Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Na Ƙuduri Aniyar Zama Sojan Kristi

Na Ƙuduri Aniyar Zama Sojan Kristi

A lokacin da na ga cewa ana ruwan harsashe, sai na ɗaga farin hankicina sama, kuma sojojin da suke harbin suka yi ihu suka ce in fito daga wurin da na ɓuya. A hankali na je wurinsu ban san ko zan mutu ko zan rayu ba. Ta yaya na sami kai na a irin wannan yanayin?

AN HAIFE ni a shekara ta 1926 a wani ƙaramin ƙauye mai suna Karítsa da ke ƙasar Girka, iyayena masu aiki sosai ne kuma mu yara takwas suka haifa amma ni ne na bakwai a cikinsu.

Iyayena sun soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki a shekara ta 1925 da wani mai ƙwazo da sunansa John Papparizos kuma wannan mutumin yana yawan magana sosai. A lokacin, ana kiran Shaidun Jehobah Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. Yadda John yake bayyana Littafi Mai Tsarki ya burge su sosai, hakan ya sa suka soma halartan taron Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a ƙauyenmu. Mahaifiyata ta yi imani da Jehobah sosai, kuma ko da yake ba ta da ilimi sosai tana yi wa mutane wa’azi a duk lokacin da ta sami dama. Mahaifina kuma ya bar ajizancin wasu ya shafe shi har hakan ya sa ya daina halartan taro.

Ko da yake ni da ‘yan’uwana muna daraja Littafi Mai Tsarki sosai, mun bar sha’awoyin da ke damun matasa su raba hankalinmu. Amma, a shekara ta 1939 sa’ad aka soma Yaƙin Duniya na Biyu a Turai, akwai wani abin da ya faru a ƙauyenmu da ya ba mu mamaki sosai. Hukuma tana son wani danginmu na nesa mai suna Nicolas Psarras da yake zama kusa da gidanmu ya shiga aikin soja kuma bai daɗe da yin baftisma ba. Nicolas da shekararsa 20 ne a lokacin ya gaya musu cewa, “Ni ba zan iya yin yaƙi ba, saboda ni sojan Kristi ne.” Sai hukumar ta kama shi kuma kotun sojoji ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara goma a kurkuku. Hakan ya ba mu mamaki sosai!

Amma a shekara ta 1941, rundunar haɗin gwiwa ta shigo cikin ƙasar Girka kuma aka saki Nicolas daga kurkuku. Yayana Ilias ya yi masa tambayoyi sosai game da Littafi Mai Tsarki sa’ad da Nicholas ya dawo Karítsa. Kuma na saurari abin da suke tattaunawa sosai. Bayan hakan, ni da Ilias da kuma ƙanwata mai suna Efmorfia muka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma halartan taro a kai a kai. Bayan shekara ɗaya, mu ukun mun yi baftisma, daga baya ‘yan’uwana guda huɗu ma suka yi baftisma kuma suka zama Shaidun Jehobah.

A shekara ta 1942, muna da matasa maza da mata guda tara a ikilisiyar da ke Karítsa da shekarunsu tsakanin 15 da 25 ne. Kuma mun san cewa za mu fuskanci jarraba mai tsanani a nan gaba. Don mu ƙarfafa kanmu, mukan yi nazarin Littafi Mai Tsarki, mu rera waƙoƙinmu kuma mu yi addu’a tare. Yin hakan ya taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu sosai.

Demetrius da abokansa a Karítsa

YAƘIN BASASA

Da aka kusan gama Yaƙin Duniya na Biyu, ‘yan kwaminis na Girka suka yi wa gwamnatin Girka tawaye, kuma hakan ya jawo yaƙin basasa. Mayaƙan kwaminis suna yawo a ko’ina a ƙasar kuma suna tilasta wa mutanen da suke zama a ƙauyuka su shiga rukuninsu. Da suka zo ƙauyenmu, sai suka kama matasa guda uku wato Antonio Tsoukaris da ni da kuma Ilias. Mun roƙe su su bar mu don mu Kiristoci ne kuma ba ruwanmu da yaƙi, amma sun tilasta mana mu bi su zuwa Dutsen Olympus, tafiyar wajen awa 12 daga ƙauyenmu.

Ba da daɗewa ba, wani sojan ‘yan kwaminis ya umurce mu mu yi aiki tare da sojoji masu kai hari. Da muka bayyana masa cewa ba za mu yi hakan ba don imaninmu, sojan ya ji haushi kuma ya kai mu gaban wani janar. Da muka gaya wa janar ɗin abin da muka gaya wa sojojin, sai ya ce “Ku ɗau jaki don ku riƙa kai waɗanda suka ji rauni a filin dāga asibiti.”

