Za Ka Iya Zama Aminin Allah
WASU SUNA GANIN CEWA . . .
Allah bai damu da mu ba ko kuma Allah ya yi nesa da mu, mai tsarki ne sosai kuma ba za a iya kusantar sa ba.
GA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE
“Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.”—Yaƙub 4:8.
“Ku danƙa masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.”—1 Bitrus 5:7.
ME ZA MU YI DON MU KUSACI ALLAH?
Ka riƙa addu’a.—Zabura 145:18, 19.
Ka saurare shi.—Zabura 32:8.
Ka riƙa bin shawararsa.—Karin Magana 3:5, 6.
Kada ka fid da rai a ƙoƙarin da kake yi don ka kusaci Allah.—Matiyu 7:7, 8.