Koma ka ga abin da ke ciki

’Yan’uwa 12 da aka tuhuma a shekara ta 2012 suna dauki hoto tare da lauyoyinsu (tsakiya) a watan Janairu 2019

9 GA DISAMBA, 2019
ARMENIA

Hukumomi a Armeniya Sun Daure ’Yan’uwa 22 Don Sun Ki Shiga aikin Soja

Hukumomi a Armeniya Sun Daure ’Yan’uwa 22 Don Sun Ki Shiga aikin Soja

A ranar 5 ga Disamba 2019, Kotun Turai Ta Kāre Hakkin Dan Adam ta yanke hukunci cewa bai dace tsare Shaidun Jehobah 22 da suka ki yin aikin soja saboda imaninsu ba. Kotun ta sa a biya su diyyar dalla 267,000. Wannan shi ne diyya mafi yawa da Kotu ta taba yanke hukunci cewa a ba ’yan’uwanmu domin an tsare su don sun ki shiga aikin soja.

A 2012 ne aka daure wadannan ’yan’uwa don sun ki shiga aikin soja da kuma kin yin aikin farar hula da sojoji ke ja-goranci saboda imaninsu. ’Yan’uwan sun ki yin aikin ne, domin a lokacin aikin na karkashin ja-gorancin sojoji. An taba yanke wa 20 a cikin ’yan’uwan hukuncin zama a kurkuku kafin 2013, a lokacin da gwamnatin kasar Armeniya ta kafa aikin farar hula da sojoji ba sa yin ja-goranci a kai kuma ta daina saka ’yan’uwa a kurkuku.

Yayin da Kotun take yanke hukunci a ranar 5 ga Disamba, ta dogara ne ga nasara da Shaidun Jehobah suka yi a 2017 wato a Shari’a tsakanin Adyan da wasu da gwamnatin Armeniya. Kotun Turai Ta Kāre Hakkin Dan Adam ta ce Armeniya tana sane da wannan hukunci da aka yanke, don haka yakamata a ce sun nema sulhu cikin lumana da ’yan’uwa 22. Duk da kokarin da ’yan’uwanmu suka yi a shekara da ta wuce, gwamnati ta ki yarda a sulhunta. Don haka, Kotun Turai ta Kāre Hakkin Dan Adam ta goyi bayan ’yan’uwan kuma ta ce ba su da laifi.

Abin farin ciki shi ne cewa gwamnatin kasar Armeniya tana kokarin canja ra’ayinta game da kin shiga aikin soja tun 2013. Ba a saka ’yan’uwanmu kurkuku ko kuma tuhume su don sun kin shiga aikin soja. Tun shekaru 7 da suka shige, aikin farar hula da gwamnatin Armeniya ta kirkiro, ya zama abin koyi ga wasu kasashe. Amma hukuncin da Kotun Turai ta Kāre Hakkin Dan Adam ta yanke a ranar 5 ga Disamba ya same gwamnatin Armeniya kin bin dokar Kasa da Kasa na 2012.

Wannan matakin da kotu ta yanke ya nuna cewa a shirye take don hukunta duk kasar da ta keta dokar kāre hakkin Adam da Majalisar Dikin Duniya ta kafa. Mun gode wa Jehobah don wannan nasara da ’yan’uwanmu a Armeniya suka yi. Muna addu’a cewa ’yan’uwanmu a wasu kasashe kamar su Azerbaijan da Koriya ta Kuda da Turkiya da kuma Turmennistan su sami damar yin aikin farar hula a maimakon na soja.