Jimrewa da Ciwo Mai Tsanani—Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimakawa Kuwa?
Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da
Hakika. Allah yana kula da bayinsa da suke rashin lafiya. Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da wani mai aminci cewa: “Ubangiji zai taimake shi sa’ad da yake ciwo.” (Zabura 41:3, Littafi Mai Tsarki) Idan kana fama da wani ciwo mai tsanani, wadannan matakai uku za su taimake ka ka jimre:
Ka yi addu’a don ka sami karfin jimrewa. Za ka iya samun “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka,” wadda za ta iya taimakonka ka jimre da duk matsalolin da kake fuskanta.—Filibiyawa 4:6, 7.
Ka kasance da ra’ayi mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kasancewa da murna yakan ba ka lafiya. Zama da bakin rai dukan lokaci mutuwar tsaye ce.” (Misalai 17:22, LMT) Ka kasance mai wasa da dariya, domin wannan zai sa ka zama da farin ciki a kowane lokaci kuma zai taimaki lafiyar jikinka.
Ka kasance da bege a alkawuran da Allah ya yi. Kasancewa da bege zai taimake ka ka yi farin ciki kome tsananin ciwonka. (Romawa 12:12) Littafi Mai Tsarki ya annabta game da lokacin da “Ba wanda zai zauna a kasarmu har ya kara yin kukan yana ciwo.” (Ishaya 33:24, LMT) A lokacin, Allah zai warkar da cututtuka masu tsanani da ’yan Adam sun kasa magancewa a yau. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana cewa tsofaffi za su dawo matasa: “Namansa za ya komo ya fi na yaro sabontaka; ya komo kwanakin kuruciyarsa.”—Ayuba 33:25.
Abin lura: Ko da Shaidun Jehobah sun fahimci taimako da Allah yake bayarwa, hakan ba ya hana su yin jinya idan suna ciwo mai tsanani. (Markus 2:17) Amma fa, ba ma gaya wa mutane irin jinyar da za su yi; domin muna ganin ya dace kowane mutum ya tsai da nasa shawara game da jinyar da ya dace masa.