TARIHI
“Yanzu Ina Jin Dadin Yin Wa’azi!”
NA YI girma a garin Balclutha da ke yankin South Island a ƙasar New Zealand. A lokacin da nake ƙarama, ina ƙaunar Jehobah kuma ina son bauta masa. Ina jin daɗin halartan taro kuma ina son cuɗanya da ’yan’uwa, hakan yana sa ni farin ciki. Ko da yake ni mai jin kunya ce, ina jin daɗin yin wa’azi a kowace mako. Ban ji tsoron yi wa abokan makarantarmu da kuma wasu wa’azi ba. Na yi alfahari cewa ni Mashaidiya ce, kuma sa’ad da nake ’yar shekara 11 na yi alkawarin bauta wa Jehobah.
NA DAINA FARIN CIKI
Abin baƙin ciki, sa’ad da na soma balaga, dangantakata da Jehobah ta soma yin sanyi. Kamar dai abokan makarantarmu suna da ’yancin yin abin da suke so, kuma ni ma ina son hakan. Na soma gani kamar dokokin iyayena da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suna hana ni sakewa, hakan ya sa na soma tunanin cewa bauta wa Jehobah yana da wuya. Ko da yake ban taɓa tunanin cewa Jehobah ba ya wanzuwa ba, amma shi ba abokina ba ne.
Amma ban daina yin wa’azi gabaki ɗaya ba, ina yi a wasu lokuta. Ba na yin shiri sosai kafin in fita wa’azi. Saboda haka, yana mini wuya in soma wa’azi ko kuma in ci gaba da tattaunawa da mutum. A sakamakon haka, ba ni da ɗalibai kuma ba na farin ciki a hidimata, hakan ya sa na daina son wa’azi. Nakan tambayi kaina, ‘Ta yaya mutum zai ci gaba da yin wannan hidimar a kowace rana?’
Sa’ad da na kai shekara 17, na so in riƙa yin abin da na ga dama. Sai na kwashe kayana
na ƙaura zuwa Ostareliya. Iyayena sun yi baƙin ciki da na bar gida kuma sun damu. Amma suna ganin cewa zan ci gaba da bauta wa Jehobah.A Ostareliya, dangantakata da Jehobah ta yi sanyi sosai. Sai na daina halartan taro a kai a kai. Na soma abokantaka da matasa kamar ni da suke halartan taro, bayan haka a je fati daddare da kulob ana shan giya da kuma cashewa. Idan na tuna rayuwata a lokacin, sai na ga cewa ina bauta wa Jehobah da kuma sha’ani sosai da mutanen duniya, amma ban sami sakewa a kowannensu ba.
NA KOYI DARASI MAI MUHIMMANCI
Bayan wajen shekara biyu, na haɗu da wata ’yar’uwa da ba tare da saninta ba ta sa na soma tunani game da rayuwata. Ina zama tare da wasu ’yan’uwa mata marasa aure guda huɗu, sai muka gayyaci mai kula da da’ira da matarsa mai suna Tamara su zauna a gidanmu na tsawon mako ɗaya. Sa’ad da maigidanta yake ayyukan ikilisiya, Tamara takan kasance tare da mu kuma mu yi wasa da dariya. Na ji daɗin hakan. Tana da sauƙin kai da kuma fara’a. Na yi mamaki cewa wadda ta shagala da hidimar Jehobah tana samun lokacin shaƙatawa.
Tamara tana da ƙwazo sosai. Yana da sauƙi ta sa ka soma son bauta wa Jehobah da kuma yin wa’azi. Tana farin cikin yin iya ƙoƙarinta a hidimar Jehobah, amma ni kuma ba na farin ciki domin ba na yin iya ƙoƙarina. Halinta da kuma yadda take farin ciki ya shafe ni sosai. Misalinta ya sa na yi tunani a kan wani abu mai muhimmanci da ke Littafi Mai Tsarki, cewa: Jehobah yana so mu yi masa “hidima da murna” da kuma “waƙoƙin farin ciki!”—Zab. 100:2.
YADDA NA SOMA SON YIN WA’AZI
Kamar Tamara, ina son in riƙa farin ciki, amma kafin in yi hakan, ina bukatar in yi wasu canje-canje. Ban yi canje-canjen nan take ba, amma a sannu a hankali sai na soma yin hakan. Na soma yin shiri kafin in fita wa’azi da kuma yin hidimar majagaba
na ɗan lokaci a wasu lokuta. Hakan ya taimaka mini in rage jin tsoro kuma in kasance da ƙarfin zuciya. Domin ina amfani da Littafi Mai Tsarki a wa’azi sosai, hakan ya sa na ji daɗin wa’azin. Nan ba da daɗewa ba, sai na soma yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a kowace wata.Na soma yin abokantaka da ’yan’uwa dabam-dabam da suke yin iya ƙoƙarinsu a hidimar Jehobah. Misalinsu ya taimaka mini in yi tunani a kan abin da ya fi muhimmanci a rayuwata kuma in soma karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. Wannan ne lokaci na farko bayan shekaru da yawa da na soma farin ciki kuma na saki jiki a ikilisiya.
