Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI | RENON YARA

Yadda Za Ku Koya wa Yaranku Game da Jimaꞌi

Yadda Za Ku Koya wa Yaranku Game da Jimaꞌi

ABIN DA YA SA YAKE DA WUYA

A shekarun baya, iyaye ne suke fara gaya wa yaransu abubuwa game da yin jimaꞌi kuma su koya musu abubuwan da ya kamata su sani dangane da wannan batun.

Amma yanzu kome ya canja. Yanzu kananan yara suna ji kuma suna ganin abubuwa game da jimaꞌi sosai. Kuma yawan abubuwan nan da ake sakawa a littattafai da fina-finai da kuma shirye-shiryen da ake yi don yara, sai karuwa suke yi, in ji wani littafi mai suna The Lolita Effect. Yaya abubuwan nan suke shafan tunanin yara?

ABIN DA YA KAMATA KA SANI

Abubuwa game da jimaꞌi suna koꞌina. A wani littafi da Deborah Roffman ta rubuta, mai suna Talk to Me First, ta ce “Mutane suna maganganu game da jimaꞌi, kuma ana nuna hotuna da kuma bidiyoyi da suke dauke da batsa a tallace-tallace da fina-finai da littattafai da wakoki da shirye-shiryen talabijin da sakonnin waya da wasanni da su fosta. Har ila, ana kallonsu a wayoyi da kuma kwamfuta. Abubuwan nan suna sa matasa da yara kanana su dauka cewa ba abin da ya kai yin jimaꞌi muhimmanci a rayuwa.”

Yadda ꞌyan kasuwa suke jawo hakan. Wani littafi mai suna So Sexy So Soon ya ce: “ꞌYan kasuwa suna son yin tallen kayan yara da ke nuna tsiraici. Kuma hakan yana sa yara su dauka cewa ya kamata su yi shigar da za ta jawo hankalin mutane ya koma kansu. ꞌYan kasuwa sun san cewa yara suna son yin abin da zai sa abokansu su so su, kuma suna son bin halin abokansu, shi ya sa suke bi ta wannan hanyar don su sami ciniki.” Littafin ya kuma kara da cewa “Ana amfani da wadannan hotuna da kayayyakin da ke nuna tsiraici ne don a rinjayi yara su so sayan kayayyakin, ba don a koya musu yin jimaꞌi ba.”

Sanin abubuwa game da jimaꞌi bai isa ba. Mutum zai iya sanin yadda mota take aiki, amma ba lallai ba ne a ce ya iya tuki ba. Haka ma ko da danka ko ꞌyarka ta san abubuwa game da jimaꞌi, ba lallai hakan ya sa ta dauki matakin da ya dace ba.

Gaskiyar batun: A wannan zamanin da muke ciki, yana da muhimmanci ku koya ma yaranku yadda za su yi “amfani da hankalinsu” don su “iya bambanta nagarta da mugunta.”​—Ibraniyawa 5:14.

ABIN DA ZAI TAIMAKA MA IYAYE

Ku tattauna da yaranku. Ko da kuna jin kunyar yin magana da yaranku game da jimaꞌi, ku tuna cewa hakkinku ne ku koya musu abin da suke bukata su sani.​—Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: Karin Magana 22:6.

Ku dinga dan kawo batun a lokacin da hankalinsu ya kwanta. Maimakon ku zaunar da yaranku ku musu dogon jawabi, ku dinga magana a kan batun saꞌad da kuke harkokinku na yau da kullum. Alal misali, idan kuna tafiya tare da su a mota ko saꞌad da kuke wani aiki a gida. Idan kana so danka ya gaya maka abin da ke zuciyarsa, ka yi masa tambayoyi. Kar ka ce masa, “Kana son kallon irin wadannan tallace-tallacen?” a maimakon haka ka tambaye shi, “A ganinka, me ya sa ꞌyan kasuwa suke amfani da irin wadannan hotunan a tallace-tallacensu?” Bayan ka ji raꞌayinsa, za ka iya tambayarsa cewa, “A ganinka akwai laifi a wannan abin da suke yi?”​—Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: Maimaitawar Shari’a 6:​6, 7. 

Ku koya wa yaranku ilimin jimaꞌi daidai da shekarunsu. Kafin yaronka ya isa zuwa makaranta, za ka iya koya masa yadda ake kiran gabobin jiki da ake amfani da su wajen jimaꞌi, da kuma abin da zai yi don kar wani ya taba shi, ko ya ci zarafinsa ta hanyar jimaꞌi. Yayin da yara suke girma, iyaye za su iya koya musu yadda ake yi a haifi mutum a hanya mai saukin fahimta. Yayin da suke balaga kuma, ya kamata a ce sun fahimci abin da ake nufi da yin jimaꞌi sosai da kuma raꞌayin Allah game da shi.

Ku koya ma yaranku su san abin da ke da kyau da marar kyau. Tun yaronka yana karami, ka koya masa ya dinga fadin gaskiya, ya yi abin da ya dace kuma ya dinga girmama mutane. Hakan zai sa tattauna batun jimaꞌi da shi, ya zo maka da sauki. Kuma gaya masa karara abin da kake ganin ya dace da wanda bai dace ba. Alal misali, idan ka yarda cewa yin jimaꞌi kafin a yi aure bai dace ba, ka sanar da shi. Kuma ka bayyana masa abin da ya sa hakan bai dace ba da kuma illarsa. “Idan yara suka san cewa iyayensu ba sa son su da yin jimaꞌi, zai yi wuya su yi hakan.” In ji littafin nan, Beyond the Big Talk.

Ku nuna hali mai kyau don su gani. Ku dinga yin abin da kuke koya musu. Alal misali, mutane sukan yi maganganun iskanci don su ba da dariya. Idan kuka ji irin maganganun nan, kukan yi dariya ne? Yaya tufafin da kuke sakawa, suna nuna tsiraicinku? Kuna yin kwarkwasa, wato nuna cewa kuna shaꞌawar wani ko wata da ba aure ya hada ku ba? Idan kuna yin abubuwan nan, zai yi wuya yaranku su saurari abin da kuke koya musu game da yin jimaꞌi.​—Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: Romawa 2:21.

Jimaꞌi abu mai kyau ne da Allah ya shirya mana. Allah ne ya halicce mu yadda za mu iya yin jimaꞌi. Kuma idan namiji da ta mace suka yi aure, yin jimaꞌi zai iya sa su ji dadi sosai. (Romawa 2:21) Ka gaya ma yaronka cewa da zarar ya yi aure, shi ma zai iya more wannan baiwar. Kuma a lokacin ba zai yi fama da matsalolin da ke tattare da yin jimaꞌi tun mutum bai yi aure ba.​—1 Timoti 1:​18, 19.