Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

29 ga Yuli–4 ga Agusta

ZABURA 69

29 ga Yuli–4 ga Agusta

Waƙa ta 13 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Yadda Aka Annabta Abubuwan da Za Su Faru da Yesu a Zabura 69

(minti 10)

An tsane Yesu ba dalili (Za 69:4; Yoh 15:​24, 25; w11 8/15 11 sakin layi na 17)

Yesu ya kasance da ƙwazo wajen ibada (Za 69:9; Yoh 2:​13-17; w10 12/15 8 sakin layi na 7-8)

Yesu ya shiga damuwa sosai kuma an ba shi ruwan inabi haɗe da wani abu mai ɗaci (Za 69:​20, 21; Mt 27:34; Lu 22:44; Yoh 19:34; g95-E 10/22 31 sakin layi na 4; it-2-E 650)


DON BIMBINI: Me ya sa Jehobah ya sa aka yi annabce-annabce game da Yesu a Nassosin Ibrananci?

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 69:​30, 31—Ta yaya ayoyin nan za su taimaka mana mu inganta adduꞌoꞌinmu? (w99 2/1 16 sakin layi na 11)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 69:​1-25 (th darasi na 2)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Haƙuri—Abin da Yesu Ya Yi

(minti 7) Tattaunawa. Ku kalli BIDIYON, sai ku tattauna lmd darasi na 8 batu na 1-2.

5. Haƙuri—Ka Yi Koyi da Yesu

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 134

6. Bukatun Ikilisiya

(minti 5)

7. Ƙaꞌidodi don Bauta Ta Iyali da Yamma

(minti 10) Tattaunawa.

A Janairu 2009, an haɗa Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya da Makarantar Hidima ta Allah da kuma Taron Hidima. Hakan ya ba wa iyalai dama yin ibada ta iyali sau ɗaya a mako kuma su ne za su zaɓi abin da za su tattauna. Iyalai da yawa sun nuna godiya don wannan shirin da aka yi da zai taimaka musu su kusaci Jehobah da kuma juna.—M.Sh 6:​6, 7.

Waɗanne ƙaꞌidodi ne za su iya taimaka wa magidanta su tsara ibada ta iyalinsu da kyau?

  • Ku riƙa yi a kai a kai. Idan zai yiwu, ku kafa lokacin da za ku riƙa yin ibada ta iyali a kowane mako. Ku kafa wata ranar da za ku iya yin ibadar idan wani abu ya hana ku yi a ranar da kuka saba

  • Ku yi shiri da kyau. Kai da matarka ku zaɓi abin da za ku tattauna, kuma a wasu lokuta, ku tambayi yaranku abin da za su so ku tattauna. Ba lalle ne yin shirin ya ɗau lokaci sosai ba, musamman idan iyalin sun saba yin abubuwa kusan iri ɗaya kowane mako

  • Ku tsara shi bisa ga bukatun iyalinku. Saꞌad da yara suke girma, bukatunsu da kuma iliminsu yakan canja. Ku tattauna abin da kowa a iyalin zai amfana kuma ya kusaci Jehobah

  • Ya kamata lokacin ya zama na farin ciki. A wasu lokuta, idan zai yiwu ku yi nazarin a waje. Idan da bukata, ku ɗan huta kafin ku ci gaba. Ko da yake lokacin ibada ta iyali lokaci ne da za a iya warware wasu matsalolin iyali, kada ku yi amfani da zarafin wajen yin faɗa ko ba da horo

  • Ku riƙa yin abubuwa dabam-dabam. Alal misali, za ku iya shirya taro a ibadarku ta iyali ko ku kalli kuma ku tattauna wani bidiyo daga jw.org/ha ko kuma ku shirya abin da za ku faɗa a waꞌazi. Ko da yake tattaunawa ne ake yawan yi a ibada ta iyali, a wasu lokuta, kowannenku zai iya yin nasa nazarin

Ku tattauna tambayar nan:

  • Shin, ka taɓa yin ƙoƙarin bin waɗannan ƙaꞌidodin a ibadarku ta iyali?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 114 da Adduꞌa