DARASI NA 17
Waɗanne Irin Halaye Ne Yesu Yake da Su?
Yayin da muke koyan abubuwan da Yesu ya faɗa kuma ya yi a duniya, za mu san halayensa. Hakan zai sa mu zama aminan Yesu da kuma Jehobah. Waɗanne irin halaye masu kyau ne Yesu yake da su? Kuma ta yaya za mu yi koyi da Yesu?
1. Ta yaya Yesu yake yin koyi da Ubansa?
Yesu ya yi shekaru da yawa a sama yana kallon abin da Jehobah yake yi kuma yana koya. Saboda haka, ra’ayinsa da tunaninsa da kuma ayyukansa kamar na Ubansa ne. (Karanta Yohanna 5:19.) Yesu yana da irin halayen Jehobah, shi ya sa ya ce: “Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban.” (Yohanna 14:9) Yayin da kake ƙara koya game da halayen Yesu, hakan zai sa ka san Jehobah sosai. Alal misali, yadda Yesu ya damu da mutane ya nuna yadda Jehobah yake damuwa da kai.
2. Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah?
Yesu ya ce: “Ina yin daidai abin da Uba ya faɗa mini in yi ne domin duniya ta sani ina ƙaunar Uban.” (Yohanna 14:31) Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna yana ƙaunar Ubansa sosai ta wajen yi masa biyayya har a lokacin da yin hakan yake da wuya. Yesu yana son yin magana game da Jehobah kuma yana taimaka wa mutane su ƙulla dangantaka da Shi.—Yohanna 14:23.
3. Ta yaya Yesu ya nuna yana ƙaunar mutane?
Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu yana son “’yan Adam” sosai. (Karin Magana 8:31) Ya nuna wannan ƙaunar ta wajen ƙarfafa mutane da kuma taimaka musu sosai. Ya yi mu’ujizai da suka nuna cewa yana da iko kuma yana jin tausayin mutane. (Markus 1:40-42) Yana nuna wa mutane alheri kuma ba ya nuna bambanci. Kalmominsa sun ƙarfafa mutanen da suka saurare shi kuma sun sa su kasance da bege. Yesu yana shirye ya sha wahala kuma ya mutu domin yana ƙaunar ’yan Adam. Amma ya fi ƙaunar waɗanda suke bin koyarwarsa.—Karanta Yohanna 15:13, 14.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu koyi game da halayen Yesu, da kuma yadda za mu nuna ƙauna da alheri kamar shi.
4. Yesu yana ƙaunar Jehobah
Mun koyi yadda za mu riƙa ƙaunar Allah daga abubuwan da Yesu ya yi. Ku karanta Luka 6:12 da Yohanna 15:10; 17:26. Bayan kun karanta kowane nassi, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Ta yaya za mu yi koyi da Yesu kuma mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah?
5. Yesu ya damu da mabukata
Yesu ya damu da bukatun mutane fiye da nasa. Ko a lokacin da ya gaji, ya yi amfani da lokacinsa da kuzarinsa don ya taimaka wa mutane. Ku karanta Markus 6:30-44, sai ku tattauna tambayoyin nan:
-
A wannan labarin, waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna ya damu da mutane?—Ka duba ayoyi na 31, 34, 41, da 42.
-
Mene ne ya sa Yesu ya taimaka wa mutane?—Ka duba aya ta 34..
-
Tun da yake Yesu ya yi koyi da halayen Jehobah, mene ne hakan ya koya maka game da Jehobah?
-
A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin koyi da yadda Yesu ya damu da mutane?
6. Yesu mai alheri ne
Duk da cewa Yesu ba mai arziki ba ne, ya taimaka wa mutane da abin da yake da shi. Kuma ya ƙarfafa mu mu riƙa yi wa mutane alheri. Ku karanta Ayyukan Manzanni 20:35, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Kamar yadda Yesu ya faɗa, me zai sa mu zama masu farin ciki?
Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.
-
A waɗanne hanyoyi ne za mu iya bayarwa, ko da ba mu da arziki?
Ka sani?
Littafi Mai Tsarki ya koya mana mu riƙa yin addu’a cikin sunan Yesu. (Karanta Yohanna 16:23, 24.) Idan muka yi addu’a hakan, muna nuna godiya don abin da Yesu ya yi don ya taimaka mana mu zama aminan Jehobah.
WASU SUN CE: “Wahalar da muke sha ƙaddara ce daga Allah.”
-
Tun da yake Yesu yana da irin halayen Jehobah, ta yaya ayyukansa suka nuna cewa ba Jehobah ne yake sa mu sha wahala ba?
TAƘAITAWA
Yesu yana ƙaunar Jehobah da kuma mutane. Tun da Yesu yana da irin halayen Jehobah, idan ka san shi, za ka san Jehobah sosai.
Bita
-
Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah kamar yadda Yesu ya yi?
-
Ta yaya za mu nuna muna ƙaunar mutane kamar yadda Yesu ya yi?
-
Wane halin Yesu ne ka fi so?
KA BINCIKA
Ku karanta talifin nan don ku koyi wasu halayen Yesu da za ku iya yin amfani da su a rayuwarku.
Ku karanta talifin nan don ku koyi muhimmancin yin addu’a cikin sunan Yesu.
“Me Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Addu’a a Cikin Sunan Yesu?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Fabrairu, 2008)
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda Littafi Mai Tsarki ya yi bayani game da kamannin Yesu.
Ku karanta talifin nan don ku ga abin da za mu iya koya daga yadda Yesu ya daraja mata.
“Mata Suna da Mutunci A Gaban Allah” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Oktoba, 2012)