Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Batsa? Laifi ne Yin Tadin Lalata da Waya?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Littafi Mai Tsarki bai ambata kome game da hotunan tsirarun mutane, jima’i ta intane, ko irin ayyukan nan kai tsaye ba. Amma Littafi Mai Tsarki ya ambata sarai yadda Allah yake ji game da irin halayen nan da ke karfafa yin jima’i da ba a tsakanin miji da matarsa ba ne ko kuma mummunar jima’i. Yi la’akari da wadannan ayoyi na Littafi Mai Tsarki:
“Ku matar da gababuwanku fa wadanda ke a duniya; fasikanci, kazanta, kwadayi, mugun guri, da sha’awa.” (Kolosiyawa 3:5) Kallon hotunan tsirarun mutane ba zai matar da sha’awar lalata ba zai dada sha’awar yin jima’i ne. Yana sa mutum ya zama mai kazanta gaban Allah.
‘Duk wanda ya dubi mace duban sha’awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita.’ (Matta 5:28) Kallon hotunan lalatar jima’i yana ta da mummunar sha’awar aikata mugun abu.
“Fasikanci, da dukan kazanta, ko sha’awa, kada a ko ambata a cikinku, gama haka ya kamata ga tsarkaka.” (Afisawa 5:3) Kada ma mu ambata mugun jima’i cikin wasa ko kuma mu kalla ko yi karatu game da shi ba.
“Ayyukan jiki fa a bayyane su ke, fasikanci ke nan, kazanta, ... da irin wadannan: ina kuwa fadakar da ku, kamar yadda na rigaya na fadakar da ku, su wadanda ke aika wadannan al’amura ba za su gaji mulkin Allah ba.” (Galatiyawa 5:19-21) Allah yana daukan duk wanda yake kallon hotunan tsirarun mutane, yake jima’i ta intane, da kuma yake aika sakon hotunan lalata kazami ne kuma marar dabi’a. Idan fa muka ci gaba da aikata irin wadannan ayyuka ba za mu sami tagomashin Allah ba.