TAMBAYOYIN MATASA
Me Ya Sa Bai Dace Ku Kwaikwayi Taurarin Kafofin Sadarwa Ba?—Sashe na 1: Don ’Yammata
Mene ne kwaikwayon taurarin kafofin sadarwa ya kunsa?
Ki karanta sassa biyu da ke gaba sa’an nan ki amsa tambayoyin da suka biyo baya.
Sashe na 1 |
Sashe na 2 |
---|---|
Marar wayo |
Wanda ya manyanta |
Mai tawaye |
Mai bin doka |
Marar dabi’a |
Mai dabi’a |
Marar tunani |
Mai ilimi |
Mai gulma |
Mai hikima |
Mai yaudara |
Mai gaskiya |
Wadanne kalmomi ne kike ganin sun kwatanta ’yammata matasa da fina-finai ko talabijin ko kuma jaridu suke nuna su kamar shahararru?
Wadanne kalmomi ne suka kwatanta irin halayen da za ki so a san ki da su?
Mai yiwuwa kin samo amsoshin tambaya ta farko daga sashe na 1 kuma kin samo amsoshin tambaya ta biyu daga sashe na 2. Idan haka ne, to kina kokari ki zama mai mutunci fiye da “hadaddiyar” matashiya da ake nunawa a cikin fina-finai ko talabijin ko jaridu, kuma ba ke kadai ba ce. Ki yi la’akari da abin da ya sa muka ce haka.
Wata mai suna Erin ta ce: “Fina-finai suna yawan nuna ’yammata matasa kamar masu tawaye da ba su da hankali. Suna sa a ga kamar dukan ’yammata ba su da mutunci kuma damuwarsu kawai ita ce yadda mutane suke ganinsu da kuma yadda za su yi rikici a kan kowane karamin abu.
Wata mai suna Natalie ta ce: “’Yammata matasa da ake nunawa a talabijin masu neman jan hankalin mutane ne kuma iyakar abin da ke kansu shi ne siffarsu da suturarsu da suna da kuma ’yan maza.”
Maria kuma ta ce: “Da wuya ki ga wata ‘hadaddiyar’ yarinya da ba ta yin maye ko kwana da maza ko kuma yi wa iyayenta tawaye. Idan ba a nuna yarinya tana yin irin wadannan abubuwa ba, to za a nuna ta tana yi kamar ba ta waye ba.”
Ki tambayi kanki: ‘Shin, yadda nake yin abubuwa da ado da kuma magana suna bayyana ainihin irin mutuniyar da nake ne ko kuma ina kwaikwayon wadanda ake nunawa a kafofin sadarwa a matsayin shahararru?’
Abin da ya kamata ki sani
Matasa da yawa da suke ganin kamar suna nuna ainihin halayensu ba su san cewa suna bin halayen mutane da suke gani a kafofin sadarwa ba ne. Wata mai suna Karen ta ce “Haka kanwata take. Tana yi kamar abubuwa da ta damu da su kawai su ne sutura da kuma ’yan maza. Ita mai ilimi ce kuma tana son koyan abubuwa da yawa amma sai ta yi kamar ba ta san kome ba domin a ganinta, ta haka ne za ta zama kamar ‘sauran ’yammata.’ Abin haushi shi ne ita ’yar shekara 12 ce kawai!”
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku kamantu bisa ga kamar wannan zamani.”—Romawa 12:2.
Ba kowace yarinya ba ce take so ta zama kamar ’yammatan da ake nunawa a kafofin sadarwa a matsayin shahararru. Alexis, wata ’yar shekara 15 ta ce: “A kafofin sadarwa ana nuna ’yammata kamar marasa hankali da suka damu da jikunansu ne kawai kuma suna yawan yin abubuwa kamar yara, amma a ganina, wannan bai dace ba. Muna yin abubuwa masu muhimmanci a rayuwa ba sai tunanin ’yan maza kawai ba.”
Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Manya ne wadanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.’—Ibraniyawa 5:14, Littafi Mai Tsarki.
’Yan kasuwa ne suke so a bi salon ’yammata da ake nunawa a kafofin sadarwa. Manyan ’yan kasuwa suna amfani da jaridu da kayan yāyi da fasaha da kuma nishadi su yaudari yara tun kafin su kai shekara 13, domin sun san cewa hakan na kawo riba sosai. Wani littafi mai jigo 12 Going on 29, ya ce “Masu talla suna nuna kamar yara kasa da shekara 13 da ba su da sutura da kayan ado da kayan kwalliya da kuma na’ura na zamani ba su shahara ba. Tun kafin yara su manyanta, suna kallon tallan da ke ta da sha’awa a kowane lokaci.”
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan abin da ke cikin duniya, da kwadayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne.”—1 Yohanna 2:16.
Abin bimbini: Su wane ne suke amfana idan kika soma damuwa da sunan kamfanoni masu kera abubuwa masu tsada? Su wane ne ainihi suke cin riba idan kika sayi wayar yāyi domin kina so ki yi suna a gaban tsaranki? Mene ne ’yan kasuwa suke bida, riban kansu ko kuma naki?
Abin da za ki iya yi
Ki yi hattara da kwaikwayon ’yammata da ake nunawa a kafofin sadarwa. Yayin da kike girma, za ki koyi kasancewa da basira sosai. Ki yi tunani sosai a kan yadda ’yammata da ake nunawa a kafofin sadarwa za su iya yin tasiri a kan rayuwarki. Alana wata ’yar shekara 14 ta ce, “Kafofin sadarwa sukan girmama ’yammata da kwalliyarsu takan fi tufafi da suke sakawa, kuma matasa da yawa ba su san cewa hakan ba ya kara musu kyau ba, amma yana sa a gan su kamar wadanda suke mutuwar neman maza ne.”
Ki shirya makasudanki game da irin mutuniya da kike so ki zama. Alal misali, ki yi tunanin halayen da kika zaba a farkon wannan talifin, wato, halayen da za ki so a san ki da su. Me zai hana ki soma kokari tun yanzu don ki koyi wadannan halayen ko kuma ki inganta wadanda kike da su? Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ku yafa sabon mutum, wanda ake sabunta shi zuwa ilimi bisa ga surar mahaliccinsa,’ ba bisa ga surar masu talla ba.—Kolosiyawa 3:10.
Ki bi misalin mutane masu kirki. Kina iya samun mutane masu kirki a cikin iyalinku, alal misali, mahaifiyarki ko gwaggonki, ko kuma a tsakanin abokanki mata da suka manyanta. Shaidun Jehobah suna da mata da yawa da suka manyanta a cikin ikilisiyoyinsu.—Titus 2:3-5.
Shawara: Ki karanta littafin nan Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu don ki san game da mata masu kirki a cikin Littafi Mai Tsarki kamar su Ruth da Hannatu da Abigail da Esther da Maryamu da kuma Martha. Shaidun Jehobah ne suka wallafa littafin nan Ka yi koyi da bangaskiyarsu kuma za ki iya samunsa a dandalin www.isa4310.com/ha.