NA SAMU ABOKIN WA’AZI
Shekara ɗaya bayan hakan, na haɗu da wani ɗan’uwa mai kirki mai suna Alex da ke ƙaunar Jehobah kuma yana son wa’azi. Shi bawa mai hidima ne kuma ya yi shekara shida yana hidimar majagaba. Alex ya yi hidima na ɗan lokaci a inda ake bukatar masu shela a Malawi. A wurin, ya yi cuɗanya da masu wa’azi a ƙasar waje da suka kafa masa misali mai kyau kuma suka ƙarfafa shi ya ci gaba da saka hidimar Jehobah a kan gaba.
A shekara ta 2003 ne ni da Alex muka yi aure, kuma mun ci gaba da yin hidimar majagaba tun lokacin. Mun koyi darussa da yawa kuma Jehobah ya yi mana albarka sosai.
JEHOBAH YA DAƊA YI MANA ALBARKA
A shekara ta 2009, an tura mu yin hidima a tsibirin Timor-Leste a matsayin masu wa’azi a ƙasar waje. Mun yi mamaki, mun yi farin ciki kuma mun ji tsoro. Bayan watanni biyar, sai muka isa birnin tarayyar mai suna Dili.
Rayuwa a ƙasar ta bambanta da wanda muka saba. Mun koyi sabon al’ada da yare da abinci da kuma rayuwa. A wa’azi, muna *
haɗuwa da mutanen da ke fama da talauci sosai, da waɗanda ba su yi karatu ba ko kuma ba su je makaranta sosai ba, da kuma waɗanda ake cin zarafinsu. Ƙari ga haka, mun haɗu da mutanen da ke fama da matsaloli domin yaƙe-yaƙe da ake yi a wurin.Mun ji daɗin wa’azi sosai! Alal misali, na taɓa haɗuwa da wata ’yar shekara 13 mai suna Maria * da take fuskantar matsaloli. Mahaifiyarta ta rasu ’yan shekaru kafin lokacin, kuma da ƙyar take ganin mahaifinta. Kamar tsararta da yawa, Maria ba ta san abin da za ta yi da rayuwarta ba. Na tuna wani lokaci da ta yi kuka sa’ad da take bayyana mini yadda take ji. Amma ban fahimci abubuwan da ta faɗa ba domin ba na jin yaren sosai. Na yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mini in ƙarfafa ta kuma na soma karanta mata nassosin da za su ƙarfafa ta. Bayan wasu shekaru, na ga yadda Littafi Mai Tsarki ya canja rayuwarta. Sai ta yi baftisma kuma yanzu tana nazari da mutane. A yanzu, Maria ta samu iyali a ƙungiyar Jehobah kuma tana ganin yadda ake ƙaunar ta.
Jehobah yana yi wa wa’azin da ake yi a Timor-Leste albarka. Yawanci masu shelar sun yi baftisma a cikin shekaru goma da suka shige, da yawa cikinsu suna yin hidimar majagaba da bayi masu hidima da kuma dattawa. Wasu suna aiki a ofishin fassara kuma suna taimakawa wajen fassara littattafai a yarukan da ake yi a ƙasar. Ina farin cikin ganin yadda suke rera waƙa a taro da yadda suke murmushi da kuma yadda suka zama abokan Jehobah.
BA RAYUWAR DA TA FI WANNAN DAƊI
Rayuwa a Timor-Leste ya bambanta da Ostareliya, amma mun ji daɗinta sosai. A wasu lokuta muna shiga motar da mutane suka cika maƙil kuma aka saka busashen kifi da kuma kayan miya. A wasu lokuta, mukan yi nazari da ɗalibanmu a ƙaramin gida mai zafi da ke da datti kuma kaji na guje-guje. Duk da ƙalubalen da muka fuskanta, ina yawan cewa ‘hakan na da ban sha’awa!’
Ina yawan godiya cewa iyayena sun koya mini game da Jehobah kuma sun taimaka mini sa’ad da nake girma. Abin da ke Karin Magana 22:6 gaskiya ne. Iyayena suna alfahari da ni da Alex kuma suna farin ciki cewa muna bauta wa Jehobah. Tun shekara ta 2016, muna hidimar mai kula da da’ira a yankin Australasia.
Ina mamaki cewa akwai lokacin da ba na son yin wa’azi. Yanzu ina son yin wa’azi sosai! Na fahinci cewa duk da matsalolin rayuwa, muna iya yin farin ciki idan muna bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Ina jin daɗin hidima tare da maigidana kuma mun yi shekaru 18 yanzu muna hidimar. Yanzu na tabbatar da gaskiyar abin da Dauda ya gaya wa Jehobah cewa: “Duk masu ɓuya a wurinka su yi farin ciki. Bari su dinga rerawa don farin ciki. . . . Masu ƙaunar Sunanka su yi murna saboda kai.”—Zab. 5:11.
^ sakin layi na 21 Tun daga 1975, an yi fiye da shekara 20 ana yaƙi a Timor-Leste domin mutanen suna so su sami ’yanci.
^ sakin layi na 22 An canja sunan.