyara halayenmu. Amma me ya sa muke bukatar mu ƙoƙarta sosai? Idan Jehobah yana albarkar mu don ƙoƙarin da muke yi, bai kamata yin gyara ya kasance mana da wuya ba. Amma me ya sa Jehobah bai sa yin nagarta ya kasance mana da sauƙi ba?

11-13. Me ya sa Jehobah yake bukata mu yi aiki tuƙuru don mu shawo kan kasawarmu?

11 Idan muka yi la’akari da duniya da sararin sama, za mu ga cewa Jehobah yana da iko sosai. Alal misali, ya halicci rana kuma tana ba da haske da zafi sosai. Amma haske da zafin rana da ke isa duniya kaɗan ne kawai kuma hakan ne muke bukata don mu rayu. (Zab. 74:16; Isha. 40:26) Hakazalika, Jehobah yana farin cikin ba wa bayinsa ƙarfin da suke bukata. (Isha. 40:29) Hakika, Allah zai iya ba mu ƙarfi don mu shawo kan kasawarmu ba tare da mun sha wahala ba. Amma me ya sa bai yi hakan ba?

12 Jehobah ya ba mu ’yancin yin abin da muke so. Sa’ad da muka zaɓa mu yi nufin Jehobah da son rai kuma muka yi iya ƙoƙarinmu don mu yi abin da yake so, muna nuna masa cewa muna ƙaunarsa sosai kuma muna so mu faranta masa rai. Ƙari ga haka, muna nuna cewa muna goyon bayan sarautarsa. Shaiɗan ya ce Jehobah bai cancanci ya yi sarauta ba. Amma sa’ad da muka yi wa Jehobah biyayya, hakan na nuna cewa muna goyon bayan sarautarsa, kuma muna da tabbaci cewa Ubanmu mai ƙauna yana farin ciki saboda ƙoƙarin da muke yi don mu yi masa biyayya. (Ayu. 2:3-5; Mis. 27:11) Idan Jehobah bai bar mu mu yi ƙoƙari don mu guji halaye marasa kyau kuma mu faranta masa rai ba, amincinmu ga Jehobah da kuma sarautarsa ba zai kasance da ma’ana ba.

13 Saboda haka, Jehobah ya gaya mana cewa mu yi “ƙoƙari” sosai don mu koyi halaye masu kyau. (Karanta 2 Bitrus 1:5-7; Kol. 3:12) Ya bukace mu mu yi ƙoƙari sosai don mu guji tunanin banza da kuma sha’awoyin da ba su dace ba. (Rom. 8:5; 12:9) A duk lokacin da muka yi iya ƙoƙarinmu don mu gyara halayenmu kuma muka yi nasara, muna farin ciki don mun san cewa Littafi Mai Tsarki yana kyautata halayenmu.

KA BAR KALMAR ALLAH TA CI GABA DA KYAUTATA HALAYENKA

14, 15. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu kasance da halayen da Jehobah yake so? (Ka duba akwatin nan “ Sun Kyautata Halayensu da Taimakon Littafi Mai Tsarki da Addu’a.”)

14 Mene ne za mu iya yi don mu koyi halaye masu kyau kuma mu faranta wa Jehobah rai? Maimakon mu dogara ga kanmu, muna bukatar mu bi ja-gorar da Jehobah ya bayar. Littafin Romawa 12:2 ta ce: “Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sake ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.” (LMT) Ta wurin Kalmarsa da kuma ruhu mai tsarki, Jehobah yana taimaka mana mu san nufinsa kuma mu bi umurninsa. Ƙari ga haka, yana taimaka mana mu canja halayenmu don su jitu da ƙa’idodinsa. Muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu wajen karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana, mu yi bimbini a kan Nassosi kuma mu riƙa addu’a Allah ya ba mu ruhu mai tsarki. (Luk. 11:13; Gal. 5:22, 23) Idan muka bar ruhu mai tsaki ya ja-gorance mu kuma muka kasance da ra’ayin Jehobah kamar yadda aka ambata a cikin Kalmarsa, za mu kasance da halayen da suke faranta wa Jehobah rai. Duk da haka, muna bukatar mu ci gaba da yin ƙoƙari don mu shawo kan kasawarmu.—Mis. 4:23.

Zai dace mu yi nazarin nassosi da kuma talifofin da suka tattauna yadda za mu iya sha kan kasawarmu (Ka duba sakin layi na 15)

15 Ban da karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai, muna bukatar mu yi nazarin Kalmar Allah da kuma littattafanmu don mu yi koyi da halayen Jehobah sosai. Wasu sun amfana ta wurin yin bitar wasu nassosi da talifofin Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! Waɗannan mujallun za su taimaka mana a ƙoƙarin da muke yi don mu kasance da halaye masu kyau kuma mu shawo kan kasawarmu.

16. Me ya sa bai kamata mu karaya ba idan yana ɗaukan lokaci kafin mu yi canje-canje a rayuwarmu?

16 Yin koyi da halayen Jehobah yana ɗaukan lokaci. Saboda haka, kana bukatar ka kasance da haƙuri yayin da kake barin Littafi Mai Tsarki ya ci gaba da gyara halayenka. Da farko, muna bukatar mu horar da kanmu don mu yi abin da yake da kyau. Da shigewar lokaci, zai kasance mana da sauƙi mu yi abin da Jehobah yake so idan muka bar tunaninmu da kuma ra’ayinmu su jitu da ƙa’idodinsa.—Zab. 37:31; Mis. 23:12; Gal. 5:16, 17.

KA YI TUNANIN YADDA RAYUWA ZA TA KASANCE A NAN GABA

17. Idan muka kasance da aminci ga Jehobah, wace rayuwa ce muke ɗokin yi a nan gaba?

17 Amintattun bayin Jehobah suna ɗokin lokacin da za su zama kamiltattu kuma su riƙa bauta masa har abada. A lokacin, ba zai mana wuya mu kasance da halaye masu kyau ba, amma za mu yi farin cikin yin koyi da Jehobah. Kafin lokacin, muna godiya saboda hadayar da Yesu ya ba da, domin yana taimaka mana mu bauta wa Allahnmu mai ƙauna. Za mu iya bauta wa Jehobah duk da ajizancinmu idan muka ci gaba da barin Kalmar Allah ta kyautata halayenmu.

18, 19. Ta yaya za mu kasance da tabbaci cewa Littafi Mai Tsarki yana da ikon canja rayuwarmu?

18 Ɗan’uwa Kevin da aka ambata farkon talifin nan ya yi ƙoƙari don ya riƙa kame kansa. Ya yi bimbini kuma ya bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ya bi shawarwarin da ’yan’uwa suka ba shi. A cikin ’yan shekaru, Kevin ya sami ci gaba kuma ya zama bawa mai hidima. Yanzu ya yi shekaru 20 yana hidima a matsayin dattijo a cikin ikilisiya. Duk da haka, ya ga cewa yana bukatar ya ci gaba da yin ƙoƙari don ya shawo kan kasawarsa.

19 Misalin Kevin ya nuna mana cewa Littafi Mai Tsarki yana taimaka wa mutanen Allah su ci gaba da kyautata rayuwarsu. Saboda haka, kada mu karaya wajen barin Kalmar Allah ta ci gaba da canja halayenmu don mu kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah. (Zab. 25:14) Yayin da muke ganin yadda Jehobah yake mana albarka saboda ƙoƙarin da muke yi, za mu kasance da tabbaci cewa Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu ci gaba da kyautata rayuwarmu.—Zab. 34:8.

^ [1] (sakin layi na 1) An canja sunan.