Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 15

Me Ya Sa Ya Kamata Ka Ci Gaba?

Me Ya Sa Ya Kamata Ka Ci Gaba?

1. Ta yaya za ka amfana idan ka ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki?

Babu shakka, wannan fitattun koyarwa ta Littafi Mai Tsarki da aka tattauna sun sa ka ƙara ƙaunar Jehobah. Zai dace ka ci gaba da ƙarfafa wannan ƙaunar. (1 Bitrus 2:2) Za ka samu rai na har abada idan ka ci gaba da kusantar Allah ta wajen yin nazarin Kalmarsa.​—Karanta Yohanna 17:3; Yahuda 21.

Yayin da kake daɗa koyon abubuwa da yawa game da Allah, bangaskiyarka za ta daɗa yin ƙarfi. Bangaskiya za ta taimaka maka ka faranta wa Allah rai. (Ibraniyawa 11:1, 6) Hakan za ta motsa ka ka tuba kuma ka yi canja-canjen da za su amfane ka a rayuwarka.​—Karanta Ayyukan Manzanni 3:19.

2. Ta yaya mutane za su amfana daga abubuwan da ka koya game da Allah?

Za ka iya more dangantaka ta musamman da Jehobah

Babu shakka za ka so ka faɗa wa wani abin da ka koya don kowane mutum yana jin daɗin gaya wa mutane albishiri. Yayin da kake ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka koya yadda za ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki don bayyana wa mutane game da Jehobah da kuma bishara.​—Karanta Romawa 10:13-15.

Mutane da yawa suna soma yin hakan ne ta wajen tattaunawa da abokansu ko kuma danginsu. Amma, ka yi magana da hikima. Kada ka ce musu suna cikin addinin ƙarya. Maimakon haka, ka yi magana a kan alkawuran da Allah ya yi. Ka kuma tuna cewa gani ya kori ji, wato, halinka mai kyau ne zai sa mutane su saurare ka.​—Karanta 2 Timotawus 2:24, 25.

3. Wace dangantaka ce za ka iya morewa da Allah?

Yin nazarin Kalmar Allah za ta taimaka maka ka kyautata dangantarka da Jehobah. Daga baya, za ka samu dangantaka na kud da kud da Jehobah. Za ka iya kasancewa cikin iyalinsa.​—Karanta 2 Korintiyawa 6:18.

4. Ta yaya za ka samu ci gaba?

Za ka kyautata dangantakarka da Jehobah ta wajen yin nazarin Kalmarsa. (Ibraniyawa 5:13, 14) Ka gaya wa wani Mashaidin Jehobah ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai da taimakon littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?Idan kana nazarin Kalmar Allah, za ka yi nasara a rayuwa sosai.​—Karanta Zabura 1:1-3; 73:27, 28.

Allah mai farin ciki ne tushen wannan bisharar. Za ka iya kusantarsa ta wajen kusantar bayinsa. (Ibraniyawa 10:24, 25) Idan ka ci gaba da yin ƙoƙari don faranta wa Jehobah rai, za ka samu rai na har abada. Abu mafi kyau da za ka yi shi ne kusantar Allah.​—Karanta 1 Timotawus 1:11; 6:19.