Sai muka ce masa, “Idan sojojin gwamnati suka kama mu fa? Ba za su ɗauka cewa mu ma mayaƙa ba ne?” Sai ya ce “Ku riƙa kai ma mayaƙa abinci a filin dāga.” Sai muka ƙara ce masa “Idan wani soja ya gan mu da jaki kuma ya umurce mu mu kai makamai zuwa filin dāga kuma fa?” Janar ya yi dogon tunani kuma daga baya ya ce mana: “Babu shakka, za ku iya yin kiwon tumaki! Ku kasance a kan tudun nan ku riƙa kiwon tumaki.”

Yayin da ake wannan yaƙin basasar, mun ga cewa zuciyarmu ba za ta riƙa damunmu ba idan muna musu kiwon tumaki. Shekara ɗaya bayan hakan, an saki yayana Ilias kuma ya koma gida don ya kula da mahaifiyarmu da gwauruwa ce da yake shi ne ɗan fari. Antonio kuma ya soma rashin lafiya sai shi ma aka sake shi. Ni kuma aka riƙe ni a wurin.

A lokacin nan, sojojin Girka suna ƙara kusatowa inda ‘yan kwaminis suke. Waɗanda suka kama ni suka gudu suna son su shiga ƙasar Albania da ke kusa da inda muke. Sai sojojin Girka suka kewaye mu a kusa da iyakan ƙasar. ‘Yan tawaye suka ji tsoro kuma suka gudu. Da na ga haka, sai na ɓuya a bayan wata bishiyar da ta faɗi, yadda na sami kai na ke nan a yanayin da na ambata ɗazun.

Sa’ad da na gaya wa sojojin Girka cewa ‘yan kwaminis ne suka kama ni, sai suka kai ni sansanin sojojin da ke kusa da birnin Véroia don su yi mini tambayoyi. Wannan birni ne Littafi Mai Tsarki ya kira Biriya a dā. A wurin, an umurce ni in riƙa haka wa sojojin ramuka, amma da na ƙi yin hakan, sai hafsan sojojin ya sa aka kai ni fursuna a wani mugun yanki da ake kira Makrónisos da ke bakin tekun.

WURIN DA AKE WAHALAR DA FURSUNONI

Wannan wurin da ake kira Makrónisos yana gaɓar yankin Attica, kuma daga wurin zuwa birnin Athens wajen kilomita 50 ne. Tsayin yankin ya kai kilomita 13 kuma faɗinsa kilomita biyu da rabi ne. Duk da cewa yankin ba shi da girma, a shekara ta 1947 zuwa 1958, an kai fursunoni fiye da 100,000 a wurin, har da waɗanda ake gani ‘yan kwaminis ne da waɗanda suka yi wa gwamnati tawaye a dā da kuma Shaidun Jehobah.

Sa’ad da muka isa wurin a shekara ta 1949, an kai fursunonin zuwa sansani dabam-dabam. Kuma an saka ni a ɓangaren da ba a tsaro sosai tare da maza da yawa. Mu kusan 40 ne muke kwana a tantin da aka gina don mutane 10. Ƙari ga haka, ruwa mai wari ne muke sha kuma abincin da muke ci shi ne wake da yalo. Rayuwa a wurin yana da wuya saboda iska da ƙura da ake yi. Duk da haka, mun ji daɗi saboda ba ma aikin farfasa duwatsu, wannan aikin ya sa fursunoni da yawa sun mutu don irin azabar da suka sha.

Tare da wasu Shaidu a fursunan Makrónisos

Akwai ranar da nake yawo a bakin teku, sai na haɗu da Shaidu da yawa daga wasu sansani. Mun yi murna sosai da ganin juna! Kuma mukan mai da hankali sosai sa’ad da muka haɗu don kada a gan mu. Ƙari ga haka, mun yi ma wasu fursunoni wa’azi da basira, kuma wasu daga cikinsu sun zama Shaidun Jehobah. Yin wa’azi da kuma addu’a sun taimaka mana sosai mu ƙarfafa bangaskiyar mu.

NA SHIGA CIKIN TSAKA MAI WUYA

Bayan na yi wata goma ina shan wahala a kurkuku, sai sojojin da suka kama ni suka ce lokaci ya yi da zan saka kayan soja. Sa’ad da na ƙi yin hakan, sai suka kai ni gaban kwamandan sansanin. Kuma na miƙa masa takardar da na rubuta cewa, “Ni sojan Kristi kaɗai nake so in zama.” Ya tsoratar da ni sosai kuma ya tura ni zuwa wurin mataimakinsa, wani akbishop na cocin Orthodox na Girka da ya sanye da kayan limaman coci. Da ya yi min tambayoyi kuma na ba shi amsa daga Littafi Mai Tsarki, sai ya yi fushi ya ce: “Ku fitar da wannan mai tsattsauran ra’ayin daga nan!”

