Shin Ya Kamata Na Yi Addu’a ga Waliyai?
Amsar Littafi Mai Tsarki
A’a. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mu yi addu’a ga Allah kadai kuma a cikin sunan Yesu. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Da hakanan fa za ku yi addu’a: Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) Bai taba gaya wa almajiransa su yi addu’a ga waliyai ko mala’iku, ko kuma wani ban da Allah ba.
Yesu ya kuma gaya wa mabiyansa: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Yesu ne kadai Allah ya ba wa iznin zama mai roko a madadinmu.—Ibraniyawa 7:25.
Idan na yi addu’a ga Allah da kuma waliyai fa?
A cikin Dokoki Goma, Allah ya ce: “Ni Ubangiji Allahnka Allah mai-kishi ne.” (Fitowa 20:5) Ta yaya Allah “mai-kishi” ne? Hasiya na cikin New American Bible ta ce yana “bukatar biyayya da zuciya daya.” Allah ya bukaci a yi biyayya da sujada da kuma addu’a gare shi kadai.—Ishaya 48:11.
Muna bata wa Allah rai idan muka yi addu’a ga wani, har ma ga waliyai ko mala’iku masu tsarki. Sa’ad da manzo Yohanna ya so ya yi wa mala’ika sujjada, mala’ikan ya hana shi yana cewa: “Kada ka yarda ka yi: ni abokin bauta ne tare da kai da ’yan’uwanka wadanda su ke rike da shaidar Yesu: ka yi sujjada ga Allah.”—Ru’ya ta Yohanna 19:10.