DARASI NA 5
Mene Ne Za Ka Gano a Taronmu na Kirista?
Mutane da yawa sun daina zuwa wuraren bauta domin sun kasa samun amsoshin tambayoyi masu muhimmanci game da rayuwa. Amma, me ya sa ya kamata ka halarci taron Kirista da Shaidun Jehobah suka tsara? Mene ne za ka shaida a wurin?
Za ka yi farin ciki domin kana tsakanin mutanen da suke ƙaunar juna kuma suna kula da juna. A ƙarni na farko, an rarraba Kiristoci zuwa ikilisiyoyi dabam-dabam, kuma suna taro don su bauta wa Allah, su yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma su ƙarfafa juna. (Ibraniyawa 10:24, 25) Saboda ƙaunar da suke nuna wa juna, sun ji kamar suna tsakanin abokansu na gaskiya, wato, ’yan’uwansu Kiristoci maza da mata. (2 Tasalonikawa 1:3; 3 Yohanna 14) Irin misalin da muke bi ke nan a yau, kuma muna farin ciki kamar Kiristoci na ƙarni na farko.
Za ka koyi yadda za ka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Kamar yadda aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki, maza da mata da kuma yara suna haɗuwa a wuri guda. Ƙwararrun malamai suna amfani da Littafi Mai Tsarki don su taimaka mana mu san yadda za mu bi ƙa’idodinsa a rayuwarmu ta yau da kullum. (Kubawar Shari’a 31:12; Nehemiya 8:8) Dukan waɗanda suka halarci wannan taron za su iya yin waƙa da furuci sa’ad da aka gayyaci masu sauraro su yi hakan, kuma wannan yana ba mu damar furta begenmu na Kirista.—Ibraniyawa 10:23.
Bangaskiyarka ga Allah za ta ƙara ƙarfi. Manzo Bulus ya gaya wa wata ikilisiya a zamaninsa cewa: “Ina marmarin ganinku, . . . mu sami ƙarfafawa a wurinku, kowannenmu ta wurin bangaskiyar junanmu, taku da tawa kuma.” (Romawa 1:11, 12) Kasancewa tare da ’yan’uwa Kiristoci a wajen taronmu a kai a kai yana ƙarfafa bangaskiyarmu da ƙudurinmu na ci gaba da bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.
Me zai hana ka karɓi wannan gayyatar na halartar taronmu na gaba don ka ga waɗannan abubuwan da kanka? Za a marabce ka da hannu bibiyu. Ba a karɓan ko sisi a wajen taronmu.
-
Bisa wane gurbi ne aka tsara taronmu?
-
Ta yaya za mu amfana idan muka halarci taron Kirista?