Washegari sojojin suka ƙara cewa in saka kayan soja, sa’ad da na ƙi, sai suka nannaushe ni suka yi mini dūka da kulki. Bayan haka, sai suka kai ni asibitin da ke sansanin don a duba ko ƙasusuwana sun karye, kuma suka ja ni zuwa tantina. Sun yi wata biyu suna dūkana.

Saboda na ƙi yin abin da suka ce, sai sojojin suka ƙara yin fushi kuma suka canja azabar da suke gana mini. Suna ɗaura hannuna ta baya kuma su riƙa dūkan tafin ƙafafuna da bulala. Sa’ad da nake shan wannan azabar sai na tuna da abin da Yesu ya ce: “Masu-albarka ne ku lokacin da ana zarginku, ana tsananta muku . . . Ku yi farin ciki, ku yi murna ƙwarai: gama ladarku mai-girma ce cikin sama: gama hakanan suka tsananta ma annabawan da suka rigaye ku.” (Mat. 5:11, 12) Bayan sun yi ta dūka na, sai na sume.

Na farfaɗo a cikin wani kurkuku mai sanyi sosai da babu burodi da ruwa ko kuma bargo. Duk da haka, na natsu, kuma kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, “salama kuwa ta Allah” ta ‘tsare zuciyata da tunanina.’ (Filib. 4:7) Washegari, wani soja mai kirki ya ba ni burodi da ruwan sha da kuma rigar sanyi. Wani ma a cikin sojojin ya ba ni abincinsa. Hakan ya nuna min cewa lallai Jehobah yana kula da ni.

Hukumomin suna yi mini kallon ɗan tawayen da ba zai taɓa canjawa ba, don haka, sai suka kai ni kotun da ke birnin Atina. A wurin aka yanke mini hukuncin shekara uku a kurkukun Yíaros, wani wurin da ke bakin teku mai nisan mil 30 daga gabashin Makrónisos.

“MUN AMINCE DA KU”

Kurkuku da ke Yíaros babban gini ne da aka yi da jan-bulo kuma a ciki akwai fursunonin siyasa wajen 5,000 da kuma Shaidun Jehobah guda bakwai da aka kama don sun ƙi yin yaƙi. Mukan yi nazarin Littafi Mai Tsarki a ɓoye, ko da yake an hana mu yin hakan. Ƙari ga haka, ana shigo mana da Hasumiyar Tsaro a ɓoye kuma mu kofa da hannu don mu yi amfani da ita a nazarin da muke yi.

Wani mai gadin fursunan ya kama mu wata rana da muke yin nazari a ɓoye, kuma ya ƙwace littattafanmu. Ƙari ga haka, ya kai mu gaban mataimakin shugaban masu gadin. Muna zaton za a ƙara mana shekarun da za mu yi a kurkukun amma mutumin ya ce mana: “Mun amince da ku, kuma muna daraja shawarar da kuka yanke. Ku koma bakin aikinku.” Ban da haka, ya ba wasu cikinmu aiki mai sauƙi, kuma hakan ya sa mu farin ciki sosai. Ko da yake an saka mu a kurkuku, amma amincinmu ya kawo yabo ga Jehobah.

Amincin da muka kasance da shi ya kawo wasu sakamako masu kyau. Wani fursuna wanda farfesa ne na lissafi ya nemi ya san abubuwan da muka yi imani da shi don ya ga cewa muna da halin kirki. Ƙari ga haka, an saki mutumin sa’ad da aka sake mu a shekara ta 1951, kuma daga baya ya yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah kuma ya soma yin hidima ta cikkaken lokaci.

HAR ILA NI SOJA NE

Ni da matata Janette

Bayan an sake ni, na koma gidanmu a ƙauyen Karítsa. Amma daga baya na koma birnin Melbourne da ke ƙasar Australia tare da mutane da yawa daga ƙasarmu. A nan ne na haɗu da Janette, wata ‘yar’uwa mai hankali kuma muka yi aure. Sai muka haifi yara huɗu, namiji ɗaya da mata uku kuma dukansu suna bauta wa Jehobah.

Yanzu na ba shekara 90 baya, amma har ila ni dattijo ne. Saboda raunin da na ji dā, jikina da kuma ƙafafuna sukan yi mini ciwo a wasu lokuta, musamman ma idan na fita wa’azi. Duk da haka, na ƙuduri niyya na ci gaba da zama sojan Kristi.2 Tim. 2:3.