13 GA DISAMBA, 2021
NIJERIYA
Shaidun Jehobah Sun Tuna da Cikar Shekaru 100 da Soma Wa’azi a Nijeriya
1921-2021: Daga Masu Shela Kadan Zuwa Masu Shela Fiye da 400,000
Shaidun Jehobah a Nijeriya sun yi abubuwa guda biyu na musamman don su tuna da cika shekara 100 da soma wa’azi a kasar. A ranar 12 ga Disamba, 2021, duka ikilisiyoyi a kasar sun halarci taro na musamman inda suka saurari jawabai da ganawa da aka riga aka yi kafin lokacin game da ci gaban aikin wa’azi a kasar. An yi taron da Turanci kuma an fassara shi zuwa yaren Efik, da Igbo, da Yaren Kurame na Nijeriya, da yaren Pidgin (West Africa), da kuma Yarbanci. Kafin ranar, wato a ranar 10 ga Disamba, 2021, sun bude gidan ajiye kayan tarihi a reshen ofishinsu da ke kasar. A yanzu haka, wadanda suke hidima a ofishin ne kadai za su iya zuwa gidan tarihin, amma da shigewar lokaci, za a bari baki su shiga.
An yi wa gidan tarihin lakabi da “100 Years of Courage.” Kayayyakin tarihin suna bayyana yadda Shaidun Jehobah suka nuna bangaskiya a kasar. Kari ga haka, suna nuna cewa Shaidun Jehobah a Nijeriya sun nuna karfin zuciya sosai sa’ad da aka yi musu ba’a, aka saka musu takunkumi, kuma aka soma wani mummunan yakin basasa. Baki za su iya sauraron sauti da kuma kallon bidiyoyi game da asalin kayayyakin tarihi da ke wurin kuma su ga yadda rayuwa ta kasance wa ’yan’uwa a lokacin. Baki za su iya ganin ci gaban aikin wa’azi a Nijeriya daga watan Disamba, 1921, a lokacin da masu shela kadan ne kawai suke halartan azuzuwan nazarin Littafi Mai Tsarki a Legas, zuwa yanzu da masu shela fiye da 400,000 suke wa’azi a duk fadin kasar.
Shaidun Jehobah a Nijeriya da kuma fadin duniya za su iya koyan karfin zuciya daga misalin ’yan’uwa a Nijeriya da suka yi wa’azi a cikin shekaru 100 da suka shige.—Yohanna 16:33.